Connect with us

Wasanni

Kwallon Kwando: Los Angeles Lakers ta lashe gasar karo na 17

Published

on

Kungiyar kwallon Kwando ta Los Angeles Lakers ta kasar Amurka ta lashe gasar kwallon Kwando ta kasar bayan da ta doke Miami Heat da ci 106 da 93.

Nasarar da Lakers ta samu ya kawo karshen jira na tsawon shekaru da ta ke yi na lashe gasar NBA karo na 17.

LeBron James shi ne ya zama gwarzon dan wasa a gasar bayan da ya samu maki 28 da jefa kwallaye 14 da kuma bayar da kwallaye 10.

Nasarar da kungiyar ta samu ya zo a kan gaba bayan da ta yi rashin tsohon dan wasan ta Kobe Bryant wanda ya rasa ransa da shi da ‘yar sa Gianna mai shekaru 13 da kuma wasu mutane 17 a cikin wani jirgi mai saukar Ungulu da ya tarwatse a lokacin da ya tashi sama.

Los Angeles Lakers ta sadaukar da kofin ga tsohon marigayi dan wasan na ta Kobe Bryant, a yayin da magoya bayan kungiyar su ka gudanar da murnar lashe gasar a kan titi duk da Corona da a ke fama da shi a kasar Amurka tare da sanya rigar marigayi tsohon dan wasan su Kobe Bryant da kuma lambar sa a jikin rigar ta su da takunkumi mai dauke da hoton Kobe Bryant, inda su ke gursheken kuka.

Wasanni

Bayer Leverkusen ta zama zakarar gasar Bundesliga ta 2023/2024.

Published

on

Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Bayer Leverkusen ta zama zakarar gasar Bundesliga ta shekarar 2023/2024, bayan da suka samu nasara a kan Weder Bremen da ci 5-0.

Hakan ne kuma ya kawo ƙarshen shekaru 11 da Bayern Munich, da ta yi tana lashe gasar.

Wannan dai shi ne karo na farko da Bayer Leverkusen suka taɓa lashe gasar a tarihi, ida suka gaza ɗaukar kofin a shekarar 2002 a ranar ƙarshe ta gasar.

Har ila yau, a dai wannan shekarar ne su kayi rashin nasara hannun Shalke 04, a wasan ƙarshe na German Cup Da ci 4-2.

Haka kuma, Real Madrid suka doke su a wasan ƙarshe na zakarun nahiyar turai.

Rahotanni sun bayyana cewa ƙungiyar bata taɓa ɗaukar wata gasa ba a ƙarni na 21, sai bayan da Xavi Alonso ya karɓe su.

Continue Reading

Wasanni

Hukumar NPFL, ta amince da buƙatar Kano Pillars na ɗage wasan ta na mako na 28 da Enyimba

Published

on

Yanzu haka an samu dai-daito da hukumar NPFL, wanda ta amince da bukatar Kano Pillars na dage wasanta na mako na 28, da Enyimba zuwa ranar Alhamis, mai zuwa.

Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Kano Pillars, ce ta wallafa hakan a shafin ta na Facebook da yammacin Litinin ɗin nan, ta ce ƴan wasan ta za su tashi a gobe Talata, da safe zuwa Aba domin fafata wasannin su.

Idan dai ba’a manta ba ƙungiyar ta wallafa kaɗan daga irin ƙalubalen da take fuskanta a harkokin gudanarwar ta.

Pillars, ta wallafa ƙalubalen ne kamar haka, “A yanzu haka zancan da muke muku Kano Pillars ta rasa kudin da za taje garin Aba, domin buga wasan hamayya na Nigeria Premier league wato Zobia Classic”.

Wasan dai shine wasa mafi ɗaukar hankali a league din Nigeria baki ɗaya, ku taya mu yadawa dan Allah.

Continue Reading

Wasanni

Glesner ya zama sabon mai horas da Palace.

Published

on

Kungiyar kwallon kafa ta Crystal Palace ta sanar da nadin Oliver Glesner a matsayin sabon mai horaswar ta.

Glesner wanda tsohon mai horas da kungiyar kwallon kafa ta Eintracht Frankfurt ne mai shekaru 49 dan asalin kasar Austrian, ya maye gurbin tsohon mai horaswa Roy Hodson, wanda ake ganin ya gaza kai kungiyar ga tudun mun tsira.

A wasanni 16 da Crystal Palace ta buga a bayan nan ta yi rashin nasara a wasanni 10 duk karkashin jagorancin Roy Hodson wanda hakan yasa take mataki na 16 a teburin gasar firimiyar kasar Ingila.

Glesner dai ya rattaba kwantaragi da Palace har na tsawon shekaru biyu, zai kuma jagoranci kungiyar a wasan sa na farko da kungiyar kwallon kafa ta Burnley a ranar Asabar mai kamawa.

Continue Reading

Trending