Connect with us

Labarai

Takardun bogi: An kori malaman firamare sama da 100 a jihar Filato

Published

on

Hukumar Kula da Ilimin Firamare ta Jihar Filato (SUBEB) ta kori malaman firamare sama da 122 wadanda suka samu aiki da takardun bogi.

Shugaban hukumar, Farfesa Mathew Sule wanda ya bayyana hakan ga manema labarai a Jos babban birnin jihar, ya ce an gano malaman bogin ne sakamakon tantancewar da Hukumar ta yi.

Ya ce shawarar sallamar malaman ya yi dai-dai da dokokin aikin gwamnati da kuma ka’idojin Majalisar Rajistar Malamai ta Najeriya (TRCN).

Farfesa Mathew ya ce daga cikin sama da malamai dubu 15, 000 a makarantun firamaren gwamnati, an gano cewa 122 sun gabatar da takardun bogi, lamarin da ya sanya Hukumar bibiyar makarantun da suka ce sun kammala, inda aka gano cewa rufa-rufa suka yiwa gwamnati.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Labarai

Harin ‘yan bindiga ya yi sanadiyar mutuwar mutane 20 a Zamfara

Published

on

Yan bindiga sun hallaka mutane 20 a wani har da suka kai garin Tungar Kwana da ke karamar hukumar Mafara a jihar ta Zamfara, bayan sun saci wasu dabbobin da jami’an tsaro suka kwato.

Kakakin ‘yan sandan jihar SP Shehu Muhammad ya bayyana hakan a zantawar sa da  wakilin mu Yusuf Ibrahim Jargaba.

Ya ce, “Tuni suka baza jami’an tsaro domin gano wadanda su ka yi kisan su fuskanci hukunci”. A cewar SP Shehu Muhammad

 

Continue Reading

Labarai

Rahoto: Tarbiyya na taka muhimmiyar rawa wajen samun zaman lafiya – Liman

Published

on

Babban limamin masallacin juma’a na Umar Bin Khaddab da ke Dangi, Dr Yahaya Tanko ya ce, addinin musulunci addini ne na zaman lafiya, saboda haka al’umma su kiyayi tayar da husuma.

Dr Yahaya Tanko ya bayyana hakan ne a zantawar sa da wakilin mu Tijjani Adamu.

Domin jin cikakken rahoton saurari wannan.

Continue Reading

Labarai

Rahoto: Matashin da ake zargi da kashe matar sa ya sake gurfana a kotu

Published

on

Gwamnatin jihar Kano ta ci gurfanar da mutumin nan da ake zargin ya kashe matar sa, a gaban babbar kotun jihar Kano mai lamba 7, karkashin mai shari’a Usman Na Abba.

Tun a ranar 2 ga watan Afirilu na shekarar da ta gaba aka yi zargin Aminu Inuwa ya yi amfani da wuka ya kashe matar sa mai suna Safara’u Muhammadu, kuma binne ta a cikin gidan sa, a unguwar Gwazaye Dorayi Karama da ke karamar hukumar Gwale.

Domin jin cikakken rahoton saurari wannan.

Continue Reading

Trending

error: Content is protected !!