Connect with us

Labarai

Babu wani jami’in SARS da zai kasance cikin sabuwar rundunar SWAT – Muhammad Adamu

Published

on

Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta ce babu wani jami’in da ya taba kasancewa karkashin sashen yaki da fashi da makami na SARS da aka rushe da zai kasance cikin sabon sashen SWAT da aka kirkira.

Biyo bayan zanga-zanga da ta dauki kwanaki, Sufeto-Janar na ‘yan sanda, Mohammed Adamu, ya rusa sashen rundunar, na SARS, bayan da al’ummar Najeriya suka yi zargin cewa jami’an sashen na cin zarafin mutanen da basu ji basu gani ba.

Kwana biyu bayan rusa rundunar ta SARS, babban sufeton ‘yan sandan ya kafa wani sashen yaki da manyan laifuka wato SWAT, amma, wannan matakin bai yi wa wadanda suka yi zanga-zangar ta rusa rundunar yaki da fashi ba, dadi, lamarin da ya sa suka sauya salon zanga-zanga daga #EndSARS zuwa #EndSWAT.

To sai dai a kokarin yin karin haske kan sabon sashin da Muhammad Adamun ya kafa, rundunar ta fitar da sanarwa ta shafin Twitter, inda ta bayyana abin da aikinsu zai kasance.

Babu tabbas ko rundunar ‘yan sanda ta sauya sunan sabon sashen da aka kafa daga SWAT zuwa Tactical Team, amma kakakinta na kasa Frank Mbah ya ce babu wani jami’in SARS da zai shiga cikin sabuwar rundunar.

Labarai

Zaman lafiya: Majalisar dinkin duniya ta taka rawa – Farfesa Kamilu Fagge

Published

on

Masanin kimiyar siyasa a jami’ar Bayero da ke jihar Kano Farfesa Kamilu Sani Fagge, ya ce majalisar dinkin duniya, ta taka rawa wajen samar da zaman lafiya a duniya.

Farfesa Kamilu Sani Fagge ya bayyana hakan yayin zantawa da wakiliyar mu Aisha Aminu Kundila a wani bangare na bikin ranar tunawa da majalisar dinkin duniya a wannan shekarar.

Ya ce, “Nijeriya ta zama mamba ce a majalisar ta dinkin duniya a 1960 a matsayin mamba ta 99”. Inji Farfesa Kamilu Sani Fagge.

Continue Reading

Labarai

Polio: Za mu dakile bullar cutar shan inna a Kano – Gwamnatin Kano

Published

on

Gwamnatin jihar Kano ta ce za ta ci gaba da sanya idanu, domin ganin ba a sake samun bullar cutar shan inna ba ta Polio a fadin jihar Kano.

Kwamishinan lafiya na jihar, Dakta Aminu Ibrahim Tsanyawa ne ya bayyana hakan a yayin zantawar sa da manema labarai a wani bangaren na bikin ranar yaki da cutar shan inna ta duniya da ake gudanarwa a yau.

Ya ce, “Za mu ci gaba da gudanar da rigakafin cutar Polio a fadin jihar Kano, duk da cewa babu cutar a jihar wanda hakan zai bai wa yara kariya daga kamuwa da cutar a nan gaba”. A cewar Dakta Aminu Ibrahim Tsanyawa.

Sai dai ya bukaci iyaye da su ci gaba da kai yaran su, domin karbar rigakafin wanda hakan ne kadai zai taimaka wajen yaki da cutar ko da a nan gaba.

 

Continue Reading

Labarai

‘Yan sandan SARS 16 za su fuskanci hukunci sakamon zargin kisan kai

Published

on

Kwamitin shugaban kasa da ke bincike kan ayyukan ‘yan sanda ya ba da shawarar hukunta ‘yan sandan SARS 16 sakamakon zarginsu da kisan kai a jihohin kasar nan 12 har da birnin tarayya Abuja.

Rahotanni sun ce tun a watan Yunin shekarar da ta gabata ne kwamitin ya yi bincike kan mutanen, inda sai akwanan ne ya mikawa shugaban kasa rahoton.

Sauran wadanda aka mikawa rahoton sun hada da sufeto Janar na ‘yan sandan Muhammed Adamu da hukumar kula da ayyukan ‘yan sanda ta kasa da kuma attorney Janar na tarayya.

Jihohin da ‘yan sandan na SARS suka gudanar da ta’asar sun hada da: Akwa Ibom, Benue, Delta, Enugu, Lagos da Ogun, Rivers, Gombe, Kaduna da Kogi da kuma Kwara.

 

 

Continue Reading

Trending

error: Content is protected !!