Connect with us

Labarai

Bai kamata a rika cin zarafin masu zanga-zanga ba – Kungiyar lauyoyi

Published

on

Kungiyar Lauyoyi ta Najeriya (NBA) ta yi Allah wadai da yadda ake yiwa masu zanga-zanga barazana ta hanyar harba bindiga da jami’an ‘yan sanda ke yi domin tarwatsa su.

Shugaban kungiyar a wani taron manema labarai a Abuja, babban birnin kasar, Olumide Akpata, ya ce yin amfani da harsashi kai tsaye zai kara tabarbarewar yanayin da kasar ke ciki.

“Muna kira ga gwamnati da ta yi dukkan mai yuwwa wajen bawa kowanne dan kasa da ke bada gud8un mowa a zanga-zanga da ake yi a fadin kasar kariya, sannan ta umarci hukumomin tsaro da su dakatar da duk wani cin zarafi da ake yiwa wadanda ba shirin tashin hankali suka zo da shi ba.” In ji shi

Olumide ya ce babu al’amari da zai sanya aci zarafin masu zanga-zanga lumana, tunda ba rikici suka tayar ba, kuma kokarin tarwatsa ba komai zai haifar face da na sani.

Labarai

Harin ‘yan bindiga ya yi sanadiyar mutuwar mutane 20 a Zamfara

Published

on

Yan bindiga sun hallaka mutane 20 a wani har da suka kai garin Tungar Kwana da ke karamar hukumar Mafara a jihar ta Zamfara, bayan sun saci wasu dabbobin da jami’an tsaro suka kwato.

Kakakin ‘yan sandan jihar SP Shehu Muhammad ya bayyana hakan a zantawar sa da  wakilin mu Yusuf Ibrahim Jargaba.

Ya ce, “Tuni suka baza jami’an tsaro domin gano wadanda su ka yi kisan su fuskanci hukunci”. A cewar SP Shehu Muhammad

 

Continue Reading

Labarai

Rahoto: Tarbiyya na taka muhimmiyar rawa wajen samun zaman lafiya – Liman

Published

on

Babban limamin masallacin juma’a na Umar Bin Khaddab da ke Dangi, Dr Yahaya Tanko ya ce, addinin musulunci addini ne na zaman lafiya, saboda haka al’umma su kiyayi tayar da husuma.

Dr Yahaya Tanko ya bayyana hakan ne a zantawar sa da wakilin mu Tijjani Adamu.

Domin jin cikakken rahoton saurari wannan.

Continue Reading

Labarai

Rahoto: Matashin da ake zargi da kashe matar sa ya sake gurfana a kotu

Published

on

Gwamnatin jihar Kano ta ci gurfanar da mutumin nan da ake zargin ya kashe matar sa, a gaban babbar kotun jihar Kano mai lamba 7, karkashin mai shari’a Usman Na Abba.

Tun a ranar 2 ga watan Afirilu na shekarar da ta gaba aka yi zargin Aminu Inuwa ya yi amfani da wuka ya kashe matar sa mai suna Safara’u Muhammadu, kuma binne ta a cikin gidan sa, a unguwar Gwazaye Dorayi Karama da ke karamar hukumar Gwale.

Domin jin cikakken rahoton saurari wannan.

Continue Reading

Trending

error: Content is protected !!