Connect with us

Labarai

Buhari ya sake nada Farfesa Yakubu a matsayin shugaban INEC

Published

on

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya sake gabatar da sunan Farfesa Mahmood Yakubu, a majalisar dokokin kasar, domin sake ci gaba da jagorantar hukumar zabe mai zaman kanta wato INEC a wa’adi na biyu.

Shugaba Buhari ya tabbatar da sake naɗa Farfesa Yakubu ne a cikin wata wasika da ya aika wa shugaban majalisar dattiajai Sanata Ahmed Lawan.

Wata sanarwa mai dauke da sa hannun mai magana da yawun shugaban, Femi Adesina, ta ce bisa tanadin sashi na 154 (1) na kundin tsarin mulkin Najeriya na 1999 da aka yiwa gyaran fuska, “Ina farin cikin gabatar da Farfesa Mahmood Yakubu ga majalisa domin tabbatar da shi a matsayin Shugaban, Hukumar zabe mai zaman kanta ta Kasa (INEC) a karo na biyu kuma wa’adi na karshe.

Farfesa Yakubu shi ya jagoranci babban zaben shekarar 2019, da kuma na gwamnoni da ake gudanarwa lokaci daban da babban zaɓe.

Duk da cewa yawancin zabukan da ya jagoranta sun sha suka daga masu sanya ido daga cikin gida da kuma wajen kasar, kan matsaloli da zargin magudi, amma kuma an yaba masa a zaben gwamnoni da ya jagoranta a baya-baya nan a jihohin Edo inda dan takarar jam’iyyar PDP mai hamayya ya lashe da kuma Ondo da dan takarar jam’iyyar APC ya yi nasara.

A watan Oktoba 2015 ne Shugaba Buhari ya naɗa Farfesa Yakubu a matsayin shugaban hukumar INEC, wanda ya maye gurbin Farfesa Attahiru Jega.

Labarai

Rahoto: Mu na bukatar gyaran titi a yankin mu – Unguwar Jakada

Published

on

Al’ummar Dorayi Babba unguwar Jakada sun yi kira ga gwamnatin jihar Kano da ta gyara musu Titin da ya tashi daga unguwar ta Jakada zuwa Rijiyar Zaki Tasha, domin ci gaba da jin dadin zirga-zirgar ababen hawa.

Al’ummar yankin sun yi kiran ne a yayin zantawar su da wakilin mu Tijjani Adamu a ranar Laraba.

Domin jin cikakken rahoton saurari wannan.

Continue Reading

Labarai

Rundunar ƴan sandan Kano ta cafke matashi da sinƙi-sinƙin tabar wiwi

Published

on

Rundunar ƴan sandan jihar Kano ta cafke wani matashi a unguwar Ɗanbare ɗauke da sinƙi-sinƙin tabar wiwi, da aka sarrafa tamkar sinƙin Biredi.

Matashin ya ce, wiwin ta mahaifinsa ce, kuma yanzu an kama shi, hakan ya sa mahaifiyarsa ta umarce shi da ya sauya wa tabar wuri.

A cewar sa, mahaifin na sa ya shafe sama da shekara ashirin yana sana’ar safarar tabar wiwin.

Jami’in hulɗa da jama’a na ƴan sandan Kano DSP. Abdullahi Haruna Kiyawa ya ce, sun cafke matashin ne ta hanyar bayanan sirri da suka samu.

Kiyawa ya ce, tuni aka mayar da lamarin zuwa sashen binciken manyan laifuka na rundunar ƴan sandan Kano.

Continue Reading

Labarai

Gwamnatin Kano za ta sauyawa gidan Zoo matsuguni

Published

on

Gwamnatin jihar Kano ta ce, za ta sauya wa gidan adana namun daji na jihar matsuguni.

Kwamishinan raya al’adu da kayan tarihi na jihar Kano Ibrahim Ahmad ne ya shaida wa Freedom Radio hakan.

Kwamishinan ya ce, dalilin wannan sauyi shi ne, gidan adana namun dajin ya yi kusa da jama’a, kuma dabbobin ba sa son hayaniya.

A cewar sa, za a mayar da gidan adana namun dajin zuwa garin Tiga da ke ƙaramar hukumar Bebeji.

Continue Reading

Trending

error: Content is protected !!