Connect with us

Labarai

Mu na neman ƙarin tallafin kayan aiki domin daƙile laifuka a Najeriya – Bijilante

Published

on

Shugaban Ƙungiyar Bijilante na ƙasa Dakta Usman Muhammad Jahun, ya buƙaci gwamnatin Najeriya da ta ƙara tallafawa jami’ansu da kayayyakin aiki, domin samun damar daƙile muggan laifuka da ke cigaba da ta’azzara a ƙasar nan.

Dakta Muhammad Jahun ya bayyana hakan ne a yayin ganawarsa da gidan Rediyon Dala FM Kano.

Yana mai cewar, “Matuƙar gwamnatin ƙasar nan za ta ƙara tallafawa ƴan ƙungiyar mu, za mu samu damar agazawa jami’an tsaron ƙasar nan, domin samun damar daƙile matsalar tsaro da yake ci gaba da wakana a faɗin Najeriya”.

“Zargin da ake yiwa jami’an mu da wuce gona da iri ba gaskiya ba ne, hasalima ƴan kwamiti ne suke fakewa damu suke aikta ba dai dain ba, kuma idan muka kama irin waɗannan mutane zamu ɗauki mataki ankansu”. Inji Muhammad Jahun.

Da yake nasa jawabin shugaban Ƙungiyar Bijilante na jihar Kano Alhaji Muhammad Kabir Alhaji, cewa ya yi, babban ƙalubalen da suka fi fuskanta da shi a   shekarar da mu ke shirin bankwana da ita, shi ne matsalar shaye shaye, faɗan daba da kuma garkuwa da mutane, amma a shirye suke wajen ganin sun bada gudunmawarsu dan kawar da wannan al’amari.

Wakilin mu Hassan Mamuda Ya’unya rawaito cewa, Muhammad Kabir Alhaji, ya kuma buƙaci gwamnatin jihar Kano, da ta ƙara tallafawa jami’ansu da kayayyakin aiki, tare kuma da rinƙa bawa ƴan sintirin ɗan ƙudin shiga domin ƙara musu ƙwarin gwiywa a kan aikin da sukeyi na yau da gobe.

Labarai

NAHCON ta sanya ranar fara jigilar maniyyata aikin hajjin bana zuwa Saudiyya

Published

on

Yanzu haka hukumar Aikin Hajji ta ƙasa NAHCON, ta 15 ga watan nan na Mayun 2024, a matsayin ranar da za’a fara jigilar maniyyata aikin hajjin bana, zuwa ƙasa mai tsarki.

Bayanin hakan ya fito ne ta bakin shugaban hukumar ta NAHCON, Jalal Ahmad Arabi, a wajen taron masu ruwa da tsaki kan aikin Hajji da Umrah, da ya gudana yau Alhamis birnin tarayya Abuja.

“Maniyyata kimanin 65,500 ne za su sauke Farali daga ƙasar nan a ƙasa mai tsarki; za su shafe aƙalla kwanaki huɗu domin yin ziyara a Madina kafin fara aikin Hajji, “in ji Arabi”.

Daga bisani shugaban hukumar aikin hajjin Jalal Ahmad Arabi, ya kuma bayyana cewa za ayi jigilar maniyyata aikin hajjin ne daga cibiyoyi 10 a faɗi ƙasar nan.

Continue Reading

Labarai

Gwamnatin tarayya ta ayyana gobe Laraba a matsayin ranar hutu

Published

on

Gwamnatin tarayya ta ayyana gobe Laraba, 1 ga watan Mayun 2024, a matsayin ranar hutu, domin bikin ranar ma’aikata na wannan shekara.

Ministan harkokin cikin gida, Olubunmi Tunji-Ojo, ne ya bayyana hakan, a cikin wata sanarwa da ya fitar a yau Talata.

Olubunmi, ya kuma sake nanata buƙatar ganin ma’aikata sun jajirce da yin aiki yadda ya kamata a dukkanib matakai daban-daban.

Continue Reading

Labarai

Wahalar Fetur ta haifar mana da koma baya a sana’ar mu – Mai Motar Haya

Published

on

Wani mai sana’ar tuƙin motar Haya, da kuma lodin fasinjoji mai suna Kabiru Muhammad, mazaunin ƙaramar hukumar Munjibir, ya ce ƙarancin motocin Haya da ake samu a yanzu, yana da alaƙa da wahalar man Fetur da ake fuskanta a sassan Najeriya.

A zantawar mutumin da wakilinmu Yusuf Nadabo Isma’il, ta cikin shirin rahotanni daga ƴan Zazu na yau Talata, ya ce a baya har motoci hamsin suke yiwa lodin fasinjoji su tashi, amma a yanzu Mota ɗaya suke iya cikawa sakamakon ƙarancin Fetur da ake fama da shi.

Ya kuma ce ƙaranci tare da tsadar man fetur ɗin da ake fama da shi, sun haddasa musu koma baya a sana’ar su, baya ga batun kuma matsalar da suke fuskanta da fasinjoji wajen biyan kuɗin Mota.

Wakiliyarmu da ta bibiyi shirin na ƴan Zazu Ummi Bala Ahmad ta rawaito cewa, matuƙin motar Kabiru Muhammad, ya kuma yi kira ga gwamnatin tarayya da ta jahohi, da su yi abinda ya kamata dan ganin farashin man Fetur ɗin ya sauka, domin al’umma su samun sauƙi.

Continue Reading

Trending