Connect with us

Wasanni

Wasan Golf: Na lashe kofi da dama a wasan – Sule Imam Daura

Published

on

Wani dan wasan kwallon Golf, a jihar Kano, Sule Imam Daura, ya ce ya lashe kofi da dama a wasan a iya tsawon lokacin da ya fafata a wasan.

Ya ce wasan na motsa jiki ne ba wai iya lashe kofin ba kadai, domin kuwa har ta kai sai da gabobin jikin shi su ka koma daidai sabanin a baya.

Daga filin wasan kwallon Golf na Kano Club, wakilin mu Musa Abdu Tudun Wada ya turo mana da rahoto.

Wasanni

NPFL: Kano Pillars ta koma mataki na daya bayan da ta doke Sunshine Stars

Published

on

Kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars ta koma mataki na daya a jerin jaddawalin gasar cin kofin kwararru ta kasa (NPFL) da maki 23, bayan da ta sami nasara da ci 1 da nema a hannun Sunshine Stars, bayan da dan wasan Pillars Nwagua Nyima ya jefa kwallo tilo a raga.

Yanzu haka Kwara United it ace a matsayi na biyu da maki 22 yayin da Enyimba take a matsayi na 3 da maki 22 a wasanni 10 da ta fafata.

Ga jerin wasannin da aka fafata mako na 12 a gasar cin kofin kwararru ta kasa (NPFL).

Enyimba 1-1 Akwa Utd

Plateau Utd 3-0 Jigawa Golden Stars

Nasarawa Utd 3-0 FC Ifeanyiubah

Kano Pillars 1-0 Sunshine Stars

Warri Wolves 1-0 Rivers Utd

Wikki 1-1Rangers

Kwara Utd 1-1 Abia Warriors

Continue Reading

Wasanni

Gasar Ahlan aji na 2:  Jalayi za ta barje gumi da Junior Morocco

Published

on

Kungiyar kwallon kafa ta Jalayi Fc za ta fafata da Junior Morocco a yammacin ranar Alhamis 25-02-2021 da karfe 4 na yamma.

Sauran wasan mako na 3 za a fafata tsakanin:

Kura Better Warriors Vs Dorayi Babba warriors

Fc Kofar Ruwa Vs Royal Star R/zaki

A gasar cin kofin Tofa Premier League FC Kofar Ruwa za ta kece raini da Wonder Boys a filin wasa na Mahaha.

Continue Reading

Wasanni

Waye Gwani Cup: Junior Star Light ta doke Ganjar United  

Published

on

A cigaba da wasan sada zumunta na Waye Gwani Cup ƙarƙashi jagorancin Abba Siniya Ja’en layin shago tara, wasan da aka buga a jiya Talata.

Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Junior Star Light dake Ja’en Arewaci, ta yi nasara a kan kungiyar Ganjar United dake unguwar Ja’en gidan Kwari da ci 3 da 1.

Wasan dai  an fafata shi ne a filin wasa na Fandanka dake Ja’en Ring Road.

Continue Reading

Trending

error: Content is protected !!