Wasanni
Dambe: Hannun Na Dada ya karye yayin da hannun Shagon Reza ya makale

Daga gidan wasan Damben gargajiya dake Ado Bayero Square a unguwar Sabon Gari a jihar Kano, a wasan da aka fafata a yammacin jiya Lahadi wasan ya Samu halartar ‘yan wasan Damben sama da dari. Hakan ya biyo bayan Ajo da aka yiwa Ebola Inda aka fara fafatawa tsakanin, Aljanin Sanin kurna ya kashe Aljanin Shaddadu a turmi na biyu.
Shagon Shattima da Shagon Bahagon Sarka ba kisa.
Na Dada da Abban Lungu ba kisa sakamakon ana dambe hannun Na Dada da yake damben d ashi ya karye.
Dogon Zee Y ya kashe Bahagon Ebola da dakika 16 da hura wasan.
Ali Kanin Bello ya kashe Shagon Aleka a turmi na biyu.
Shagon Reza Bunza da Bahagon Dage Ana dambatawa hannun Shagon Reza Bunza ya Makale hakan tasa aka kashe Damben.
Dan Alin bata isarka ya buge Mola-Mola a turmin farko.
Boka da Shagon-Shagon Buhari turmi uku ba kisa.
Wasanni
Unity Cup: M.Y Jamil za ta barje gumi da Zoo United

A ci gaba da gasar Unity Cup ajin matasa da ake fafatawa a jihar Kano, a yammacin ranar Juma’a ne kungiyar kwallon kafa ta M.Y Jamil za ta kara da Zoo United a filin wasa na Mahaha Sport Complex dake Kofar Na’isa a cikin filin Kano United.
Soccer Strikes za ta kece raini da Clever Warriors a filin wasa na Sky Limit dake Mahaha.
Kano Rovers za ta fafata da Gama Emirates a filin wasa na Gwagwarwa Mini Stadium.
Dabo Babies za ta buga da Dabo Babies a filin wasa na Diso United dake Mahaha.
Wasannin duka za a fafata su ne da karfe hudu na yammacin ranar Juma’a.
Wasanni
Kano: Sakamakon gasar Unity Cup

Sakamakon wasannin kwallon kafar da aka fafata a yammacin ranar Alhamis a jihar Kano.
Admiral United 0-2 Ramcy FC
Leeders FC 2-0 Royal Form
Kano United 5-2 Zango Academy
Wasanni
Kwallon Golf: Na fara zuwa filin wasan Golf tun 1977 – Malam Isah Lafiya

Wani dan wasan kwallon Golf, Malam Isah Lafiya, ya ce ya fara wasan kwallon Golf sakamakon ya kasance mai matsayin daukar jakar ‘yan wasa.
Malam Isa Lafiya ya kuma ce tun ya na daukar jakar ‘yan wasan kwallon Golf ta na rinjayar shi, har ta kai gay a kai matsayin fara buga wasan.
Wakilin mu Musa Abdu daga filin wasan kwallon Golf na jihar Kaduna ya turo mana da rahoto.
-
Manyan Labarai1 year ago
KAROTA: An baiwa Baffa Babba wa’adin kwanaki bakwai
-
Nishadi1 year ago
Ina neman mijin aure – Rayya
-
Labarai12 months ago
Auren dan Panshekara da ba Amurkiya ya samu cikas
-
Nishadi1 year ago
Mansura Isah ta yi kaca-kaca da Sadiya Haruna
-
Labarai5 months ago
Hamisu Breaker ya kai kan sa wajen ‘yan sanda
-
Nishadi1 year ago
An gano daliban da Adam Zango ya dauki nauyin karatun su
-
Manyan Labarai1 year ago
Ba’amurkiya da masoyin ta sun hada cinkoso a kasuwar Sabon Gari
-
Manyan Labarai1 year ago
Sabuwar damfarar da ta fito a Kano
You must be logged in to post a comment Login
You must log in to post a comment.