Connect with us

Siyasa

Suturar da dan Kwankwasiyya ya ke sawa dan Gandujiyya ba ya sawa – Muttaka Dan Gambo

Published

on

Guda daga cikin sojan baka na jam’iyar APC a jihar Kano, Muttaka Dan Muhammad Gambo, ya ce suturar da dan tsagin Kwankwasiyya ya ke sawa ya fi na tsagin Gandujiyya.

Muttaka Dan Muhammad Gambo, ya furta hakan ne a cikin shirin siyasa na Hangen Dala da ya ke zuwa da karfe 10 na dare.

Cikin zantawar sa da wakilin mu Abdulkadir Yusuf Gwarzo da yi da shi, Muttaka Dan Muhammad ya ce mudin jam’iyar APC ba ta taimaki dan jam’iyar ta ba, akwai gagarumar matsala a zaben shekarar 2023.

Labarai

Idan Kwankwaso na son dawowa APC sai ya yiwa Ganduje biyayya – Aminu Black

Published

on

Dan Jam’iyyar APC a jihar Kano, Aminu Black Gwale, kuma guda daga cikin magoya bayan tsagin Gandujiyya  ya ce, tsarin da ‘yan Jamiyyar PDP kwankwasiyya su ke kai a yanzu ya nuna cewa, ba su shirya karbar mulki ba a hannun APC  a zaben 2023.

Aminu Black ya bayyana hakan ne ta cikin Shirin siyasa Hangen Dala, na gidan rediyon Dala a ranar  Alhamis.

Ya ce, “Mu na sane da yadda Madugun PDP ya ke zuwa wurare daban-daban domin sahale masa ya dawo Jam’iyyar APC, wanda kuma su ke watsa masa kasa a ido”

Ya kuma ce “Matukar kwankwaso na son dawowa cikin APC to babu makawa sai ya risunawa gwamna Ganduje domin shi ne jagoran APC a jihar Kano”. A cewar Aminu Black Gwale.

Kazalika, Aminu Black Gwale ya kuma nuna takaicin sa, kan yadda wasu ke fara hasashen gadon kujerar gwamnan Kano tun yanzu, lamarin da ya ce, babu wani raba gardama a Jam’iyyar APC, kuma a jira zuwa lokacin ya zo tukunna.

Continue Reading

Labarai

Matasa kar ku kara zabar duk wanda bai yi mu ku aikin da ya kamata ba – Farfesa Hafsat Ganduje

Published

on

Matar gwamnan jihar Kano, Farfesa Hafsat Ganduje ta bukaci al’ummar jihar Kano da su rinka sanya idanu a kan yadda shugabannin kananan hukumomi su ke gudanar da ayyukan su.

Wannan na zuwa ne yayin kaddamar da rabon tallafin Naira dubu goma-goma ga mutum 701 a karamar hukumar Birni a jihar Kano.

Ta ce”Duk wanda al’umma su ka zaba bai yi mu su aikin da ya kamata ba kar ku kara zabar sa, domin ba shi da wani amfani. Mutune su rinka zabar jagorori matasa wanda hakan zai taimaka wajen yi mu ku abun da ya kamata, wanda kuma ya ke tafiya da zamani”. A cewar Farfesa Hafsat Ganduje.

Wakiliyar mu Aisha Shehu Kabara ta rawaito mana cewa, Farfesa Hafsat Ganduje ta ja hankalin wadanda a ka baiwa jarin da su yi amfani da shi ta hanyar da ta dace, domin hakan zai taimaka wajen rage rashin sana’a a tsakanin al’umma.

Continue Reading

Labarai

Sayar da filin gidan rediyo: Mu na kalubalantar gwamnatin Kano – PDP     

Published

on

Jamiyyar PDP a Kano ta kalubalanci gwamnatin jihar Kano, kan batun zargin sayar da gidan rediyon manoma na unguwar Tukuntawa dake karamar hukumar birni.

Sakataren yada labaran jam’iyyar na Kano, Bashir Sanata ne ya bayyana hakan, ta cikin Shirin Hangen Dala.

Ya ce”Abun kunya ne a ce gwamnatin ta fito ta bayyana cewa rashin tsaro ne ya sanya ta za ta sayar da gidan rediyon manoma na Tukuntawa. Kamata ya yi gwamnatin APC ta yi koyi da abin da gwamnatin Rabiu Kwankwaso ta yi, na mayar da wasu wuraren da al’umma za su amfana”.

 

Continue Reading

Trending

error: Content is protected !!