Labarai
Yan Bijilante ku rinƙa bin doka a ayyukan ku – Usman Abdullahi

Hukumar karɓar ƙorafe-ƙorafe da yaƙi da cin hanci da rashawa ta jihar Kano ta ce, ya zama dole ƙungiyoyin bijilante, su ƙara dagewa wajen bin doka sau da ƙafa, a yayin gudanar da ayyukansu na yau da kullum.
Shugaban kai sumame na hukumar CSP Usman Abdullahi Gambo ne bayyana hakan, a yayin buɗe Ofishin Bijilante na unguwar Jakara dake yankin ƙaramar hukumar HukumarDala, a ranar Lahadi.
Ya ce, “Kamata ya yi Jami’an Bijilante su ƙara himma wajen aiki tare da kaucewa karya doka”. A cewar CSP Usman Abdullahi Gambo.
A nasa jawabin Kwamandan Bijilante na ofishin da aka buɗe Alhaji Haruna Ahmad Maja, cewa ya yi, za su yi iya bakin ƙoƙarin suna kakkaɓe ɓata gari a yankin da kewaye.
Wakilinmu Hassan MamudaYa’u ta ruwaito cewa shugaban ƙaramar hukumar Dala Alhaji Ibrahim Sulaiman Ɗan Isle, wanda yasa mu wakilcin Kakakin majalisar ƙaramar hukumar Dalan Alhaji Idris Tijjani Idris ya ce, za su yi bakin ƙoƙarin su wajen ganin sun bayar da ta su gudunmawar ga ƴanƙungiyar.

Hangen Dala
Rashin wuta: Muna cikin mawuyacin hali – al’ummar Kano, Katsina da Jigawa

Al’ummar jihohin Kano, katsina da Jigawa na fuskantar yanayi mara dadi, Sakamakon karancin samun wutar lantarki daga hukumar KEDCO.
Al’ummar jihohin sun ce iya sa’o’i uku kacal suke samun wutar, wanda hakan ke haifar musu da nakasu a harkokin kasuwancin su.
Wani bincike da jaridar Daily Trust tayi ta ambato yadda masu kananan masana’antu irin su Walda, Cajin Waya, Kankara da masu sana’ar dinki da dai sauran kananan sana’o’i dake amfani da wutar lantarki sun shiga mawuyacin hali.
Kazalika rashin wutar ya shafi hatta bangaren ruwan sha, dama masu sana’ar sayar da Ruwa a irin yankunan Hotoro da sauran irin wuraren dake sayen ruwa, Inda yanzu haka ruwan yayi tashin gwauron zabi a kowace jarka.
Koda dai ana ta bangaren hukumar rarraba hasken wutar lantarkin me kula da shiyyar Kano, Katsina da Jigawa KEDCO sun nemi afuwar al’umma.
Idan za’a tuna dai a makon jiya ne Ministan Wutar lantarki yace ‘yan Nigeria Miliyan 150 na samun wadatacciyar wutar lantarki.
Sai dai kuma a jihohi irin su Kano, Katsina da Jigawa na bayyana damuwa kan karancin Wutar, Inda suka ce bata wuce ta sa’o’i uku suke samu a kowa ce rana.

Hangen Dala
Rashin wuta:- Muna cikin mawuyacin hali – al’ummar Kano, Katsina da Jigawa

Ci gaba ba ya zuwa sai an samu haɗin kan al’umma – Dagacin Ja’en

Dagacin garin Ja’en da ke ƙaramar hukumar Gwale a jihar Kano, Alhaji Isma’il Sa’ad Usman, ya ce hadin kai ne kaɗai zai kawo ci gaba ga kowa ce irin al’umma.
Dagacin ya bayyana hakan ne Jim kaɗan bayan wani taron masu Ruwa da tsaki na Garin Ja’en, wanda Hakimin Gundumar Ɗorayi Barde Kerarriya Alhaji Shehu Kabir Bayero ya shirya, aka gudanar a yankin Ja’en a ƙarshen makon da ya gabata.
“Dukkanin wani ci gaba ba ya zuwa har sai an samu haɗin kan kowa ne bangare na al’umma, “in ji Dagacin”.
Wakilin Dala FM Kano, Ahmad Rabi’u Ja’en ya ruwaito cewa, taron ya samu halartar dukkanin bangarori, na unguwannin Ja’en, da suka haɗar da kungiyar mafarauta da maharba dabma kungiyar malaman makaranta.

-
Nishadi5 years ago
Ina neman mijin aure – Rayya
-
Labarai5 years ago
Hamisu Breaker ya kai kan sa wajen ‘yan sanda
-
Nishadi6 years ago
Mansura Isah ta yi kaca-kaca da Sadiya Haruna
-
Manyan Labarai5 years ago
KAROTA: An baiwa Baffa Babba wa’adin kwanaki bakwai
-
Labarai5 years ago
Auren dan Panshekara da ba Amurkiya ya samu cikas
-
Lafiya3 years ago
Rahoto: An gano wani gida da ake gini da takardun Kur’ani da Alluna
-
Manyan Labarai5 years ago
Sabuwar damfarar da ta fito a Kano
-
Nishadi6 years ago
An gano daliban da Adam Zango ya dauki nauyin karatun su