Manyan Labarai
Majalisa: A gyara gadar Dakatsalle zuwa Tiga – Abubakar Uba Galadima

Majalisar dokokin jihar Kano ta bukaci gwamnatin jihar, karkashin jagorancin gwamna Dr Abdullahi Umar Ganduje da ta kai dauki gadar da ta hade Dakatsalle zuwa Tiga dake garin Bagauda.
Kiran ya biyo bayan kudurin gaggawa da wakilin karamar hukumar Bebeji, Abubakar Uba Galadima ya gabatar yayin zaman majalisar na ranar Laraba.
Ya ce, “Yin hanyar zai taimakawa al’ummar yankin tare da tabbatar mu su da cewa, su ma su na amfana da mulkin Demokradiyya”. A cewar Abubakar Uba Galadima.
A yayin zaman majalisar na ranar bisa jagorancin kakakin majalisar, Hamisu Ibrahim Chidari, zauren ya gabatar da karatu na biyu kan dokar samar da ofishin kula da basussuka na jihar Kano.
Mataimakin shugaban masu rinjaye, Abdullahi Iliyasu Yaryasa shi ne ya jagoranci gabatar da na biyu.
Wakiliyar mu Khadija Ishaq Muhammad ta rawaito cewar, bayan kammala zaman na ranar Larabar ne kuma majalisar ta amince da dage zaman ta zuwa ranar Litinin mai zuwa.

Hangen Dala
Gwamnoni sun bukaci a kawo karshen matasalar Filato

Ƙungiyar Gwamnonin kasar nan (NGF) ta buƙaci jagororin jihar Plateau su haɗa kan al’ummar jihar mai yawan al’adu da ƙabilu domin dakatar da kashe-kashen mutane da ake yawan samu a jihar.
Shugaban ƙungiyar, wanda kuma shi ne gwamnan jihar Kwara – Abdulrahman Abdulrazaq, ne ya bayyana haka ranar Alhamis lokacin da ya kai ziyarar jaje.
“Muna kira da jagorori da masu faɗa a ji a duka garuruwan jihar da sauran fannoni da su haɗa hannu da gwamnan jihar wajen haɗa kan al’ummar jihar tare da dawo da zaman lafiya mai ɗorewa”, in ji shugaban ƙungiyar ta NGF.
“Ya kamata shugabannin matasan al’umomin jihar su fito su haɗa kai wajen yin Allah wadai da tashin hankalin da ake samu a jihar, muna kira da a riƙa sasanta duka matsalolin da suka taso ta hanyar tattaunawa da lalama tare da girmama juna,” a cewar Abdulrahman Abdulrazaq.
Fiye da mutum 100 ne aka kashe cikin mako biyu da suka gabata, lokacin da wasu mahara suka kai hari a wasu garuruwan ƙananan hukumomin Bokkos da Bassa a jihar.
A ranar Talata ne babban sifeton ƴansandan ƙasar, Kayode Egbetokun ya ziyarci jihar inda ya sha alwashin kamo waɗanda suka ƙaddamar da kashe-kashen, da ya bayyana da na rashin imani, domin hukunta su.

Baba Suda
‘Yan Nigeria Miliyan 150 na samun wadatacciyar wutar lantarki – Minista

Ministan Wutar Lantarki, Adedayo Adelabu ya bayyana cewa kimanin ’yan Najeriya miliyan 150 ne yanzu ke samun isasshiyar wutar lantarki, yayin da miliyan 80 ke da ƙarancin wutar lantarki.
Ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis a yayin taron sabunta sassan ministoci na 2025 da aka gudanar a Abuja, inda ya yi magana tare da ministan yaɗa labarai da wayar da kan jama’a, Mohammed Idris Malagi, da sauran masu ruwa da tsaki.
Adelabu ya bayyana cewa ci gaban ya samo asali ne daga shigar Najeriya cikin shirin “Mission 300” – wani gagarumin ƙoƙarin haɗin gwiwa na Bankin Duniya da Bankin Raya Afirka (AfDB) da nufin samar da wutar lantarki ga ‘yan Afirka miliyan 300 nan da shekarar 2030.
Ƙa’idar ta tsara kyawawan manufofi don haɓaka hanyoyin samar da wutar lantarki, ƙara haɓaka makamashi da inganta hanyoyin magance matsalolin dafa abinci mai tsafta ga miliyoyin ‘yan Najeriya – wato Mission 300, kuma muna samun ci gaba mai kyau a kan wannan,” in ji shi.
Ya ci gaba da cewa, “Ina mai farin cikin gaya muku cewa cikin ‘yan Afirka miliyan 300 da Bankin Duniya da AfDB ke son cimmawa, Najeriya na kan hanyar da za ta biya ƙasa da kashi 25 cikin 100, wanda ke nufin kusan ‘yan Najeriya miliyan 75. Da muka gabatar da yarjejeniyarmu, sun amince da mu.”

Manyan Labarai
Muna Allah wa-dai da hukuncin ECOWAS, kan yunƙurin soke dokar hukunta masu ɓatanci ga Ma’aiki – Zauren haɗin kan Malamai

Zauren haɗin kan Malamai da ƙungiyoyin Musulunci na jihar Kano, ya yi Allah wa-dai da yunƙurin da ƙungiyar haɓaka tattalin arziƙin ƙasashen yammacin Afrika (ECOWAS) ke yi.
ECOWAS, dai na buƙatar gwamnatin tarayya ta soke dokar da ta yi tanadin hukunta waɗanda suka yi ɓatanci ga Ma’aiki S.A.W, wai saboda dokar ta ci karo ɗaɓɓaƙa haƙƙin ɗan adam na faɗin albarkacin Baki.
Sakataren haɗakar ƙungiyoyin Dakta Sa’edu Ahmad Dukawa ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwar da ya aikowa Dala FM Kano, a ranar Alhamis.
Ya ce wajen yanke hukuncin ya nuna kotun ECOWAS, ba ta yi la’akari da cewar kowacce doka tana da iya da kuma neman zaman lafiya don gujewa ramuwar gayya ba.
Ya ci gaba da cewa, “Kotun wajen yanke hukuncin ba ta yi la’akari da tsarin mulkin ƙasashen da suke cikin haɗakar ƙungiyar ba, wanda ya bai wa kowacce ƙasa hurumin yin dokokin da suka dace da ita, sannan ya fifita tsarin mulkin ta na ciki da wajen ƙasar, “in ki Dukawa”.
A cewar sa, a dalilin hakan zauren ke tur da Allah wa-dai da wannan makahon hukuncin, inda zauren ya kuma yabawa gwmanan jihar Kano Abba Kabir Yusuf, wajen azama da ya yi wajen fitar da matsayar gwamnatinsa game da hukuncin, da ya ce ba za su soke dokar da ta bada damar hukunta wanda ya yi ɓatanci ga Ma’aiki S.A.W.

-
Nishadi5 years ago
Ina neman mijin aure – Rayya
-
Labarai5 years ago
Hamisu Breaker ya kai kan sa wajen ‘yan sanda
-
Nishadi6 years ago
Mansura Isah ta yi kaca-kaca da Sadiya Haruna
-
Manyan Labarai5 years ago
KAROTA: An baiwa Baffa Babba wa’adin kwanaki bakwai
-
Labarai5 years ago
Auren dan Panshekara da ba Amurkiya ya samu cikas
-
Lafiya3 years ago
Rahoto: An gano wani gida da ake gini da takardun Kur’ani da Alluna
-
Manyan Labarai5 years ago
Sabuwar damfarar da ta fito a Kano
-
Nishadi5 years ago
An gano daliban da Adam Zango ya dauki nauyin karatun su