Connect with us

Labarai

Kurar ruwa: Matasa sun shiga hannun Bijilante

Published

on

Kwamandan Ƙungiyar Bijilante na unguwar Hayin Diga bayan gidan Rodi, Salisu Aliyu Ɗan Mallam, ya ja hankalin iyaye da su ƙara lura da shige da ficen ƴaƴansu, domin kaucewa faɗawar yaran cikin wani hali.

Salisu Ɗan Mallam ya bayyana hakan ne baya da ƙungiyar su ta kama wasu matasa biyu da zargin satar kurar dakon kaya guda biyu, da zummar su je su siyar.

Ya na mai cewa,”Matuƙar iyayen za su ƙara lura da shige da ficen ƴaƴan na su, to kuwa shakka babu za a samu raguwar faɗawar yaran cikin matsala, ƙungiyar mu za ta miƙa matasa da su ka kama ɗin za mu miƙa matasa wajen jami’an tsaro mafi kusa, domin ɗaukar matakin da ya dace a kan su”. Inji Salisu Aliyu.

Waɗanda a ka kama ɗin sun bayyana nadamar su, inda su ka nemi sassauci, duk da dai wanda a ka ɗaukarwa kurar Shamsu ya ce fatansa shi ne a bashi kurayen tura ruwan nasa.

Wakilin mu Hassan Mamuda Ya’u ya rawaito mana cewar, kwamandan ƙungiyar Bijilante Salisu Ɗan Mallam ya ce, za su ci gaba da bada tsaro a yankin dama sauran sassa daban-daban na jihar Kano, domin samun damar kakkaɓe ɓata gari.

Hangen Dala

Rashin wuta: Muna cikin mawuyacin hali – al’ummar Kano, Katsina da Jigawa

Published

on

Al’ummar jihohin Kano, katsina da Jigawa na fuskantar yanayi mara dadi, Sakamakon karancin samun wutar lantarki daga hukumar KEDCO.

Al’ummar jihohin sun ce iya sa’o’i uku kacal suke samun wutar, wanda hakan ke haifar musu da nakasu a harkokin kasuwancin su.

Wani bincike da jaridar Daily Trust tayi ta ambato yadda masu kananan masana’antu irin su Walda, Cajin Waya, Kankara da masu sana’ar dinki da dai sauran kananan sana’o’i dake amfani da wutar lantarki sun shiga mawuyacin hali.

Kazalika rashin wutar ya shafi hatta bangaren ruwan sha, dama masu sana’ar sayar da Ruwa a irin yankunan Hotoro da sauran irin wuraren dake sayen ruwa, Inda yanzu haka ruwan yayi tashin gwauron zabi a kowace jarka.

Koda dai ana ta bangaren hukumar rarraba hasken wutar lantarkin me kula da shiyyar Kano, Katsina da Jigawa KEDCO sun nemi afuwar al’umma.

Idan za’a tuna dai a makon jiya ne Ministan Wutar lantarki yace ‘yan Nigeria Miliyan 150 na samun wadatacciyar wutar lantarki.

Sai dai kuma a jihohi irin su Kano, Katsina da Jigawa na bayyana damuwa kan karancin Wutar, Inda suka ce bata wuce ta sa’o’i uku suke samu a kowa ce rana.

Continue Reading

Hangen Dala

Rashin wuta:- Muna cikin mawuyacin hali – al’ummar Kano, Katsina da Jigawa

Ci gaba ba ya zuwa sai an samu haɗin kan al’umma – Dagacin Ja’en

Published

on

Dagacin garin Ja’en da ke ƙaramar hukumar Gwale a jihar Kano, Alhaji Isma’il Sa’ad Usman, ya ce hadin kai ne kaɗai zai kawo ci gaba ga kowa ce irin al’umma.

Dagacin ya bayyana hakan ne Jim kaɗan bayan wani taron masu Ruwa da tsaki na Garin Ja’en, wanda Hakimin Gundumar Ɗorayi Barde Kerarriya Alhaji Shehu Kabir Bayero ya shirya, aka gudanar a yankin Ja’en a ƙarshen makon da ya gabata.

“Dukkanin wani ci gaba ba ya zuwa har sai an samu haɗin kan kowa ne bangare na al’umma, “in ji Dagacin”.

Wakilin Dala FM Kano, Ahmad Rabi’u Ja’en ya ruwaito cewa, taron ya samu halartar dukkanin bangarori, na unguwannin Ja’en, da suka haɗar da kungiyar mafarauta da maharba dabma kungiyar malaman makaranta.

Continue Reading

Trending