Connect with us

Manyan Labarai

Ba zan bar Cavani ya tafi ba – Rangnick

Published

on

Kocin rikon kwarya na Manchester United Ralf Rangnick ya ce yana matukar son dan wasan gaba Edinson Cavani ya ci gaba da zama a Old Trafford har zuwa karshen kakar wasa ta bana.

Cavani, wanda ya koma United kan cinikin kyauta daga Paris St-Germain a shekarar 2020, ya rattaba hannu kan kwantiragin da kungiyar har zuwa watan Yuni 2022.

An danganta dan wasan na Uruguay da Barcelona da Juventus a kasuwar musayar ‘yan wasa ta Janairu.

“Ya san cewa tabbas ba zan bar shi ya tafi ba,” inji Rangnick.

Cavani, mai shekaru 34, ya fito ne daga benci inda ya zura kwallo a ragar United a wasan da suka tashi 1-1 da Newcastle a makon da ya gabata, sannan kuma ya hada kai da Cristiano Ronaldo a gaba a wasan da suka doke Burnley da ci 3-1 kwanaki uku bayan haka.

Labarai

Rahoto: Dokar hana shan shisha ta fara aiki gadan-gadan a Kano – Hisba

Published

on

Hukumar Hisba ta jihar Kano ta kai simamen shagunan da ake sayar da Shisha a kan titin Bompai da ke jihar Kano, inda ta samu nasarar kama dillalan Shishar, domin tabbatar da dokar hana sha da siyar da ita.

A zantawar daya daga cikin masu shagunan sayar da Shisha da wakilin mu na ‘yan Zazu, Ibrahim Abdullahi Soron Dinki, ya bayyana cewar, ya yi tunanin dokar hana shan Shisha ta tsaya kan masu wuraren shan Shisha ba masu sayarwa ba.

Mu na da cikakken rahoton a muryar da ke kasa.

Continue Reading

Labarai

Rahoto: Shekaru 10 ina sarrafa Turoso amma ko ciwon kai ban taba yi ba – Mai Turoso

Published

on

Wani magidanci mai sana’ar sarrafa Turoso a yankin Kududdufawa ya ce, sama da shekaru goma ya na aikin sarrafa Turoso, amma ko ciwon kai bai taba yi ba.

Malam Isah Musa Katsinawa mazunin karamar hukumar Ungogo a jihar Kano, ya bayyana hakan ne, a zantawarsa da wakilin mu na ‘yan Zazu, Yusuf Nadabo Isma’il.

Domin jin cikakken rahoton saurari wannan.

Continue Reading

Labarai

Rahoto: Gobara ta lakume ran mutane 3 ciki harda dattijuwa

Published

on

Hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar Kano, ta kai tallafi wani gida da aka samu iftila’in gobara, wanda ta yi sanadiyar rasa mutane Uku  a unguwar Gama A, da ke karamar hukumar Nasarawa.

Wakilin mu na ‘yan zazu, Abba Isah Muhammad, ya rawaito cewar, hukumar karkashin shugabanta Salihu Aliyu Jili, ta kuma kai tallafi gidan iyayen Hanifa, dalibar da aka yi zargin malaminta ya kashe ta.

Domin jin cikakken rahoton saurari wannan.

Continue Reading

Trending