Connect with us

Ilimi

Kwalejin Rumfa: Za mu tallafawa dalibai da marasa lafiya – Tsofaffin Dalibai

Published

on

Kungiyar tsofaffin daliban makarantar Kwalejin Rumfa a jihar Kano aji na 2000, ta ce za su mayar da hankali wajen tallafawa duk wani dalibi da ya ke fama da rashin lafiya, tare da daukar nauyin karatun ‘ya ‘yan marasa karfi.

Mai magana da yawun kungiyar, Jamilu Garba ne ya bayyana hakan yayin taron sada zumunci da su ka saba gudanarwa a duk shekara wanda ya gudana a Asaba.
Ya ce”Kungiyar mu ta dauki nauyin rashin lafiya dalibai da dama ciki harda guda daga cikin mu da ya sami lalurar kwakwalwa”.

A nasa jawabin Jamilu Shehu Kabara, jan hankalin dalibai ya yi da su kara mayar da hankali wajen yin karatu, domin sai da sakamako mai kyau za su sami gurbin shiga makarantun gaba da sakandire.

Jamilu Kabara ya kara da cewar,”Kimanin shekaru 20 keman mu na gudanar da taron wanda kuma kowacce shekara mu ke duba bangaren da za mu bayar da gudunmawa”.

Wakiliyar mu Aisha shehu Kabara ta rawaito cewar, yayin taron sada zumuncin an zabi Ajin na daya ya zama shi zai jagoranci duk kannin sauran ajujowan shekarar ta dubu biyu.

Ilimi

ASUU ta ƙara tsunduma yajin aikin sai baba ta gani

Published

on

Kungiyar malaman jami’o’i ta ƙasa ASUU, ta kara tsawaita yajin aikin da take yi da makonni 12.

ASUU ta dauki matakin ne a wani taron gaggawa na majalisar zartarwarta ta ƙasa da ta yi a sakatariyar ta a Abuja.

Taron gaggawar, wanda ya samu halartar manyan shugabannin reshen ta, an fara shi ne a ranar Lahadi kuma ya ƙare da sanyin safiyar Litinin.

Yajin aikin na watanni biyu da kungiyar ASUU ta ayyana ranar 14 ga Maris, 2022, ya kawo karshe a yau 9 ga watan Mayu, don haka hukumar ta NEC ta ga bukatar kara wa’adin makonni 12 bayan fara yajin aikin sai baba-ta-gani, saboda gaza magance matsalolin da ake takaddama a kai.

Ma’anar tsawaita yajin aikin shi ne, jami’o’in gwamnati za su kasance a rufe.

Continue Reading

Ilimi

Ciyar da dalibai: Gwamnati ta bayar da horo ga masu dafa abinci

Published

on

A ranar Talata ne ma’aikatar jin kai da kula da bala’o’i da ci gaban jama’a ta tarayya, ta horas da masu sayar da abinci 50 a kan tsafta a karkashin shirinta na ciyar da Makarantun.

Shugabar tawagar masu bayar da horo a jihar Naija, Fatima Bissalla, ta ce sun gudanar da wannan horon ne domin baiwa masu sayar da abinci da ilimin da ake bukata kan yadda za su iya kula da tsaftar jikinsu da abinci da kuma yanayin girki, domin amfanin daliban.

“Na yi imanin cewa tsaftar da masu dafa abinci ke yi zai dakile barkewar cututtuka a tsakanin wadanda suka ci gajiyar shirin,” in ji ta.

Ta kara da cewa an bada horon ne, domin tabbatar da cewa, duk dan kwangila, sun rungumi tsaftar muhalli bisa, ka’idar da ma’aikatar ta gindaya musu na su bi tsarin.

Bisallah ta ce, wadanda suka samu horon za su koma kananan hukumominsu, sannan su sauke horon ga sauran masu dafa abinci, ta kara da cewa, jami’an teburi da masu kula da abinci mai gina jiki za su rinka lura da su a yankunan kansilolin.

Har ila yau, Umar Shaba, Manajan Shirye-Shirye na shirin ciyar da Makarantun da ake nomawa a Naija, ya ce, horon ya kara nuna masu yadda dafa abinci irin na tsafta.

Continue Reading

Ilimi

Ganduje ya mika sakon ta’aziyar sa ga iyalan Malaman da suka mutu a hanyar Sumaila

Published

on

Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, a ranar Lahadin ya jajantawa iyalan malaman addinin Islama guda shida da suka rasa rayukansu a wani hatsarin mota da ya rutsa da su yayin da suke dawowa daga karamar hukumar Sumaila kwanan nan.

“Mutuwar wadannan mutanen ba babban rashi ne ga iyalansu kadai ba, har ma ga jihar baki daya. Abin takaici ne,” inji shi.

“Mun samu labarin cewa Malaman da Sheikh Alkassim Zakariyya ya jagoranta sun fara ziyarar aiki karkashin inuwar Imam Malik Islamic Foundation.

A wata sanarwa da babban sakataren yada labaran Abba Anwar ya rabawa manema labarai, ya ruwaito Gwamna Ganduje yana cewa: “Jahar mu ta yi asarar mutane masu tsoron Allah, daga cikinsu akwai Sheikh Alkassim, Malam Isiya Tela, Mustapha Musa Sa’ad, Malam Ishaq, Rummawa da Malam Zakariyya Alkassim Dataka. Allah Ya gafarta musu,” inji shi.

Continue Reading

Trending