Connect with us

Ƙasashen Ƙetare

Kididdiga: Adadin’yan kasar Crotia ya ragu da kaso 10

Published

on

Kasar Croatia ta yi asarar kusan mutane 400,000 kusan kashi 10% na al’ummarta a cikin shekaru goma da suka gabata, saboda ƙaura da ƙarancin haihuwa.

Kamfanin dillancin labarai na Hina ya wallafa cewa, sakamakon farko na ƙidayar 2021 na kasar an gano adadin asarar mutanen da ta yi.

Babban daraktan hukumar kididdiga ta kasar, Lidija Brkovic, ya ce, yawan al’ummar Croatia ya kai miliyan 3.9 ya zuwa ranar 31 ga Agusta, na shekrar 2021, wanda ya ragu da miliyan 4.3 a shekarar 2011.

Alkalumman da a ka yi sun nuna cewa, wasu daga cikin ‘yan kasar sun yi gudun hijira mafi girma a gabashin Croatia da kuma mafi ƙasƙanci a babban birnin Zagreb.

Hukumar ba ta bayyana inda wadanda suka yi hijira suka tafi ba, amma wasu ‘yan Croat na zauna ne a wasu kasashen Tarayyar Turai bayan da kasarsu ta shiga kungiyar a shekara ta 2013.

 

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a Reply

Ƙasashen Ƙetare

Rikicin Ukraine: Rasha ta gudanar da aitasayen soji

Published

on

Rasha ta gudanar da atisayen soji bayan ta tura karin sojoji da jiragen yaki zuwa Belarus, domin atisaye a wata mai zuwa a daidai lokacin da jami’ai ke shirin zama domin tattaunawa ta hanyoyi hudu a birnin Paris kan rikicin gabashin Ukraine.

Mai magana da yawun fadar Kremlin kan Ukraine zai gana da jami’ai daga Faransa da Jamus da kuma Ukraine, domin tattaunawa ta “Normandy format” a birnin Paris domin nuna adawa da yadda Rasha ta girke sojojin ta a kusa da Ukraine wanda ya haifar da fargabar mamayewa.

Rasha ta dage cewa, ba ta shirya mamayewa ba, amma kasashen Yamma sun yi barazanar fuskantar hukunci mai tsanani na tattalin arziki idan hakan ta faru.

Shugaban Amurka Joe Biden ya bayyana a ranar Talata cewa, zai yi la’akari da takunkumi na kashin kai kan shugaban Rasha Vladimir Putin kuma Birtaniyya ta ce, a ranar Laraba ba za ta kawar da yin hakan ba.

Rikicin da ya barke a Ukraine ya haifar da ciniki a kasuwannin Rasha a wannan makon, kuma kudin ruble ya sake raguwa a ranar Laraba.

Continue Reading

Ƙasashen Ƙetare

Fireminista Birtaniya Boris na ci gaba da shan matsi ya sauka daga mukamin sa

Published

on

Firayim Ministan Biritaniya, Boris Johnson, ya na shan matsi da daga ‘yan majalisar dokokin da suka fusata kan jerin kulle-kulle na Korona da ya karya ka’ida a Downing Street.

Johnson ya sha neman afuwar jam’iyyun kuma ya ce, bai san da yawa daga cikinsu ba. Koyaya, ya halarci abin da ya ce, ya na tsammanin wani taron aiki ne a ranar 20 ga Mayu, 2020.

Domin haifar da ƙalubalen shugabanci, 54 daga cikin 360 ‘yan majalisar masu ra’ayin mazan jiya a majalisa dole ne su rubuta wasiƙar rashin amincewa ga shugaban kwamitin jam’iyyar na 1922.

Kimanin ‘yan majalisar masu ra’ayin mazan jiya 20 da suka ci kujerunsu a zaben kasar da ya gabata a shekarar 2019 sun shirya mika wasikun rashin amincewa ga Johnson, in ji jaridar Telegraph. Wasu tsiraru sun riga sun ce sun rubuta irin waɗannan wasiƙun.

Continue Reading

Ƙasashen Ƙetare

Koriya ta Arewa ta kara harba makamai masu linzami

Published

on

Koriya ta Arewa ta harba akalla makamai masu linzami guda biyu, abin da ya jawo suka da kuma neman tattaunawa daga gwamnatin Amurka da ta kara kakaba wasu sabbin takunkumi kan harba makaman da Koriya ta Arewa ta yi.

Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya rawaito cewa, wannan dai shi ne harba makami mai linzami na uku da Koriya ta Arewa ta yi a cikin kasa da makwanni biyu kenan.

Sai dai kasar Amurka ta yi Allah wadai da harba na baya-bayan nan, ta na mai cewa hakan barazana ce ga makwabtan Koriya ta Arewa da kuma kasashen duniya.

A cikin wata sanarwa ta imel mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen Amurka ta sake yin kira da a tattauna.

Sanarwar ta ce, “Muna ci gaba da jajircewa wajen kulla huldar diflomasiyya da DPRK, tare da yin kira gare su da su shiga tattaunawa. Yunkurinmu na kare Jamhuriyar Koriya da Japan ya ci gaba da kasancewa cikin lumana.”

Continue Reading

Trending