Connect with us

Ƙasashen Ƙetare

Masu zanga-zanga a Tunisia sun sha barkonon tsohuwa

Published

on

‘Yan sandan Tunisiya sun yi amfani da tankar ruwa da kulkaye, domin tarwatsa masu zanga-zanga sama da 1,000 da ke kokarin isa tsakiyar birnin Tunis, domin yin zanga-zangar nuna adawa da shugaban kasar na nuna rashin amincewa da takunkumin Korona.

Kasancewar ‘yan sanda da yawa ya hana masu zanga-zanga da dama yin taro a titin Habib Bourguiba, babban titin tsakiyar Tunis wanda shi ne wurin da aka saba gudanar da zanga-zangar ciki har da lokacin juyin juya halin na 2011 wanda ya kawo sauyin dimokiradiyyar kasar.

Ma’aikatar harkokin cikin gida ta kasar ta ce mutane 1,200 ne suka yi zanga-zangar kuma ta ce dakarunta sun yi taka-tsantsan.

Ƙasashen Ƙetare

Jamhuriyar Niger: Ba mu yarda da ƙarin kuɗin Man Fetur ba – Ƙungiyar REPPAD

Published

on

Kungiyar fararan hula ta kasar Nigar mai rajin kare hakkin talaka da kuma tabbata ‘yancin dan Adam (REPPAD), ta ce, bata yarda da karin kudin man fetur a jamhuriyar Niger ba.

Dya daga cikin membobin kungiyar, Isma’ila Abubakar, ya bayyana hakan, yayin taron da kungiyar ta gudanar a babban birnin Yamai, domin bukatar a soke Karin farashin kudin man ferur

Wakilin mu na kasar Niger, Maman Imanite daga birnin Yamai ya hada mana rahoto.

 

Continue Reading

Ilimi

Karo na Farko: Saudiyya ta cire shingen kariyan da ya kewaye ɗakin Ka’aba

Published

on

Shugaban mai kula da harkokin masallatai masu alfarma guda biyu a ƙasar Saudiyya,Sheikh Abdul Rahman Al-Sudais, a ranar Talata ya sanar da dage shingen kariya da aka yi a kewayen dakin Ka’aba.

Sarki Salman ne tun da farko, ya ba da umarnin, yayin da ya ce, wannan matakin ya zo daidai da fara sabuwar kakar Umrah.

Sheikh Al-Sudais ya jaddada cewa, wannan shawarar ta kunshi yadda mahukuntan Saudiyya suke da himma wajen saukakawa mahajjata da maziyartan Masallacin Harami, domin gudanar da ayyukansu cikin aminci da kwanciyar hankali, musamman ganin yadda ake samun karuwar alhazai da maziyartan Masallacin Harami a wannan rana na farkon sabuwar kakar Umrah.

“Shugaban kasa yana aiki tare da dukkanin sassan da ke aiki a Masallacin Harami don karbar maniyyata tare da samar musu da dukkanin ayyuka da kayan aiki,” in ji Sheikh Al-Sudais.

Ya ce, fadar shugaban kasa tana hada hannu da dukkanin bangarorin da abin ya shafa da ke aiki a babban masallacin juma’a, domin karbar maniyyata tare da samar musu da duk wani hidimomi da suka dace da kyakkyawan fata na shugabanni masu hikima.

“Abin lura ne cewa, fadar shugaban kasa ta sanya shinge a kewayen Ka’aba mai alfarma a ranar 1 ga Yuli, 2020, kuma hakan yana aiwatar da umarnin Cibiyar Yaki da Cutar Coronavirus ta Kasa, a matsayin matakin riga-kafi, domin dakile yaduwar cutar. Haka kuma an hana mahajjata Hajji da Umra da masu ziyara tabawa ko sumbantar dakin Ka’aba da dutsen Hajar Al-Aswad”. A cewar Sudais kamar yadda jaridar Saudi Gazzete ta rawaito.

Continue Reading

Ƙasashen Ƙetare

Buhari zai tafi kasar Liberia domin taya su murnar cika shekaru 175 da samun ‘yancin kai

Published

on

Shugaban kasa Muhammadu Buhari, zai bar Najeriya zuwa kasar Laberiya, domin halartar bikin murnar cika shekaru 175 da samun ‘yancin kai, a matsayin kasa mafi tsufa a Afirka bayan samun ‘yancin kai.

Babban mataimaki na musamman kan harkokin yada labarai, da wayar da kan jama’a, Garba Shehu, a wata sanarwa da ya fitar jiya, ya ce, shugaba Buhari zai bar Najeriya a yau Talata, inda zai gabatar da jawabi, inda ya kara da cewa, tafiyar na nuni da muhimmancin da aka baiwa tsaro da walwalar Laberiya da sauran kasashen yammacin Afirka.

“Ana sa ran shugaban kasa ya jaddada muhimmancin mutunta tsarin doka a fadin yankin. Idan babu tsarin doka da tsarin mulki, ba za a iya samun zaman lafiya da ci gaba ba.

“Tafiya zuwa Laberiya ta zo ne a daidai lokacin da rashin kwanciyar hankali na siyasa da kuma dawo da juyin mulkin da aka yi ya inganta tsarin dimokuradiyya na shekaru biyu zuwa talatin a yankin.

“Laberiya da Saliyo tare da Najeriya za su yi zabe a 2023, kuma ana sa ran sShugaba Buhari zai jaddada musu mahimmancin zabe mai inganci da inganci.” In ji Garba Shehu.

Continue Reading

Trending