Connect with us

Ƙasashen Ƙetare

Ba ni da wani zabi illa na dauki matakin luguden wuta a Ukraine – Putin

Published

on

Dakarun Ukraine sun gwabza da mahara na Rasha daga bangarori uku a ranar Alhamis, bayan da Moscow ta kai farmaki ta kasa da ruwa da kuma ta sama, wanda shi ne hari mafi girma da aka kaiwa wata kasar Turai tun bayan yakin duniya na biyu.

Bayan da shugaban kasar Rasha, Vladimir Putin ya shelanta yaki a wani jawabi da ya gabatar a gidan talabijin na kasar, an ji karar fashewar wasu abubuwa da kuma harbe-harbe a birnin Kyiv mai mutane miliyan 3.

Makamai masu linzami sun yi ruwan sama a kan yankunan Ukraine, kuma hukumomi sun ba da rahoton ginshikan dakaru da ke kwarara a kan iyakokin Ukraine daga Rasha da Belarus zuwa Arewa da Gabas, tare da sauka a kan gabar Kudu daga tekun Black Sea da Azov Sea.

Hare-haren ya kawo karshen mummunan yunkurin da shugabannin kasashen yammacin duniya suka yi na diflomasiyya na tsawon makwanni na hana yaki.

Bayan fadan kwana daya, Putin ya shaidawa ‘yan kasuwa a Moscow cewa, ba shi da wani zabi illa ya dauki mataki, yayin da shugabannin kasashen Yammacin duniya suka yi tir da shugaban na Rasha tare da yin alkawarin kakaba takunkumin tattalin arziki.

Ƙasashen Ƙetare

Sojoji Sun yi juyin Mulki a Gabon

Published

on

Sojoji sun bayyana a gidan talabijin na kasar Gabon tare da sanar da karbi mulki.

Sun ce sun soke sakamakon zaben da ka gudanar ranar Asabar, inda aka ayyana shugaba Ali Bongo a matsayin wanda ya lashe zaben.

Hukumar zaben ta ce Mr Bongo ya samu nasara ne da kasa da kashi biyu bisa uku na kuri’un da aka kada a zaben da ‘yan adawa suka ce an tafka magudi.

Sun Kuma ce Hambarar da shi zai kawo karshen mulkin shekaru 53 da iyalan gidansu ke yi a Gabon.

Sojoji 12 ne suka bayyana a gidan talabijin dake sanar da soke sakamakon zaben tare da rusa dukkan hukumomin kasar.

Daya daga cikin sojojin ya fada a tashar talabijin ta Gabon 24 cewa, “Mun yanke shawarar kare zaman lafiya ta hanyar kawo karshen mulkin da ake yi a yanzu.”

Mr Bongo ya hau karagar mulki lokacin da mahaifinsa Omar ya rasu a shekara ta 2009.

Continue Reading

Ƙasashen Ƙetare

Sojoji sunyi juyin Mulki a jamhuriyar Nijar

Published

on

Rahotanni daga jamhuriyar Nijar na cewa Sojojin Kasar sun yi juyin Mulki, tare da sanar da kawo karshen mulkin shugaba Muhammad Bazum.

Cikin sanarwar da suka bayar a gidan telebijin din Kasar, jagoran tawagar sojojin Kanal Amadu Abdramane yace “mun kawo karshen mulkin shugaba Muhammad Bazum tare da karbe dukkanin Wani Iko”.

Sojojin dai sun bayar da dalilin halin rashin tabbas da Kuma Matsin tattalin arziki a kasar.

Tuni dai sojojin suka garkame dukkanin iyakokin Kasar tare da Sanya dokar takaita zirga zirga daga karfe 10 na dare zuwa 6 na safe.

Tun a safiyar laraba ne dai aka wayi gari da fara wancan yunkuri, Wanda yanzu haka ta tabbata, Kasar Nijar na hannun sojoji, Wanda shi ne Karo na hudu ana gudanar da juyin mulkin a jamhuriyar Nijar.

Continue Reading

Ƙasashen Ƙetare

An tsaurara tsaro a fadar shugaban Kasar Nijar

Published

on

Rahotanni daga Jamhuriyar Nijar, na nuni da cewa dakarun da ke gadin fadar shugaban ƙasa sun rufe duk wata hanyar shiga fadar a wani lamari da ba a kai ga ganowa ba.

Sai dai rahotanni na cewa yanzu haka wasu daga cikin tsofaffin shugabannin ƙasar ta Nijar na tattaunawa da sojojin domin sasanta lamarin.

Karin bayani nan tafe….

Continue Reading

Trending