Connect with us

Ƙasashen Ƙetare

Shugaban kasar Ukraine ya bukaci daukin gaggawa daga duniya

Published

on

Makamai masu linzami sun fada babban birnin Ukraine a ranar Juma’a yayin da sojojin Rasha suka matsa kaimi, kuma shugaban kasar Ukraine Volodymyr Zelenskiy ya roki kasashen duniya da su kara kaimi, ya na mai cewa takunkumin da aka sanar bai wadatar ba.

Ire-iren hare-haren jiragen sama sun yi ta kururuwa a kan birnin mai mutane miliyan 3, inda wasu ke fakewa a tashoshi na karkashin kasa, kwana guda, bayan da shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ya kaddamar da wani hari da ya girgiza duniya.

Jami’an kasar Ukraine sun ce, an harbo wani jirgin kasar Rasha tare da fada cikin wani gini a birnin Kyiv cikin dare, lamarin da ya sa ya kone tare da jikkata mutane takwas.

Wani babban jami’in Ukraine ya ce, sojojin Rasha za su shiga wasu yankuna da ke wajen babban birnin kasar nan gaba a yau Juma’a kuma sojojin na Ukraine suna kare wurare a bangarori hudu duk da cewa sun fi yawa.

An yi rugugu da tagogi daga wani bene mai hawa 10 da ke kusa da babban filin jirgin saman Kyiv, inda wani rami mai tsawon mita biyu cike da tarkace ya nuna inda harsashi ya fado kafin wayewar gari. Wani dan sanda ya ce, an jikkata mutane a can amma ba a kashe su ba.

Ƙasashen Ƙetare

Sojoji Sun yi juyin Mulki a Gabon

Published

on

Sojoji sun bayyana a gidan talabijin na kasar Gabon tare da sanar da karbi mulki.

Sun ce sun soke sakamakon zaben da ka gudanar ranar Asabar, inda aka ayyana shugaba Ali Bongo a matsayin wanda ya lashe zaben.

Hukumar zaben ta ce Mr Bongo ya samu nasara ne da kasa da kashi biyu bisa uku na kuri’un da aka kada a zaben da ‘yan adawa suka ce an tafka magudi.

Sun Kuma ce Hambarar da shi zai kawo karshen mulkin shekaru 53 da iyalan gidansu ke yi a Gabon.

Sojoji 12 ne suka bayyana a gidan talabijin dake sanar da soke sakamakon zaben tare da rusa dukkan hukumomin kasar.

Daya daga cikin sojojin ya fada a tashar talabijin ta Gabon 24 cewa, “Mun yanke shawarar kare zaman lafiya ta hanyar kawo karshen mulkin da ake yi a yanzu.”

Mr Bongo ya hau karagar mulki lokacin da mahaifinsa Omar ya rasu a shekara ta 2009.

Continue Reading

Ƙasashen Ƙetare

Sojoji sunyi juyin Mulki a jamhuriyar Nijar

Published

on

Rahotanni daga jamhuriyar Nijar na cewa Sojojin Kasar sun yi juyin Mulki, tare da sanar da kawo karshen mulkin shugaba Muhammad Bazum.

Cikin sanarwar da suka bayar a gidan telebijin din Kasar, jagoran tawagar sojojin Kanal Amadu Abdramane yace “mun kawo karshen mulkin shugaba Muhammad Bazum tare da karbe dukkanin Wani Iko”.

Sojojin dai sun bayar da dalilin halin rashin tabbas da Kuma Matsin tattalin arziki a kasar.

Tuni dai sojojin suka garkame dukkanin iyakokin Kasar tare da Sanya dokar takaita zirga zirga daga karfe 10 na dare zuwa 6 na safe.

Tun a safiyar laraba ne dai aka wayi gari da fara wancan yunkuri, Wanda yanzu haka ta tabbata, Kasar Nijar na hannun sojoji, Wanda shi ne Karo na hudu ana gudanar da juyin mulkin a jamhuriyar Nijar.

Continue Reading

Ƙasashen Ƙetare

An tsaurara tsaro a fadar shugaban Kasar Nijar

Published

on

Rahotanni daga Jamhuriyar Nijar, na nuni da cewa dakarun da ke gadin fadar shugaban ƙasa sun rufe duk wata hanyar shiga fadar a wani lamari da ba a kai ga ganowa ba.

Sai dai rahotanni na cewa yanzu haka wasu daga cikin tsofaffin shugabannin ƙasar ta Nijar na tattaunawa da sojojin domin sasanta lamarin.

Karin bayani nan tafe….

Continue Reading

Trending