Connect with us

Ƙasashen Ƙetare

Wata ‘yar Jarida ‘yar kasar Rasha ta rasa ranta a harin da Rashan ta kai a Ukraine

Published

on

An kashe wata ‘yar jarida ‘yar kasar Rasha Oksana Baulina, da ke aiki a kafar yada labaran The Insider, a lokacin da take bayar da rahoto kan rikicin Kyiv na Ukraine.

An kashe Baulina ne lokacin da sojojin Rasha suka kai hari a wata unguwa a birnin Kyiv, kafar yada labarai ta ce a ranar Laraba ne lamarin ya faru, a cewar wani rahoto da kungiyar ‘yan jarida ta duniya (IFJ) ta tabbatar.

A halin da ake ciki kuma, IFJ da kungiyar ‘yan jarida ta Turai (EFJ) sun yi Allah wadai da harin da sojojin Rasha ke kaiwa fararen hula.

ksana Baulina, a cewar rahoton, a baya ya yi aiki da kungiyar yaki da cin hanci da rashawa ta jagoran ‘yan adawa na Rasha Alexey Navalny.

Ta mutu tare da wani farar hula tare da jikkata wasu mutane biyu. Baulina ya yi aiki da gidauniyar yaki da cin hanci da rashawa ta Navalny har sai da aka ayyana ta a matsayin kungiyar masu tsattsauran ra’ayi a bara. Hakan ne ya sa ta fice daga kasar ta kuma ci gaba da bayar da rahoto kan cin hanci da rashawa a Rasha ga jaridar The Insider. Bayan da Rasha ta mamaye Ukraine wata guda da ta wuce, Baulina ya buga rahotanni da yawa a cikin The Insider daga Kyiv da Lviv a yammacin Ukraine.

Tuni shugaban kungiyar ‘yan jarida ta kasar Ukraine Sergiy Tomilenko, ya tabbatar da mutuwar Baulina a cikin wata sanarwa da ya fitar ta shafin Facebook, inda ya ce, ta na tsaka da bayar da rahoto ne kan sakamakon wani ruwan harsasai da aka yi a lokacin da aka sake samun sabon harbe-harbe. Tun da farko, kungiyar Tomilenko ta ce an kuma kashe wani mai daukar hoto daga wani gidan talabijin na kasar a birnin Mariupol da ke kudancin kasar da aka yi wa kawanya.

Hoton ‘yar Jaridar mai suna Oksana.

Ƙasashen Ƙetare

Sojoji Sun yi juyin Mulki a Gabon

Published

on

Sojoji sun bayyana a gidan talabijin na kasar Gabon tare da sanar da karbi mulki.

Sun ce sun soke sakamakon zaben da ka gudanar ranar Asabar, inda aka ayyana shugaba Ali Bongo a matsayin wanda ya lashe zaben.

Hukumar zaben ta ce Mr Bongo ya samu nasara ne da kasa da kashi biyu bisa uku na kuri’un da aka kada a zaben da ‘yan adawa suka ce an tafka magudi.

Sun Kuma ce Hambarar da shi zai kawo karshen mulkin shekaru 53 da iyalan gidansu ke yi a Gabon.

Sojoji 12 ne suka bayyana a gidan talabijin dake sanar da soke sakamakon zaben tare da rusa dukkan hukumomin kasar.

Daya daga cikin sojojin ya fada a tashar talabijin ta Gabon 24 cewa, “Mun yanke shawarar kare zaman lafiya ta hanyar kawo karshen mulkin da ake yi a yanzu.”

Mr Bongo ya hau karagar mulki lokacin da mahaifinsa Omar ya rasu a shekara ta 2009.

Continue Reading

Ƙasashen Ƙetare

Sojoji sunyi juyin Mulki a jamhuriyar Nijar

Published

on

Rahotanni daga jamhuriyar Nijar na cewa Sojojin Kasar sun yi juyin Mulki, tare da sanar da kawo karshen mulkin shugaba Muhammad Bazum.

Cikin sanarwar da suka bayar a gidan telebijin din Kasar, jagoran tawagar sojojin Kanal Amadu Abdramane yace “mun kawo karshen mulkin shugaba Muhammad Bazum tare da karbe dukkanin Wani Iko”.

Sojojin dai sun bayar da dalilin halin rashin tabbas da Kuma Matsin tattalin arziki a kasar.

Tuni dai sojojin suka garkame dukkanin iyakokin Kasar tare da Sanya dokar takaita zirga zirga daga karfe 10 na dare zuwa 6 na safe.

Tun a safiyar laraba ne dai aka wayi gari da fara wancan yunkuri, Wanda yanzu haka ta tabbata, Kasar Nijar na hannun sojoji, Wanda shi ne Karo na hudu ana gudanar da juyin mulkin a jamhuriyar Nijar.

Continue Reading

Ƙasashen Ƙetare

An tsaurara tsaro a fadar shugaban Kasar Nijar

Published

on

Rahotanni daga Jamhuriyar Nijar, na nuni da cewa dakarun da ke gadin fadar shugaban ƙasa sun rufe duk wata hanyar shiga fadar a wani lamari da ba a kai ga ganowa ba.

Sai dai rahotanni na cewa yanzu haka wasu daga cikin tsofaffin shugabannin ƙasar ta Nijar na tattaunawa da sojojin domin sasanta lamarin.

Karin bayani nan tafe….

Continue Reading

Trending