Connect with us

Ƙasashen Ƙetare

Da Duminsa: Maniyaciyyar jihar Nasarawa ta rasu a kasar Saudiyya

Published

on

Maniyaciyar jihar Nasarawa mai suna, Hajiya Aisha Ahmad, ta rasu a yau Laraba sakamakon rashin lafiya a kasar Saudiyya.

Aisha Ahmed ‘yar karamar hukumar Keffi a jihar Nasarawa ta rasu ne bayan ta yi fama da gajeruwar rashin lafiya kamar yadda babban sakataren hukumar jin dadin alhazai ta jihar Nasarawa Idris Al-makura ya tabbatar.

Al-Makura ya shaida wa Kamfanin Dillancin Labarai na kasa ranar Laraba a birnin Makkah na kasar Saudiyya cewa, Aisha ba ta da wani labari na rashin lafiya kafin ta tashi daga Najeriya.

Ya ce “An fara kai ta Asibitin Hukumar Alhazai ta kasa da ke Makkah, sannan aka kai ta Asibitin Sarki Abdulaziz inda ta rasu. An sanar da iyali yadda ya kamata.

Ya kuma ce, “Mun aika wa dangin ta faifan bidiyo na tsarin tabbatar da mutuwarta, zuwa ga jana’izar ta, kuma a karshe mun yi jana’izar ta,” in ji shi.

Ƙasashen Ƙetare

China ta yi Allah wadarai da kisan da aka yi a Kano

Published

on

Kungiyar ‘yan kasuwan kasar China a Najeriya CBCAN, ta mayar da martani kan kisan da aka yi wa Ummukulsum Buhari a Kano.

Matar mai suna Ummita, an zargi wani dan kasar China Geng Quanrong ne ya kashe ta a daren ranar Juma’a.

Wata sanarwa da shugaban kungiyar CBCAN a jihar Kano, Mike Zhang ya fitar a ranar Litinin, ya yi Allah wadai da wannan mummunan kisan.

Zhang ya ce, kamata ya yi a bar hukumomin tsaro da abin ya shafa su kula da wannan aikin cikin kwarewa.

Ya ce, “Al’ummar Sinawa a Kano suna goyon bayan dokar da ta dace a kan dan kasar mu,” in ji shi.

Ya ce, jama’ar kasar Sin sun yaba da karramawar da aka yi musu a Kano kawo yanzu, kuma za su ci gaba da bin doka da oda, da ba da gudummawa ga ci gaban jihar.

Sanarwar ta kuma jajantawa iyalan mamacin wanda ta kammala karatunta na kimiyyar aikin gona a jami’ar Kampala.

Ummita mai shekaru 23 ta kasance a cikin hukumar yi wa kasa hidima (NYSC).

Continue Reading

Ƙasashen Ƙetare

Ban kwanan karshe na Sarauniya Elizabeth ta biyu

Published

on

Shugabannin kasashen duniya sama da dari ciki harda shugaban kasar Amurka Joe Biden da kuma mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbanjo tare da kuma wakilan gwamnati daga kasashe dari biyu ne suka halarci jana’izar Sarauniyar Burtaniya, Elizabeth ta biyu da aka gudanar a birnin Landan a ranar Litinin.

An dai shafe tsawon kwanaki goma sha biyu a na gudanar da bukukuwan mutuwar Sarauniyar da ta shafe shekaru 70 ta na mulki a Burtaniya, daidai lokacin da ta shafe tsawon shekaru 96.

Sama da mutane dubu dari da saba’in ne suka yi jern gwano a bakin fadar Windsor, wurin da za a binne Sarauniya kusa da iyayen ta mijinta Yarima Philips tare da sauran sarakunan da suka shude a yankin Burtaniya.

Bikin jana’aizar dai na mutuwar Sarauniya, shi ne biki mafi girma a Burtaniya sama da shekaru hamsin da suka gabata, za kuma a bar ahalinta su shiga wajen binne ta, yayin da za a dakatar da ‘yan jaridu daga shiga wurin da za a binne ta, kamar yadda ahalin ta suka bukaci hakan.

Continue Reading

Ƙasashen Ƙetare

Zelensky ya tsallake rijiya da baya

Published

on

Wani Hatsarin mota ya rutsa da shugaban kasar Ukraine Volodymyr, Zelensky a Kyiv babban birnin kasar.

A wata sanarwar da mai magana da yawun shugaban ya fitar ya ce, wata motar fasinja ce ta daki tawagar motocin da shugaban ke ciki ranar Laraba a birnin na Kyiv.

Shugaban dai bai samu munanan raunuka ba kamar yadda likitansa ya bayyana hakan. In ji BBC.

Tuni dai aka yi wa diraban motar fasinjan magani, yayin da kuma daga bisani aka dauke shi a motar daukar masara lafiya

Hadarin ya faru ne bayan da Mista Zelensky ya ziyarci birnin Izyum da ke Arewa maso Gabashin kasar, wanda dakarunsa suka kwace daga hannun sojojin Rasha.

Continue Reading

Trending