Connect with us

Labarai

NDLEA ta kama wata makauniya da ta tabar Wiwi buhu 24

Published

on

Hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta NDLEA, ta tabbatar da cafke wata ‘yar kasuwa mai suna Celina Ekeke, a unguwar Obunku, a karamar hukumar Oyigbo ta jihar Ribas.

Kakakin jihar Emmanuel Ogbumgbada, a wata sanarwa da ya fitar, ya ce, an kama matar da ake zargi makauniya ce, an kama ta da buhu 24 na tabar wiwi mai nauyin kilogiram 231.2.

Sanarwar ta ci gaba da cewa, “A ranar Laraba, 29 ga watan Yuni, 2022, da misalin karfe 2 na safe, jami’an hukumar yaki da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa reshen Etche na jihar Ribas sun gudanar da bincike a unguwar Obunku dake karamar hukumar Oyigbo inda suka kama wata Celina Ekeke, sanannen dillalin magunguna da buhu 24 na cannabis sativa mai nauyin 231.2kg.

“Ta kasance cikin jerin masu sa ido a hukumar tun da dadewa, inda take amfani da gurbatattun kafafunta wajen yin kwalliya da sayar da muggan kwayoyi. A yanzu haka tana gudanar da bincike a hedikwatar rundunar jihar Ribas.”

Labarai

Ranar ‘yan jaridu ta duniya: Aljanu na satar labarai daga sama – Danfodio

Published

on

Masanin harkokin aljanu a jihar Kano, Abdullahi Idris Danfodio ya ce, aljanu na satar labarai daga sama domin fada wa al’umma.

Abdullahi Idris Danfodio, ya bayyana hakan ne, a zantawarsa da wakilin mu na ‘yan Zazu, Ibrahim Abdullahi Soron Dinki.

Akwai cikakken rahoton a muryar da ke kasa.

Continue Reading

Labarai

Rahoto: Da zarar PI ta fashe za mu yi abinda za mu taimaka wa mutane – Matashi

Published

on

Wani matashi a jihar Kano, Auwal Muhammad Musa, mai jiran fashewar PI ya ce, da zarar ta fashe za su gudanar da abubuwan da za su taimakawa al’umma.

Auwal Muhammad, ya bayyana, ya bayyana hakan ne, yayin zantawarsa da wakilin mu na ‘yan Zazu, Yusuf Nadabo Isma’il.

Domin jin cikakken rahoton saurari wannan.

Continue Reading

Labarai

Rahoto: Matasa masu jiran fashewar PI na fama da matsalar damuwa – Masani

Published

on

Wani masani da ke karatun babban Digiri a jami’ar Bayero, bangaren nazarin halayyar Dan Adam a jihar Kano, Shu’aibu Lawan Matawalle, ya ce, akwai damuwa ga matasan da ke jiran fashewar PI, domin babu wanda yake samun kudi haka kawai ba tare da yayi kasuwanci ba.

Shu’aibu  Matawalle, ya bayyana hakan ne, a zantawarsa da wakilin mu na ‘yan Zazu, Yusuf Nadabo, dangane da yadda matasa ke jiran fashewar PI.

Muna da cikakken rahoton a muryar da ke kasa.

Continue Reading

Trending