Manyan Labarai
Da Duminsa: Tinubu ya ki amincewa da Ganduje da El-Rufa’i ya gwammace ya zabi mataimaki a Borno

Rahotanni na nuni da cewa, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC mai mulki a zaben 2023, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya ki amincewa da damar zaben gwamna Nasir El-Rufai na jihar Kaduna ko kuma gwamna Abdullahi Ganduje na jihar Kano a matsayin abokin takararsa.
Rahotanni sun bayyana cewa, Ana sa ran Tinubu, tsohon gwamnan jihar Legas, zai zabi gwamna Babagana Zulum na jihar Borno ko kuma tsohon gwamnan jihar, Sanata Kashim Shettima.
An tattaro cewa, Tinubu zai dawo daga kasar Faransa ya bayyana abokin takararsa kafin ranar 15 ga watan Yuli da hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta tsayar.
Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, wanda ya takaita bincikensa a jihohin Borno, Kano, da Kaduna, inda dukkanin masu son tsayawa takara Musulmi ne, ya ki zabar Nasir El-Rufai duk da irin rawar da ya taka wajen fitowar Tinubu.
Wani na hannun damar Tinubu ya shaidawa jaridar The PUNCH cewa, ana sa ran tsohon gwamnan zai tuntubi wanda zai zaba tsakanin Zulum da Shettima idan ya dawo daga kasar Faransa.
Majiyar ta ci gaba da cewa, “Ya rage mutane biyu kacal da dan takarar Asiwaju zai zaba a tsakanin su. Sun hada da gwamnan jihar Borno, Babagana Zulum, da kuma magabacinsa, Kashim Shettima, wanda shine sanata mai wakiltar Borno ta tsakiya. Duk abubuwa daidai suke, ya kamata abokin takara ya fito tsakanin waɗannan mutane biyu.

Manyan Labarai
Da na hadu da kwankwaso da sai na mare shi – Ganduje

Tsohon Gwamnan Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje yace da sun hadu da kwankwaso da akwai yiyuwar ya mare shi, a fadar shugaban kasa.
Tsohon Gwamnan ya bayyana Hakan ne yayin wata ganawa da gidan television na channels, yayin da yake martani Kan ganawar shugaban kasa Asuwaju Bola Ahmad Tinubu da Kuma jagoran jam’iyyar NNPP Sanata Rabiu Musa Kwankwaso a yammacin wannan juma’a.
” Nasan yana gidan Amma bamu hadu ba, da mun hadu akwai yiyuwar na kwada masa Mari” inji Ganduje.
Idan za’a iya tunawa dai kwanakin baya shugaban kasa Asuwaju Bola Ahmad Tinubu yayi wata ganawa da kwankwaso, lamarin da aka jiyo tsohon Gwamnan na korafi cewa ba’a Yi musu adalchi ba, Koda dai a wancan lokaci, Ganduje ya musanta, ta bakin tsohon kwamishinan yada labarai Muhammad Garba, inda yace ba muryar Ganduje bace.
Wannan dai na zuwa ne a Gabar da gwamnatin Kano ke cigaba da rushe wuraren da tayi zargin gwamnatin baya ta Abdullahi Umar Ganduje ta cefanar ba bisa ka’ida ba.

Manyan Labarai
Gargadin Gwamnatin Kano Kan masu kaya a wuraren gwamnati

Gwamnatin jihar Kano ta gargadi dukkanin masu kaya a wuraren da tayi zargin gwamnatin baya ta cefanar ba bisa ka’ida ba, dasu kwashe kayan su cikin gaggawa.
Cikin wata sanarwa da sakataren gwamnatin Dakta Abdullahi Baffa Bichi ta fitar ta bayyana cewa, dukkanin masu kaya a shagunan da aka gina a jiki ko cikin makarantu, Maƙabartu, Asibitoci, Masallatai, gefen badala, Filayen ma’aikatu, Filayen wasanni da sauran wuraren shakatawa mallakin gwamnati da cewa suyi gaggawar kwashe dukkanin kayan su dake cikin shagunan da aka gina a waƴannan gurare ba tare da ɓata lokaci ba.

Manyan Labarai
Abba Gida Gida ya fara rusau

Gwamnatin jihar Kano ta fara rushe wasu gine gine da aka yi su a wuraren gwamnati Ba bisa ka’ida ba.
A cikin daren Asabar din nan ne tawagar Kwamitin kar ta kwana mai lura da rushe gine gine ta fara da rushe wani sabon rukunin shaguna mai kunshe da sama da shaguna 90 dake jikin filin sukuwa a jihar Kano.
Mai magana da yawun gwamnan Kano Sunusi Ahmad Bature Dawakin Tofa ya bayyana cewar wannan aiki somin tabi ne domin batun rushe gine ginen da aka yi su akan filayen jama ar Kano lamari ne da babu gudu babu ja da baya kamar yadda gwamna Engr Abba Kabir Yusif ya bayyana a lokacin da yake yakin neman zabe.
Tawagar kwamitin na kar ta kwana zai cigaba da rushe dukkan wasu gine gine da aka yi su ba bisa kaida ba.

-
Nishadi4 years ago
Ina neman mijin aure – Rayya
-
Manyan Labarai3 years ago
KAROTA: An baiwa Baffa Babba wa’adin kwanaki bakwai
-
Labarai3 years ago
Hamisu Breaker ya kai kan sa wajen ‘yan sanda
-
Nishadi4 years ago
Mansura Isah ta yi kaca-kaca da Sadiya Haruna
-
Labarai3 years ago
Auren dan Panshekara da ba Amurkiya ya samu cikas
-
Lafiya1 year ago
Rahoto: An gano wani gida da ake gini da takardun Kur’ani da Alluna
-
Nishadi4 years ago
An gano daliban da Adam Zango ya dauki nauyin karatun su
-
Manyan Labarai3 years ago
Sabuwar damfarar da ta fito a Kano