Connect with us

Labarai

Mun samu rashin fitowar jama’a wajen yin rijistar katin zabe a Katsina – INEC

Published

on

Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC), ta bayyana damuwarta kan yadda mazauna yankin jihar  Katsina suka yi rijistar katin zabe na dindindin (PVC) a sabbin rumfunan zabe 1,750 da aka kafa a jihar.

Alhaji Jibril Zarewa, kwamishinan zabe na INEC a jihar, ya bayyana hakan a wata hira da kamfanin dillancin labarai na kasa NAN a ranar Juma’a a Katsina.

Ya ce, bayan shekara daya da fara rajistar PVC, an samu rashin fitowar jama’a domin yin rajista a sabbin rumfunan zabe da aka kafa.

A cewar Zarewa, “A watan Mayun 2022 da muka yi bincike, mun gano a cikin sabbin rumfunan zabe 1,750 da aka kafa, kusan guda 1,200 ba su da mutane sama da 50 da suka yi rajista a kowannen su.

“Wannan rijistar ta ƙunshi canja wuri. Wasu rumfunan zabe ba su da rijista, yayin da wasu ba su wuce mutane 50 da suka yi rajista ba.

“Ko da yake ana iya danganta hakan da dakatar da hanyoyin sadarwa a kananan hukumomi 17 daga cikin 34 na kananan hukumomi kusan watanni biyar saboda matsalar tsaro.

“Muna kira ga al’ummar yankunan da aka kirkiro sabbin rumfunan zabe da su je su yi rajista, domin INEC a shirye take a kodayaushe.

Ya bayyana cewa da farko akwai rumfunan zabe 4,902 a jihar amma tare da samar da karin rumfunan zabe 6,652 a halin yanzu.

Labarai

Marayu na buƙatar tallafi sosai – Kwamared Abu Saleem

Published

on

Shugaban ƙungiyar tallafawa Marayu da ci gaban al’umma ta ƙaramar hukumar Birnin Kano Kwamared Adam Umar Abu Saleem, ya ce ƙarancin samun tallafi daga masu ƙarfi ne ke sanyawa Marayu ke faɗawa cikin mawuyacin hali.

Kwamared Adam Abu Saleem na wannan jawabin ne yayin zantawarsa da gidan rediyon Dala FM, lokacin musabaƙar Alƙur’ani mai girma na marayu ƴan ƙaramar hukumar Birni 5 yayin da ɗalibi dake Karkasara Ja’afar Aliyu Abubakar ya zama gwarzon shekara na ƙaramar hukumar wanda aka ɗauki nauyin al’amuran rayuwarsa baya ga kyaututtuka da ya samu, wanda Musabaƙar ta gudana cikin Firamen Salanta a ranar Asabar.

Wakilinmu Hassan Mamuda Ya’u ya rawaito cewa Kwamared Adam ya ce sukan shirya Musaɓakar ne domin zaburar da Marayu akan harkokin karatun Alkur’ani mai girma, da kuma rage musu wani tunanin maraici da suke kasancewa a maban-banta lokuta.

Continue Reading

Labarai

Lokacin zaɓe: Rundunar ƴan sanda ta shirya daƙile tayar da tarzoma – SP Kiyawa

Published

on

Rundunar ƴan sandan jihar Kano ta ce, ta shirya wajen samar da tsaro, tare da ɗaukar matakin da ya dace ga ɓata garin da suke shirin tayar da tarzoma.

Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ƴan sandan jihar Kano SP Abdullahi Haruna Kiyawa ne ya bayyana hakan ga Wakilinmu Hassan Mamuda Ya’u a yau juma’a, yayin da yake tsokaci kan shirin da rundunar su ta yi kan zaɓe.

Continue Reading

Labarai

Al’umma da su dage da addu’a a lokacin da za su fita zaɓen gwamna da na ƴan majalisa – Malam Ali Ɗan Abba

Published

on

Gamayyar rukunin wasu Limamai da Malaman jihar Kano sun buƙaci al’umma da su dage da yin addu’a musamman ma a lokacin da zasu fita zaɓen gwamna da na ƴan majalisar jiha, domin hakan zai taimaka wajen yin zaɓen cikin kwanciyar hankali da lumana.

Shugaban magayyar limamai da malaman da suka fito daga Ɗariyar Tijjaniyya, Kaɗiriyya da Izala, da kuma Mahaddata Alƙur’ani mai girma na Kano Malam Ali Ɗan Abba ne ya bayyana hakan, yayin wani taron zaman lafiya da suka gudanar a ranar Alhamis.

Malam Ali Ɗan Abba, ya kuma shawarci al’umma da su gujewa tayar da tarzoma a yayin zaɓen, domin zama lafiya yafi komai mahimmanci a rayuwa.

Ya kuma ce kamata yayi suma malamai su ƙara dagewa da yin addu’in da suke yi, domin samun shugabanni na gari da za su yiwa al’umma adalci.

Continue Reading

Trending