Connect with us

Labarai

Karancin man fetur a Najeriya gazawar gwamnati ne – NUPENG

Published

on

Kungiyar ma’aikatan man fetur da iskar gas ta kasa NUPENG, ta zargi gwamnatin tarayya da laifin karancin man fetur da ake fama a Najeriya.

NUPENG ta ce karancin man fetur ya samo asali ne sakamakon gazawar gwamnati.

Da yake jawabi yayin taron wakilai karo na 5 na kungiyar direbobin tankar mai karakshin reshen NUPENG a Ibadan, babban birnin jihar Oyo, shugaban kungiyar, Kwamared William Akporeha, ya ce, maimakon dora laifin karancin man fetur a kan direbobin tankar man fetur ba su ba ne laifin gwamnati ne, wanda ya ce ta ki gina sabbin matatun mai a cikin shekaru 30 zuwa 40 da suka wuce.

Akporeha ya ce: “Me ya sa ake karancin man fetur? Ina man yake? Karancin ba direbobin tanka ne suka haddasa shi ba,  idan man fetur yana samuwa, membobin mu za su kawo shi.

“Ta hanyar shigo da kayan, zai samar da ayyukan yi. Matatun man da muke da su a yau sojoji ne suka gina su tun shekaru 30 zuwa 40 da suka wuce.” In ji shi.

Baba Suda

NNPP:- Kwankwaso ya sulhunta rikicin jamiyyar

Published

on

Rahotanni daga Abuja sun tabbatar da jagoran kwankwasiyya Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya yi wani zama da Dan majalisar tarayya Mai wakiltar kananan hukumomin Rimin Gado, Tofa da Dawakin Tofa, Wato Honorable Abdulkadir Jobe, da kuma Daraktan yada labaran Gwamnan Kano Honorable Sunusi Bature Dawakin Tofa.

 

Ganawar wadda ta gudana a yammacin wannan Alhamis ta kawo karshen Jan Zaren dake faruwa tsakanin Dan majalisar da kuma Sunusi Bature.

 

A baya bayan nan dai an kai ruwa rana tsakanin su, Inda kowa ne bangare ke mayar da martani.

Abdulkadir Jobe da kuma Sunusi Bature dukkanin su mabiya jamiyyar NNPP ne tsagin kwankwasiyya.

Continue Reading

Labarai

Real Madrid ta kaddamar da Alexander

Published

on

Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Real Madrid ta ƙaddamar da ɗan wasa Trent Alexander Arnold a yau a matsayin ɗan wasan ta

Inda shugaban ƙungiyar Flerontino Perez yace yau suna matuƙar Farin ciki kasancewar sun mallaki babban ɗan wasan baya a duniya.

 

Shima ɗan Wasa Arnold ya bayyana cewa yana cikin farin ciki kuma mafarkin sa ya cika na zama ɗan Wasan Madrid a yau.

Continue Reading

Daurin Boye

Zan shiga kawancen ‘yan jamiyyar hamayya – tsohon Minista

Published

on

Tsohon ministan sufurin Najeriya, Rotimi Amaechi ya ce a shirye yake don shiga ƙawancen ƴan jamiyyar hamayya domin ƙalubalantar Shugaba Bola Tinubu a zaben 2027

A wata hira da BBC, tsohon gwamnan na jihar Rivers ya ce suna ƙoƙarin samar da haɗakar siyasar da za ta samar da sauyi a ƙasar.

Amaechi wanda ɗan jam’iyyar APC ne  ya nuna damuwa kan abin da ya ƙira halin ƙuncin rayuwa da ƙasar ke ciki.

Amaechi ya ce bai cire tsammanin yin takarar shugaban ƙasa ba, illa lokaci ne kawai zai tantance.

Continue Reading

Trending