Connect with us

Labarai

Da Ɗuminsa: Ma’aikatan NAFDAC sun janye yajin aikin sati 6 da suka tsunduma

Published

on

Ma’aikatan hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta kasa (NAFDAC), a ranar Litinin, sun dakatar da yajin aikin da suka kwashe makonni shida suna yi, a fadin kasar nan.

Ma’aikatan dai mambobin kungiyar ma’aikatan lafiya ne da ma’aikatan lafiya ta ƙasa (MHWUN).

Mataimakin shugaban kungiyar, Idzi Isua, ya tabbatar da faruwar lamarin, a yayin taron kungiyar a safiyar ranar Litinin. In ji Solacebase.

Isua ya ce, kungiyar ta yanke shawarar dakatar da yajin aikin ne bayan wata yarjejeniya da ta kulla da mahukunta.

Kungiyar ta tsunduma yajin aikin ne a ranar 21 ga watan Yuni, 2022, domin nuna rashin amincewa da wasu abubuwa, rashin jin dadin jama’a da basussukan ci gaba da ba a biya ba.

Labarai

Rahoto: Mu nisanci abinda Allah Ya hana domin samun saukin rayuwa – Limamin Tukuntawa

Published

on

Limamin masallacin juma’a na Masjidul Kuba da ke unguwar Tukuntawa a jihar Kano, Malam Ahmad Ali, ya ce, al’umma su duba tsakanin su da Allah tare da nisantar abinda ya hana, domin saukin tsadar rayuwa.

Malam Ahmad Ali, ya bayyana hakan ne, yayin da yake yiwa wakilin mu na ‘yan Zazu,  Ibrahim Abdullahi Soron Dinki, Karin bayani dangane da abinda hudubar da ya gabatar ta kunsa.

Akwai cikakken bayanin hudubar a muryar da ke kasa.

 

Continue Reading

Labarai

Rahoto: Rubutu na da muhimmanci a mu’amalar bashi – Limamin Bompai

Published

on

Limamin masallacin juma’a na Shelkwatar rundunar ‘yan sandan jihar Kano da ke unguwar Bompai, SP Abdulkadir Haruna, ya ce, akwai bukatar mu rinka gudanar da mu’amalar bashi yadda addinin musulunci.

SP Abdulkadir Haruna, yana bayyana hakan, a zantawarsa da wakilin mu na ‘yan Zazu, Abba Isah Muhammad, bayar idar da Sallar Juma’a.

Domin jin cikakken rahoton saurari wannan.

Continue Reading

Labarai

Rahoto: Matashi ya yi yunkurin cinye tabar Wiwin da aka kama shi da ita a hanyar kotu

Published

on

Ana zargin wani matashi ya yi yunkurin hadiye tabar Wiwi da miyagun kwayoyi da aka kama shi da ita a hanyar kotu.

Tunda fari jami’an tsaron, sun kama matasahin da zargin samun sa da kayan maye, inda yake boye da wasu basu sani ba, kafin kuma a kai shi kotu, ya ciro su yana yunkurin hadiye wa.

Wakilin mu na ‘yan Zazu, Ibrahim Abdullahi Soron Dinki yana da cikakken rahoton.

Continue Reading

Trending