Connect with us

Ilimi

Wata 6 babu albashi: Za mu jure wa duk wata yunwa – ASUU

Published

on

Kungiyar Malaman Jami’o’i (ASUU), ta ce, babu daya daga cikin malaman jami’o’inta da a ka biya shi albashi, tun bayan da kungiyar ta fara yajin aiki a watan Fabrairu.

Da yake magana a wata hira da gidan talabijin na Channels Television’s Sunrise Daily, shugaban ASUU, Farfesa Emmanuel Osodeke, ya zargi Gwamnatin Tarayya da amfani da yunwa a matsayin makami wajen tilasta wa malaman da ke yajin aikin komawa ajujuwa.

Osodeke ya bayyana cewa, an kwashe watanni 6 kenan ba a biyansu albashi, ya ce, “Gwamnati mai ci ba za ta iya amfani da karfin yunwa, wajen ja da ‘yan kungiyar da ke yajin aiki ba.

A cewarsa, gwamnatin tarayya na tunanin hana malaman jami’o’in albashi zai sa malaman jami’o’in durkushewa tare da kawo karshen yajin aikin.

“An gudanar da albashin mu, wannan shi ne wata na shida da ake ƙin biyan albashi. Sun dauka idan sun rike albashin mu wata biyu ko uku za mu zo bara mu ce ku yi haƙuri ku bar mu mu koma bakin aiki.

“Amma mu a matsayinmu na ƙungiyar masu hankali, mun girma fiye da haka. Ba za ku iya amfani da karfin yunwa, domin ja da membobinmu ba, wanda shine ainihin abin da gwamnati ke yi, “in ji shi.

A ranar 14 ga watan Fabrairu ne kungiyar ASUU ta shiga yajin aiki, domin matsawa bukatunta na samar da ingantaccen tsarin walwala da inganta fannin ilimi da sauran su, lamarin da ya tilastawa daliban Najeriya zama a gida.

Ilimi

An wanke Ɗakin Allah bayan kammala aikin Hajji

Published

on

Hukumomi a Saudiyya sun yi bikin wanke Ka’abah, bayan kammala aikin Hajjin bana.

Yarima mai jiran gado, Muhammad bin Salman tare da shugaban masallatan Harami, Sheikh Abdul Rahman da kuma Limaman Masallatan Haramin ne suka jagorancin wankin Dakin Allah.

Shafin intanet na Haramain, wanda ya wallafa hotunan wankin Ka’abah, ya ce an gudanar da shi ne a yau Talata. A cewar BBC.

Ana amfani ruwan zam-zam da turaruka masu kamshi, ciki har da miski da kuma tawul mai tsabta wajen wanke dakin Ka’abah.

Akan tanadi dukkan abubuwan da ake bukata kwana guda kafin a wanke dakin.

Haka kuma ana shafe sa’oi biyu wajen wanke dakin.

Wanke dakin Ka’abah ya faru ne tun daga lokacin Annabi Muhammad (SAW).

Continue Reading

Ilimi

Alhajin Kano ɗan karamar hukumar Madobi ya rasu a Makkah

Published

on

Hukumar jin dadin alhazai ta jihar Kano, ta tabbatar da rasuwar wani Alhaji mai suna Sani Idris Muhammed a kasar Saudiyya bayan kammala aikin Hajjin shekarar 2022.

Sakataren zartarwa na hukumar jin dadin alhazai ta jiha, Alhaji Muhammed Abba Danbatta ne ya bayyana hakan ga manema labarai a ranar Asabar.

Ya ce, Idris Muhammed wanda ya fito daga karamar hukumar Madobi, ya rasu ne a ranar Asabar bayan ya yi fama da gajeruwar rashin lafiya a babban asibitin Makkah.

A cewarsa, “An yi jana’izar marigayin kamar yadda addinin Musulunci ya tanada a babban masallacin Juma’a da ke farfajiyar Masallacin Harami na Makkah”.

Abba Danbatta ya yi wa marigayin addu’a tare da miƙa ta’aziyya tare da iyalansa.

Continue Reading

Ilimi

Waɗanda su ke yi mana gurguwar fahimta sun jahilce mu – ASUU

Published

on

Kungiyar Malaman Jami’o’i, ASUU, shiyyar Calabar, ta ce, ‘yan Najeriya da ke zargin kungiyar da daukar nauyin ayyukan masana’antu na yajin aiki, ba su da masaniya kan ainihin bukatunsu ba.

Ko’odinetan shiyyar kuma babban malami a sashen nazarin zamantakewa da al’adu na jami’ar Uyo (UNIUYO), Dr. Aniekan Brown, ya yi magana a wata tattaunawa da aka yi da shi a Uyo, babban birnin jihar Akwa Ibom.

Brown ya jaddada cewa, gwagwarmayar kungiyar ba ta son kai, sabanin yadda ake ta yada jita-jita a wasu bangarori na cewa, suna son samun riba mai yawa kamar na siyasar kasar.

Ya yabawa ‘yan Najeriya da dama, wadanda duk da haka, sun goyi bayan kungiyar tare da tausayawa kungiyar, domin fahimtar cewa, abin da suke yi shi ne a cikin hirar da ake yi na makomar kasar.

“Na yaba da goyon bayan da muka samu tsawon watanni. Shawara ce da aka yi niyya don fara yajin aikin don samun kyakkyawar makoma ga mu duka”.

Amma ra’ayina shi ne duk wanda zai yi fushi da kungiyar, duk wanda ke zargin ASUU a yau ya yi hakan ne bisa jahilci. Domin haka zan yi kira gare su da su sauƙaƙa su fahimta tare da mu.

“Abin da ASUU ke yi gwagwarmaya ce ta rashin son kai. Wadanda suke zargin ASUU, kalubalenmu shi ne mu ilmantar da su, domin da sun san dalilin da ya sa muke yajin aiki, ba za su zargi ASUU ba.

Watanni biyar babu albashi, sadaukarwa ce babba, amma bai isa ya hana mu ba. Don haka zan so in gaya wa mutane cewa, don gobenmu, mun sadaukar da kai a yau”. In ji a cewar Vanguard.

Continue Reading

Trending