Connect with us

Labarai

Ɗalibi ya rataye kansa a kan ya kasa cin jarabawa

Published

on

Wani matashi dan shekara 27 da haihuwa ɗan makarantar Offa Grammar dake karamar hukumar Offa a jihar Kwara, Adegoke Adeyemi, ya kashe kansa sakamakon gaza cin jarrabawar da ya yi na karin aji daga matakin SS1 zuwa SS2.

Adegoke, wanda aka same shi yana rataye a kan bishiya, an bukaci ya maimaita karatun, kamar yadda jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, Okasanmi Ajayi, ya tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwa a Ilorin a daren Laraba.

Ya ce, tawagar ‘yan sanda daga shelkwatar ‘yan sanda na Offa ne suka ɗauke gawar dalibin marigayin daga wata bishiya da ke bayan wani Otal a Offa da misalin karfe 15.34 na ranar Talata.

An kai gawar zuwa babban asibitin Offa, domin gudanar da bincike, yayin da aka fara bincike kan lamarin.

Labarai

Rahoto: Mu nisanci abinda Allah Ya hana domin samun saukin rayuwa – Limamin Tukuntawa

Published

on

Limamin masallacin juma’a na Masjidul Kuba da ke unguwar Tukuntawa a jihar Kano, Malam Ahmad Ali, ya ce, al’umma su duba tsakanin su da Allah tare da nisantar abinda ya hana, domin saukin tsadar rayuwa.

Malam Ahmad Ali, ya bayyana hakan ne, yayin da yake yiwa wakilin mu na ‘yan Zazu,  Ibrahim Abdullahi Soron Dinki, Karin bayani dangane da abinda hudubar da ya gabatar ta kunsa.

Akwai cikakken bayanin hudubar a muryar da ke kasa.

 

Continue Reading

Labarai

Rahoto: Rubutu na da muhimmanci a mu’amalar bashi – Limamin Bompai

Published

on

Limamin masallacin juma’a na Shelkwatar rundunar ‘yan sandan jihar Kano da ke unguwar Bompai, SP Abdulkadir Haruna, ya ce, akwai bukatar mu rinka gudanar da mu’amalar bashi yadda addinin musulunci.

SP Abdulkadir Haruna, yana bayyana hakan, a zantawarsa da wakilin mu na ‘yan Zazu, Abba Isah Muhammad, bayar idar da Sallar Juma’a.

Domin jin cikakken rahoton saurari wannan.

Continue Reading

Labarai

Rahoto: Matashi ya yi yunkurin cinye tabar Wiwin da aka kama shi da ita a hanyar kotu

Published

on

Ana zargin wani matashi ya yi yunkurin hadiye tabar Wiwi da miyagun kwayoyi da aka kama shi da ita a hanyar kotu.

Tunda fari jami’an tsaron, sun kama matasahin da zargin samun sa da kayan maye, inda yake boye da wasu basu sani ba, kafin kuma a kai shi kotu, ya ciro su yana yunkurin hadiye wa.

Wakilin mu na ‘yan Zazu, Ibrahim Abdullahi Soron Dinki yana da cikakken rahoton.

Continue Reading

Trending