Connect with us

Labarai

Rahoto: Ba za ka ce kana san Annabi ba kuma kana abin da ya hana – Limamin Sabon Gari

Published

on

Limamin masallacin Juma’a na Akafaruddeen da ke unguwar Sabon Gari, karamar hukumar Fagge, jihar Kano, Dr Muhammad Ahmad, ya ce, an zo wani zamani da wasu daga cikin al’ummar musulmi, ba sa bin Allah da manzonSa, bayan fadi tashi da ya yi shi da Sahabban sa, domin tabbatar da addinin musulunci.

Dr Muhammad Ahmad, ya bayyana hakan ne, yayin da yake yiwa wakilin mu na ƴan Zazu, ƙarin bayani dangane da darussan da ke cikin huɗubar da ya gabatar.

Audio Player

Daurin Boye

Mun kafa kwamiti domin rage farashin – Gwamnatin tarayya

Published

on

Gwamnatin tarayya ta kafa wani kwamiti da zaiyi Duba kan hanyoyin shigo da abinci domin rage farashin sa da kaso 50.

Kwamitin dai dake karkashin mataimakin shugaban kasa Sanata Kashim Shettima zai yi aiki ne da wasu ministoci, domin ganin an wadatar Nigeria da abinci.

 

Yayin jawabin sa, Sanata Kashim Shettima yace hakan wani bangare NE na kara inganta tattalin arziki da shugaban kasa Asuwaju Bola Tinubu ke kokari.

 

Continue Reading

Labarai

Arsenal ba kanwar lasa ba ce – Me tsaron Gidan Real Madrid

Published

on

Me tsaron Gidan kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid Thibaut Courtois yace sun yi rashin nasara ne a wasan da suka buga a jiya da kungiyar kwallon kafa ta Arsenal, saboda Arsenal din ba kanwar lasa ba ce.

A jiya Laraba ne dai aka fafata wasan kusa da na kusa da na karshe, tsakanin kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid da kuma Arsenal Inda Arsenal ta lallasa Real Madrid da ci 2 da 1.

Continue Reading

Hangen Dala

Bamu da labarin kwankwaso zai koma APC – NNPP

Published

on

Jamiyyar NNPP a Kano tace ba ta da masaniyar labarin da ake yadawa na cewa Sanata Rabiu Musa Kwankwaso na Shirin komawa jamiyyar APC.

Shugaban jamiyyar na Kano Honorable Hashimu Suleman Dungurawa ne ya bayyana hakan ta cikin Shirin siyasa hangen dala, na tashar Dala Fm.

Yace abin da ake yadawa zance ne mara tushe balle makama, a don haka al’umma suyi watsi da wannan labari.

 

Koda dai yace su na maraba da duk wani Mataki da Sanata Kwankwason ya dauka suna tare dashi.

 

Continue Reading

Trending