Ƙasashen Ƙetare
Magen gidan Firaministar Birtaniya na dakon uwar dakin ta

A yau ne iyalan tsohon firaministan Burtaniya Boris Johnson ke tattara komatsansu a shirye-shiryen da suke yi na bankwana da gidan firaministan wanda ke Downing Street, domin bayar da waje ga sabuwar firaministar Mrs Liz Truss tare da iyalanta, wacce za ta ci gaba da zama a gidan na tsawon mulkinta,
To sai dai yayin da ake wannan shiri na ficewa daga gidan Kyanwar gidan mai suna ‘Lary’ na nan daram a gidan tana jiran isowar sabuwar firaministar
A rahoton BBC sun ce, Lary wacce ba mallakin kowa ba ce, ta zama babbar Kyanwar gidan firaminstan Birtaniya.
Kyanwar mai shekara 15, wacce ta yi zamani da firaministocin Burtaniya har guda uku, na shirin zama da iyalan Mrs Truss.

Ƙasashen Ƙetare
Shek Shuraim yayi ritaya daga limancin Masallacin harami

Guda cikin manyan limaman masallaci Mai alfarma na Makkah Shek Shuraim ya rubuta takardar ajiye limancin masallacin.
Shafin Haramain Sharifain ya ruwaito cewa, cikin takarar ajiye limancin da Shek Shuraim ya rubuta, ya bayar da uzurin mayar da hankali kan wasu ayyuka da suka kulla yarjejeniya da shugabancin Kasar tun a shekarar bara ta 2022.
Sai dai takardar ta bayyana cewa, Shek Shuraim zai rinka zuwa masallacin domin jagorantar wasu salloli, musamman Tarawih a watan Ramadhana.
Shek Shuraim dai ya dauki tsawon shekaru Yana Jan sallah a masallacin harami, Kuma guda ne cikin gwanayen alqur’ani, inda wasu lokutan suke karanta shi da Shek Abdurrahman Assudais.

Ƙasashen Ƙetare
Yadda birnin Makkah ya koma bayan saukar ruwan sama

. Yawan korayen ciyayi a birnin Makkah alama ce ta tashin alqiyama.
. Saukar ruwan sama ya sanya korayen ciyayi sun fito a birnin Makkah.
Shafin Haramain Sharifain ya wallafa cewa yanzu haka korayen ciyayi sun mamaye birnin Makkah sakamakon mamakon ruwan sama da aka yi.
Sai dai Malamai irin su Dakta Zakir Naik sunyi fashin baki, Ina suka ce hakan wata alama ce da take nuna kusantowar tashin alqiyama, dogaro da hadisin Annabi S.A.W,
“Alqiyama ba za ta tsaya ba har sai yankin larabawa ya koma kiwo da koramu, wanda hakan zai faru ne ta sanadin korayen ciyayi”. Muslim 157

Ƙasashen Ƙetare
‘Yan Sanda sun ce Beraye ne suka shanye hodar Ibilis a ofishin su

‘Yan sandan kasar Indiya, sun ce ɓeraye sun lalata kusan kilogram 200 na hodar Ibilis da aka ƙwace a hannun wasu mutane da ke safararta aka kuma ajiye a ofishinsu.
“Ɓeraye kananan halittu ne da ba su san wani tsoron ‘yan sanda ba. Abu ne mai wahala iya kare su,” a cewar Kotu da ke zamanta a jihar Uttar Pradesh.
Kotun ta bukaci ‘yan sanda su gabatar da shaida da ke tabbatar da cewa ɓeraye ne suka lalata hodar.
Alkalin ya bada misali da kararraki uku da aka gabatar kan ɓeraye sun lalata kwayar.
Mai shari’a Sanjay Chaudhary ya ce ko a baya an samu rahotanni da ke cewa ɓerayen sun lalata kilo 195 na hodar iblis, da kuma kilo 700 duk a ofisoshin ‘yan sanda.
Sanjay ya faɗawa ‘yan sanda cewa ba su da kwarewar yaƙi da irin waɗannan ɓeraye. Ya ce hanya ɗaya tilo na kare aukuwar irin wannan shi ne kai hodar ko kwayar dakunan adana magunguna ko aiwatar da gwaji. In ji BBC.

-
Nishadi3 years ago
Ina neman mijin aure – Rayya
-
Manyan Labarai3 years ago
KAROTA: An baiwa Baffa Babba wa’adin kwanaki bakwai
-
Labarai3 years ago
Auren dan Panshekara da ba Amurkiya ya samu cikas
-
Nishadi3 years ago
Mansura Isah ta yi kaca-kaca da Sadiya Haruna
-
Labarai2 years ago
Hamisu Breaker ya kai kan sa wajen ‘yan sanda
-
Lafiya10 months ago
Rahoto: An gano wani gida da ake gini da takardun Kur’ani da Alluna
-
Nishadi3 years ago
An gano daliban da Adam Zango ya dauki nauyin karatun su
-
Manyan Labarai3 years ago
Sabuwar damfarar da ta fito a Kano