Connect with us

Labarai

Jiagawa: An tsamo gawar mutum biyu da suka mutu a ruwa

Published

on

Hukumar tsaro ta Civil Defence, NSCDC, ta gano gawarwakin wasu mutane biyu da ruwa ya nutse da su a jihar Jigawa.

Mai magana da yawun hukumar na jihar Jigawa, CSC Adamu Shehu ya tabbatar wa da manema labarai hakan cewa, gawarwakin biyun sun mutu ne sakamakon wasu abubuwa guda biyu da suka faru a kananan hukumomin Buji da Kaugama.

Ya ce, an kwato su daban daga wurare biyu daban-daban.

A cewarsa, “An tsinci gawar Zahraddeen Yusuf dan shekara 30 a kauyen Lafia dake unguwar Madabe a karamar hukumar Buji a ranar Litinin din da ta gabata a wani tafki mai suna Ruwan Kidibo bayan ya yi kokarin tsallaka ruwa tare da ‘yan uwansa domin isa gonarsa a ranar Asabar.

“Haka nan a karamar hukumar Kaugama, NSCDC ta samu rahoton nutsewar wani yaro dan shekara 15, Anas Hamza a Garin Badde, Marke, karamar hukumar Kaugama.

“Marigayin ya na dawowa gida daga gona sai ya yanke shawarar yin wanka daga wani tafki da ke kusa da shi, kuma abin takaici, ruwa ya nutse da shi daga baya kuma sai kayan sa aka gani a gefen tafkin.”

CSC Adamu ya ce, an kaddamar da aikin ceto tare da taimakon mutanen yankin wanda a karshe aka gano gawarwakin mutanen biyu.

Ya ce, an mika gawarwakin ga iyalansu, wanda tuni suka yi jana’izar su.

Labarai

Ba mu san Hamisu Breaker ya saki waƙar Amanata ba – Hukumar tace fina-finai

Published

on

Hukumar tace Fina-finai da Ɗab’i ta jihar Kano ta ce yanzu haka tana kan bincike don gano yadda akai mawakin nan Hamisu Breaker, ya saki sabuwar wakarsa mai suna “Amanata” ba tare da an tantance ta ba.

Mai magana da yawun hukumar Abdullahi Sani Sulaiman, shi ne ya bayyana hakan a wani sakon murya da ya aikowa Dala FM Kano, a ranar Alhamis 24 ga watan Afrilun 2025.

Ya kuma ce aikin dakatar da wakar ba na hukumar Hisbah ba ne na hukumar tace fina-finai ne, amma ba laifi ba ne kasancewar duk hukumomi ne na Gwamnati, a don haka idan hukumar ta Hisbah ta magantu akai babu laifi, domin dama suna aiki kafaɗa da kafaɗa.

A game da wakar ta Hamisu Beraker, mai suna “Amanata”, Abdullahi Sani, ya ce su har yanzu ba su san ta ina wakar ta fita ba tare da an tantance ta ba, amma tuni shugaban hukumar Abba Al-mustapha ya bada umarnin gudanar da bincike akan ta.

Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ce dai ta hannun mataimakiyar babban kwamandan ta a ɓangaren mata Dakta Khadijah Sagir Sulaiman, ta yi Allah wa-dai da wakar Hausar mai taken “Amana ta” da mawaki Hamisu Breaker ya rera, inda ta shawarci matasa da su guji sauraren wakar, bisa yadda take ɗauke da abubuwan da ke ƙarfafa aikata alfasha, da kuma amfani da kalmomin batsa a cikin bidiyon ta.

Continue Reading

Hangen Dala

Rashin wuta: Muna cikin mawuyacin hali – al’ummar Kano, Katsina da Jigawa

Published

on

Al’ummar jihohin Kano, katsina da Jigawa na fuskantar yanayi mara dadi, Sakamakon karancin samun wutar lantarki daga hukumar KEDCO.

Al’ummar jihohin sun ce iya sa’o’i uku kacal suke samun wutar, wanda hakan ke haifar musu da nakasu a harkokin kasuwancin su.

Wani bincike da jaridar Daily Trust tayi ta ambato yadda masu kananan masana’antu irin su Walda, Cajin Waya, Kankara da masu sana’ar dinki da dai sauran kananan sana’o’i dake amfani da wutar lantarki sun shiga mawuyacin hali.

Kazalika rashin wutar ya shafi hatta bangaren ruwan sha, dama masu sana’ar sayar da Ruwa a irin yankunan Hotoro da sauran irin wuraren dake sayen ruwa, Inda yanzu haka ruwan yayi tashin gwauron zabi a kowace jarka.

Koda dai ana ta bangaren hukumar rarraba hasken wutar lantarkin me kula da shiyyar Kano, Katsina da Jigawa KEDCO sun nemi afuwar al’umma.

Idan za’a tuna dai a makon jiya ne Ministan Wutar lantarki yace ‘yan Nigeria Miliyan 150 na samun wadatacciyar wutar lantarki.

Sai dai kuma a jihohi irin su Kano, Katsina da Jigawa na bayyana damuwa kan karancin Wutar, Inda suka ce bata wuce ta sa’o’i uku suke samu a kowa ce rana.

Continue Reading

Hangen Dala

Rashin wuta:- Muna cikin mawuyacin hali – al’ummar Kano, Katsina da Jigawa

Trending