Connect with us

Lafiya

PCN ta lalata magunguna na Naira miliyan 100 bayan wa’adin su ya kare

Published

on

Hukumar Kula da Magunguna ta Kasa (PCN), ta lalata magungunan da suka wuce na sama da Naira miliyan 100 a jihar Adamawa.

Hukumar ta bayyana hakan ne a ranar Litinin cewa, an tattara magungunan da wa’adin su ya kare daga shagunan sayar da magunguna daban-daban a fadin jihar.

Wakilin kakakin majalisar dokokin jihar, Iya Aminu Abbas ne ya jagoranci lalata magungunan da aka yi a wajen garin Yola mai suna Conerwire, daura da hanyar Yola-Numan.

Mataimakin shugaban majalisar, Pwamakino Mankendo, wanda ya tsaya a madadin Abbas, ya yabawa kungiyar masu harhada magunguna ta kasa reshen jihar Adamawa kan yadda suka hana sayar da magungunan da wa’adin su ya kare zuwa cikin kasuwa.

Shima da yake jawabi yayin atisayen lalata magungunan, kwamandan hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA a jihar Adamawa, Femi Agbolu, ya ce, abin farin ciki ne a gano magungunan tare da lalata su.

Tun da farko, Shugaban Hukumar PCN na jihar, Ibrahim Talba ya ce, an kama magungunan ne daga sassan jihar a wani bangare na kokarin kawar da magungunan da wa’adin su ya kare da na jabu.

Lafiya

Rahoto: Kada matashi ya bari a ba shi kudi ya sha kayan maye a lokacin zabe – Kwamared Mai Salati

Published

on

Wani matashi dan gwagwarmaya a jihar Kano, Kwamared Adamu Mai Salati Hausawa, ya ce, kada matashi ya bari a ba shi kudi ya sha kayan maye a lokacin zabe.

Kwamared Mai Salati, ya bayyana hakan ne, a zantawarsa da wakilin mu na ‘yan Zazu, Ibrahim Abdullahi Soron Dinki.

Domin jin cikakken rahoton saurari wannan.

Continue Reading

Lafiya

Naira tiriliyan 2.565 tallafin man fetur ya lakume saboda haka zamu janye – Gwamnati

Published

on

Ministar kuɗi, kasafi da tsare-tsare, Hajiya Zainab Ahmed, ta ce, gwamnatin tarayya za ta daina biyan kuɗin tallafin man fetur a watan Yunin 2023.

Hajiya Zainab ta bayyana haka ne a lokacin taron manema labarai da ta gudanar a Abuja bayan kammala taron tattalin arziki na ƙasa karo na 28.

Kamfanin dillacin labarai na NAN ya ruwaito cewa, biyan tallafin kudin man fetur ya laƙume Naira tiriliyan 2.565 tsakanin watan Janairu zuwa Agustan 2022.

Haka kuma a cikin kasafin kudinta, gwamnatin tarayya ta ƙiyasta kashe naira tiriliyan 3.3 wajen biyan tallafin man tsakanin watan Janairu zuwa Yunin 2023.

Ta ci gaba da cewa kuɗin tallafin man na kawo wa kasafin kudin giɓin da dole sai an ciwo bashi kafin cike shi.

“Ba kuɗi ne da muke da su a hannu ba, kudi ne da muke karɓo bashinsu domin biyan tallafin”, A cewar Zainab.

Continue Reading

Lafiya

Rahoto: Aikin Hisba ba iya kalallahu kala rasulu ba ne kawai sai da horon kare kai – Ibn Sina

Published

on

Hukumar Hisba ta jihar Kano ta ce, aikin Hisba ba iya kalallahu kala rasulu ba ne kawai sai da horon kare kai

Babban kwamandan hukumar Hisbar, Sheikh Muhammad Harun Ibni Sina ne, ya bayyana hakan, a zantawarsa da wakilin mu na ‘yan Zazu, Ibrahim Abdullahi Soron Dinki.

Akwai cikakken rahoton a muryar da ke kasa.

Continue Reading

Trending