Connect with us

Wasanni

Kowane dan wasa na Rivers United zan ba shi dala 40,000 idan kun doke Wydad – Wike

Published

on

An yi wa ‘yan wasan Rivers United alkawarin dala 40,000 kowannensu idan suka kai matakin rukuni a gasar cin kofin zakarun nahiyar Afirka ta CAF.

Tawagar Stanley Eguma za ta kara da Wydad Casablanca ta Morocco a wasan farko na zagayen farko a Fatakwal ranar Lahadi.

Za a fafatawa a Casablanca a karshen mako mai zuwa.

Wadanda suka yi nasara sama da wasa biyu za su tsallake zuwa matakin rukuni na gasar.

Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike ya bai wa kowane dan wasa dala 20,000 da ya lashe gasar cin kofin kwararru ta kasa NPFL a karon farko a tarihin su a watan Yuni, kuma yanzu ya yi alkawarin ba da sabon dala 40,000.

Kungiyar tan Fatakwal na neman zama kungiya na biyu a Najeriya da ya lashe gasar cin kofin CAF bayan Enyimba ta ci a 2003 da 2004.

Plateau United ita ce sauran kungiyoyin Najeriya da za su fafata a gasar bana.

Labarai

Arsenal ba kanwar lasa ba ce – Me tsaron Gidan Real Madrid

Published

on

Me tsaron Gidan kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid Thibaut Courtois yace sun yi rashin nasara ne a wasan da suka buga a jiya da kungiyar kwallon kafa ta Arsenal, saboda Arsenal din ba kanwar lasa ba ce.

A jiya Laraba ne dai aka fafata wasan kusa da na kusa da na karshe, tsakanin kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid da kuma Arsenal Inda Arsenal ta lallasa Real Madrid da ci 2 da 1.

Continue Reading

Wasanni

Bayer Leverkusen ta zama zakarar gasar Bundesliga ta 2023/2024.

Published

on

Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Bayer Leverkusen ta zama zakarar gasar Bundesliga ta shekarar 2023/2024, bayan da suka samu nasara a kan Weder Bremen da ci 5-0.

Hakan ne kuma ya kawo ƙarshen shekaru 11 da Bayern Munich, da ta yi tana lashe gasar.

Wannan dai shi ne karo na farko da Bayer Leverkusen suka taɓa lashe gasar a tarihi, ida suka gaza ɗaukar kofin a shekarar 2002 a ranar ƙarshe ta gasar.

Har ila yau, a dai wannan shekarar ne su kayi rashin nasara hannun Shalke 04, a wasan ƙarshe na German Cup Da ci 4-2.

Haka kuma, Real Madrid suka doke su a wasan ƙarshe na zakarun nahiyar turai.

Rahotanni sun bayyana cewa ƙungiyar bata taɓa ɗaukar wata gasa ba a ƙarni na 21, sai bayan da Xavi Alonso ya karɓe su.

Continue Reading

Wasanni

Hukumar NPFL, ta amince da buƙatar Kano Pillars na ɗage wasan ta na mako na 28 da Enyimba

Published

on

Yanzu haka an samu dai-daito da hukumar NPFL, wanda ta amince da bukatar Kano Pillars na dage wasanta na mako na 28, da Enyimba zuwa ranar Alhamis, mai zuwa.

Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Kano Pillars, ce ta wallafa hakan a shafin ta na Facebook da yammacin Litinin ɗin nan, ta ce ƴan wasan ta za su tashi a gobe Talata, da safe zuwa Aba domin fafata wasannin su.

Idan dai ba’a manta ba ƙungiyar ta wallafa kaɗan daga irin ƙalubalen da take fuskanta a harkokin gudanarwar ta.

Pillars, ta wallafa ƙalubalen ne kamar haka, “A yanzu haka zancan da muke muku Kano Pillars ta rasa kudin da za taje garin Aba, domin buga wasan hamayya na Nigeria Premier league wato Zobia Classic”.

Wasan dai shine wasa mafi ɗaukar hankali a league din Nigeria baki ɗaya, ku taya mu yadawa dan Allah.

Continue Reading

Trending