Connect with us

Wasanni

Na so na jawo dan wasan Bayern Munich ya buga wa Najeriya wasa abun ya ci tura – Rohr

Published

on

Tsohon mai horas da Super Eagles, Gernot Rohr, ya bayyana cewa, ya yi kokarin shawo kan matashin dan wasan Bayern Munich, Jamal Musiala, da ya bugawa Najeriya wasa, amma abun ya ti tura.

An haifi Musiala a kasar Jamus ga mahaifin dan Najeriya kuma mahaifiyarsa ‘yar Birtaniya.

Dan wasan ya zabi ya wakilci Jamus a matakin manya, bayan ya fara bugawa Ingila wasa a matakin shekaru na kanana.

Rohr, wanda ya jagoranci Super Eagles tsakanin 2016 zuwa 2021 ya bayyana cewa, ya yi kokarin shawo kan dan wasan mai shekaru 19 ya wakilci zakarun Afirka sau uku.

Rohr ya shaida wa Owngoal cewa “Ina fata da na samu Musiala ya buga wa Najeriya wasa, amma ya zabi ya buga wa Jamus wasa.”

“Dan wasa ne mai ban sha’awa, na sadu da shi lokacin yana shekara 17, kuma na yi magana da wakilansa da iyayensa.

“A wannan lokacin, ya kasa yanke shawara, kuma bayan shekara guda, ya zama abin da yake yanzu, kuma shi ke nan.”

Hukumar kwallon kafa ta kasa ta kori Rohr a watan Disambar 2021.

Labarai

Arsenal ba kanwar lasa ba ce – Me tsaron Gidan Real Madrid

Published

on

Me tsaron Gidan kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid Thibaut Courtois yace sun yi rashin nasara ne a wasan da suka buga a jiya da kungiyar kwallon kafa ta Arsenal, saboda Arsenal din ba kanwar lasa ba ce.

A jiya Laraba ne dai aka fafata wasan kusa da na kusa da na karshe, tsakanin kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid da kuma Arsenal Inda Arsenal ta lallasa Real Madrid da ci 2 da 1.

Continue Reading

Wasanni

Bayer Leverkusen ta zama zakarar gasar Bundesliga ta 2023/2024.

Published

on

Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Bayer Leverkusen ta zama zakarar gasar Bundesliga ta shekarar 2023/2024, bayan da suka samu nasara a kan Weder Bremen da ci 5-0.

Hakan ne kuma ya kawo ƙarshen shekaru 11 da Bayern Munich, da ta yi tana lashe gasar.

Wannan dai shi ne karo na farko da Bayer Leverkusen suka taɓa lashe gasar a tarihi, ida suka gaza ɗaukar kofin a shekarar 2002 a ranar ƙarshe ta gasar.

Har ila yau, a dai wannan shekarar ne su kayi rashin nasara hannun Shalke 04, a wasan ƙarshe na German Cup Da ci 4-2.

Haka kuma, Real Madrid suka doke su a wasan ƙarshe na zakarun nahiyar turai.

Rahotanni sun bayyana cewa ƙungiyar bata taɓa ɗaukar wata gasa ba a ƙarni na 21, sai bayan da Xavi Alonso ya karɓe su.

Continue Reading

Wasanni

Hukumar NPFL, ta amince da buƙatar Kano Pillars na ɗage wasan ta na mako na 28 da Enyimba

Published

on

Yanzu haka an samu dai-daito da hukumar NPFL, wanda ta amince da bukatar Kano Pillars na dage wasanta na mako na 28, da Enyimba zuwa ranar Alhamis, mai zuwa.

Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Kano Pillars, ce ta wallafa hakan a shafin ta na Facebook da yammacin Litinin ɗin nan, ta ce ƴan wasan ta za su tashi a gobe Talata, da safe zuwa Aba domin fafata wasannin su.

Idan dai ba’a manta ba ƙungiyar ta wallafa kaɗan daga irin ƙalubalen da take fuskanta a harkokin gudanarwar ta.

Pillars, ta wallafa ƙalubalen ne kamar haka, “A yanzu haka zancan da muke muku Kano Pillars ta rasa kudin da za taje garin Aba, domin buga wasan hamayya na Nigeria Premier league wato Zobia Classic”.

Wasan dai shine wasa mafi ɗaukar hankali a league din Nigeria baki ɗaya, ku taya mu yadawa dan Allah.

Continue Reading

Trending