Connect with us

Wasanni

Flamingos za ta doke Jamus a gasar kofin duniya ta mata – Bankole

Published

on

Babban mai horas da tawagar kungiyar kwallon kafa ta mata Flamingos, Bankole Olowookere, ya ce, tawagarsa za ta tashi tsaye domin samun nasara a kan Jamus a wasansu na farko a gasar cin kofin duniya na mata ta ‘yan kasa da shekaru 17 na 2022 da za a fara a kasar Indiya yau Talata.

‘Yan matan  za su bukaci yin iya bakin kokarinsu da Jamusawa, wadanda ke daya daga cikin wadanda suka fi so a gasar.

Za a fafata wasan na yau a filin wasa na Pandit Jawaharlal, Goa.

Mai horas war ya bayyana cewa tawagarsa a shirye take don aikin da ke gaba kuma baya tsoron fuskantar Jamusawa.

“Muna farin cikin fara gasar ta hanyar buga wasa da daya daga cikin kungiyoyin mata masu karfi a duniya. Kalubale ne mai kyau domin idan za ku ci kofuna, dole ne ku doke mafi kyawun kungiyoyi,” Olowookere ya shaida wa thenff.com.

“Mayar da hankalinmu shine samun maki uku a kan Jamusawa, wanda zai kara mana kwarin gwiwa game da sauran wasannin rukunin rukuni da kuma ci gaba a gasar.”

Chile da New Zealand su ne sauran kungiyoyi a rukunin da Najeriya za ta fafata da su a gasar.

Labarai

Arsenal ba kanwar lasa ba ce – Me tsaron Gidan Real Madrid

Published

on

Me tsaron Gidan kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid Thibaut Courtois yace sun yi rashin nasara ne a wasan da suka buga a jiya da kungiyar kwallon kafa ta Arsenal, saboda Arsenal din ba kanwar lasa ba ce.

A jiya Laraba ne dai aka fafata wasan kusa da na kusa da na karshe, tsakanin kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid da kuma Arsenal Inda Arsenal ta lallasa Real Madrid da ci 2 da 1.

Continue Reading

Wasanni

Bayer Leverkusen ta zama zakarar gasar Bundesliga ta 2023/2024.

Published

on

Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Bayer Leverkusen ta zama zakarar gasar Bundesliga ta shekarar 2023/2024, bayan da suka samu nasara a kan Weder Bremen da ci 5-0.

Hakan ne kuma ya kawo ƙarshen shekaru 11 da Bayern Munich, da ta yi tana lashe gasar.

Wannan dai shi ne karo na farko da Bayer Leverkusen suka taɓa lashe gasar a tarihi, ida suka gaza ɗaukar kofin a shekarar 2002 a ranar ƙarshe ta gasar.

Har ila yau, a dai wannan shekarar ne su kayi rashin nasara hannun Shalke 04, a wasan ƙarshe na German Cup Da ci 4-2.

Haka kuma, Real Madrid suka doke su a wasan ƙarshe na zakarun nahiyar turai.

Rahotanni sun bayyana cewa ƙungiyar bata taɓa ɗaukar wata gasa ba a ƙarni na 21, sai bayan da Xavi Alonso ya karɓe su.

Continue Reading

Wasanni

Hukumar NPFL, ta amince da buƙatar Kano Pillars na ɗage wasan ta na mako na 28 da Enyimba

Published

on

Yanzu haka an samu dai-daito da hukumar NPFL, wanda ta amince da bukatar Kano Pillars na dage wasanta na mako na 28, da Enyimba zuwa ranar Alhamis, mai zuwa.

Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Kano Pillars, ce ta wallafa hakan a shafin ta na Facebook da yammacin Litinin ɗin nan, ta ce ƴan wasan ta za su tashi a gobe Talata, da safe zuwa Aba domin fafata wasannin su.

Idan dai ba’a manta ba ƙungiyar ta wallafa kaɗan daga irin ƙalubalen da take fuskanta a harkokin gudanarwar ta.

Pillars, ta wallafa ƙalubalen ne kamar haka, “A yanzu haka zancan da muke muku Kano Pillars ta rasa kudin da za taje garin Aba, domin buga wasan hamayya na Nigeria Premier league wato Zobia Classic”.

Wasan dai shine wasa mafi ɗaukar hankali a league din Nigeria baki ɗaya, ku taya mu yadawa dan Allah.

Continue Reading

Trending