Wasanni
Jamus ta doke Najeriya a gasar cin kofin mata ta duniya

Tawagar kungiyar kwallon kafa ta mata ta kasa, Flamingos ta ji jiki da ci 2-1 a hannun Jamus a wasansu na farko a gasar cin kofin duniya ta mata na ‘yan kasa da shekaru 17 a filin wasa na Pandit Jawaharlal, Goa a kasar Indiya ranar Talata.
Duk da rinjayen da Jamusawa suka yi, kungiyar Flamingos ce ta kusa zura kwallon farko a wasan.
Kwallon da Opeyemi Ajakaye ta zura kwallo a bugun daga kai sai mai tsaron gida a minti na 17 ya bugi katako.
‘Yan matan Bankole Olowookere za su kara da New Zealand a wasansu na gaba ranar Juma’a.

Labarai
Arsenal ba kanwar lasa ba ce – Me tsaron Gidan Real Madrid

Me tsaron Gidan kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid Thibaut Courtois yace sun yi rashin nasara ne a wasan da suka buga a jiya da kungiyar kwallon kafa ta Arsenal, saboda Arsenal din ba kanwar lasa ba ce.
A jiya Laraba ne dai aka fafata wasan kusa da na kusa da na karshe, tsakanin kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid da kuma Arsenal Inda Arsenal ta lallasa Real Madrid da ci 2 da 1.

Wasanni
Bayer Leverkusen ta zama zakarar gasar Bundesliga ta 2023/2024.

Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Bayer Leverkusen ta zama zakarar gasar Bundesliga ta shekarar 2023/2024, bayan da suka samu nasara a kan Weder Bremen da ci 5-0.
Hakan ne kuma ya kawo ƙarshen shekaru 11 da Bayern Munich, da ta yi tana lashe gasar.
Wannan dai shi ne karo na farko da Bayer Leverkusen suka taɓa lashe gasar a tarihi, ida suka gaza ɗaukar kofin a shekarar 2002 a ranar ƙarshe ta gasar.
Har ila yau, a dai wannan shekarar ne su kayi rashin nasara hannun Shalke 04, a wasan ƙarshe na German Cup Da ci 4-2.
Haka kuma, Real Madrid suka doke su a wasan ƙarshe na zakarun nahiyar turai.
Rahotanni sun bayyana cewa ƙungiyar bata taɓa ɗaukar wata gasa ba a ƙarni na 21, sai bayan da Xavi Alonso ya karɓe su.

Wasanni
Hukumar NPFL, ta amince da buƙatar Kano Pillars na ɗage wasan ta na mako na 28 da Enyimba

Yanzu haka an samu dai-daito da hukumar NPFL, wanda ta amince da bukatar Kano Pillars na dage wasanta na mako na 28, da Enyimba zuwa ranar Alhamis, mai zuwa.
Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Kano Pillars, ce ta wallafa hakan a shafin ta na Facebook da yammacin Litinin ɗin nan, ta ce ƴan wasan ta za su tashi a gobe Talata, da safe zuwa Aba domin fafata wasannin su.
Idan dai ba’a manta ba ƙungiyar ta wallafa kaɗan daga irin ƙalubalen da take fuskanta a harkokin gudanarwar ta.
Pillars, ta wallafa ƙalubalen ne kamar haka, “A yanzu haka zancan da muke muku Kano Pillars ta rasa kudin da za taje garin Aba, domin buga wasan hamayya na Nigeria Premier league wato Zobia Classic”.
Wasan dai shine wasa mafi ɗaukar hankali a league din Nigeria baki ɗaya, ku taya mu yadawa dan Allah.

-
Nishadi5 years ago
Ina neman mijin aure – Rayya
-
Labarai5 years ago
Hamisu Breaker ya kai kan sa wajen ‘yan sanda
-
Nishadi6 years ago
Mansura Isah ta yi kaca-kaca da Sadiya Haruna
-
Manyan Labarai5 years ago
KAROTA: An baiwa Baffa Babba wa’adin kwanaki bakwai
-
Labarai5 years ago
Auren dan Panshekara da ba Amurkiya ya samu cikas
-
Lafiya3 years ago
Rahoto: An gano wani gida da ake gini da takardun Kur’ani da Alluna
-
Manyan Labarai5 years ago
Sabuwar damfarar da ta fito a Kano
-
Nishadi6 years ago
An gano daliban da Adam Zango ya dauki nauyin karatun su