Connect with us

Manyan Labarai

Ba maganar janye takara ta ga wani – Kwankwaso

Published

on

Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar New Nigerian Peoples Party (NNPP), Rabi’u Musa Kwankwaso, ya kawo karshen rade-radin da ake yi na cewa zai janye takarar sa ya bar wa wata jam’iyya.

Da yake magana ta bakin mai magana da yawunsa, Ladipo Johnson, Kwankwaso ya ce, babu maganar janyewa a yakin neman zabensa ga wani.

Ladipo ya yi wannan tsokaci ne a gidan talabijin na Channels ta cikin shirn Sunrise Daily a ranar Laraba, a yayin da ake ta rade-radin cewa jam’iyyar NNPP za ta janye yakin neman zabenta ta baiwa wani dan takarar shugaban kasa kafin 2023.

“Babu maganar rugujewar yakin neman zabe, kamfen din Kwankwaso, ko yakin neman zaben NNPP a kowane mataki a halin yanzu tare da wani jam’iyya ko daya daga cikin ‘yan takara.

“Abin da nake nufi cewa za mu ci gaba da tafiya har zuwa 25 ga watan Fabrairu na shekara mai zuwa,” in ji shi.

Manyan Labarai

Da na hadu da kwankwaso da sai na mare shi – Ganduje

Published

on

Tsohon Gwamnan Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje yace da sun hadu da kwankwaso da akwai yiyuwar ya mare shi, a fadar shugaban kasa.

Tsohon Gwamnan ya bayyana Hakan ne yayin wata ganawa da gidan television na channels, yayin da yake martani Kan ganawar shugaban kasa Asuwaju Bola Ahmad Tinubu da Kuma jagoran jam’iyyar NNPP Sanata Rabiu Musa Kwankwaso a yammacin wannan juma’a.

” Nasan yana gidan Amma bamu hadu ba, da mun hadu akwai yiyuwar na kwada masa Mari” inji Ganduje.

Idan za’a iya tunawa dai kwanakin baya shugaban kasa Asuwaju Bola Ahmad Tinubu yayi wata ganawa da kwankwaso, lamarin da aka jiyo tsohon Gwamnan na korafi cewa ba’a Yi musu adalchi ba, Koda dai a wancan lokaci, Ganduje ya musanta, ta bakin tsohon kwamishinan yada labarai Muhammad Garba, inda yace ba muryar Ganduje bace.

Wannan dai na zuwa ne a Gabar da gwamnatin Kano ke cigaba da rushe wuraren da tayi zargin gwamnatin baya ta Abdullahi Umar Ganduje ta cefanar ba bisa ka’ida ba.

Continue Reading

Manyan Labarai

Gargadin Gwamnatin Kano Kan masu kaya a wuraren gwamnati

Published

on

Gwamnatin jihar Kano ta gargadi dukkanin masu kaya a wuraren da tayi zargin gwamnatin baya ta cefanar ba bisa ka’ida ba, dasu kwashe kayan su cikin gaggawa.

Cikin wata sanarwa da sakataren gwamnatin Dakta Abdullahi Baffa Bichi ta fitar ta bayyana cewa, dukkanin masu kaya a shagunan da aka gina a jiki ko cikin makarantu, Maƙabartu, Asibitoci, Masallatai, gefen badala, Filayen ma’aikatu, Filayen wasanni da sauran wuraren shakatawa mallakin gwamnati da cewa suyi gaggawar kwashe dukkanin kayan su dake cikin shagunan da aka gina a waƴannan gurare ba tare da ɓata lokaci ba.

Continue Reading

Manyan Labarai

Abba Gida Gida ya fara rusau

Published

on

Gwamnatin jihar Kano ta fara rushe wasu gine gine da aka yi su a wuraren gwamnati Ba bisa ka’ida ba.

A cikin daren Asabar din nan ne tawagar Kwamitin kar ta kwana mai lura da rushe gine gine ta fara da rushe wani sabon rukunin shaguna mai kunshe da sama da shaguna 90 dake jikin filin sukuwa a jihar Kano.

Mai magana da yawun gwamnan Kano Sunusi Ahmad Bature Dawakin Tofa ya bayyana cewar wannan aiki somin tabi ne domin batun rushe gine ginen da aka yi su akan filayen jama ar Kano lamari ne da babu gudu babu ja da baya kamar yadda gwamna Engr Abba Kabir Yusif ya bayyana a lokacin da yake yakin neman zabe.

Tawagar kwamitin na kar ta kwana zai cigaba da rushe dukkan wasu gine gine da aka yi su ba bisa kaida ba.

Continue Reading

Trending