Manyan Labarai
Karo na farko dan Najeriya ya zama Kansila bakar fata a Canada

Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya yaba da gudunmawar da kungiyar ‘yan Najeriya mazauna ketare ke bayarwa wajen daga martabar kasar a kasashen waje, bayan da aka zabi Ayo Owodunni a matsayin bakar fata na farko da ya zama kansila a mazabar Kitchener da ke birnin London Ontario na kasar Canada.
A wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban kasa, Malam Garba shehu ya fitar, shugaba Buhari ya ce, nasarar da mista Owodunni ya samu a wannan zabe mai cike da tarihi, ya nuna karara yadda mutumin ya ke bullo da tsare-tsare na ci gaba, da goyon bayan ‘yan Najeriya mazauna Canada a matsayinsa na mai bayar da shawara da kuma kokarinsa na hada kan ‘yan kasar a kasar da yake zaune ta Canada.
Shugaba Buhari ya umarci ‘yan Najeriya mazauna ketare da su kasance jakadun gwamnatin kasar na gari a duk inda suka samu kansu a fadin duniya, ya kuma shawarce su da kada su ji shakkun cimma muradunsu’.
Daga karshe shugaban ya taya mista Owodunni tare da matarsa Folake da kuma yaransu biyu murnar nasarar lashe zaben, wanda ya bayyana a matsayin ”mai matukar muhimmanci’. In ji BBC.

Labarai
Mu yawaita karanta Alƙur’ani da aikin alkhairi a watan Ramadan – Malam Ibrahim Bunkure

Limamin masallaacin Juma’a na Salafussalih dake unguwar Ɗorayi ƙarama Malam Ibrahim Abdullahi Bunkure, ya shawarci al’ummar musulmi da su ƙara himma wajen karanta Al-ƙur’ani mai girma, tare da aikata ayyukan alkhairi domin rabauta da rahamar Allah S.W.T a nan duniya dama gobe ƙiyama.
Mallam Ibrahim Bunkure ya bayyana hakan ne lokacin da yake tsokaci kan huɗubar Juma’ar da ya gabatar yau a masallacin.
Ya ce, kamata yayi musulmai su ƙara yin koyi da kyawawan ɗabi’un Annabi Muhammadu Sallallahu alaihi Wasallama, domin zama ababen koyi a rayuwa.
Wakilinmu Hassan Mamuda Ya’u ya rawaito cewar Mallam Ibrahim Abdullahi Bunkure, ya kuma shawarci al’umma da su ƙara kasancewa masu yafiya musamman a lokacin da aka yi mutu abinda bai musu daɗi ba, bisa mahimmancin da hakan yake da shi.

Manyan Labarai
Gawuna ya taya Abba Gida Gida murna

Dan takarar Gwamnan Kano na jam’iyyar APC a zaben 2023 Dakta Nasiru Yusuf Gawuna ya bayyana karbar kaddara tun bayan da ya Fadi zaben 18 ga watan Maris.
Cikin Wani Sakon murya, Dakta Nasiru Gawuna ya godewa magoya baya, tare da yin fatan alkhairi ga sabuwar gwamnati.
” Wannan sabuwar gwamnati Allah ya Bata ikon yiwa al’umma adalchi, mu Kuma Allah ya bamu ikon yin biyayya.”
Manyan Labarai
Abba Gida Gida ya karbi shaidar lashe zabe

Sabon zaɓaɓɓen gwamnan jihar Kano Injiniya Abba Kabiru Yusuf wanda aka fi sani da Abba Gida gida ya karbi shaidar lashe zaben Gwamnan Kano.
Ya karbi wannan shaida ce yayin wani taro da hukumar INEC ta shirya domin bashi shaidar satifiket, bayan nasarar da ya samu a zaben ranar 18 ga watan Maris 2023.
Taron dai Wanda ya samu halartar da dama daga cikin manyan jihar Kano dama shiyyar arewa maso yamma, ya gudana ne a dakin taro na ofishin hukumar zabe INEC na jihar Kano.
-
Nishadi3 years ago
Ina neman mijin aure – Rayya
-
Manyan Labarai3 years ago
KAROTA: An baiwa Baffa Babba wa’adin kwanaki bakwai
-
Labarai3 years ago
Auren dan Panshekara da ba Amurkiya ya samu cikas
-
Nishadi3 years ago
Mansura Isah ta yi kaca-kaca da Sadiya Haruna
-
Labarai2 years ago
Hamisu Breaker ya kai kan sa wajen ‘yan sanda
-
Lafiya10 months ago
Rahoto: An gano wani gida da ake gini da takardun Kur’ani da Alluna
-
Nishadi3 years ago
An gano daliban da Adam Zango ya dauki nauyin karatun su
-
Manyan Labarai3 years ago
Sabuwar damfarar da ta fito a Kano