Connect with us

Kasuwanci

Zargin cinye filin makaranta: Kotu ta sake aikewa karamar hukumar Gwale sammace

Published

on

Babbar kotun jiha mai lamba 17, karkashin jagorancin justice Sanusi Ado Ma’aji ta yi umarnin da a sake aikewa da karamar hukumar Gwale sammace a kunshin wata shari’a, wadda Alhaji Umar Sale da wasu mutane a unguwar Dorayi Babba suka shigar, suna karar karamar hukumar Gwale da wani mai suna Alh Umar Ibrahim yan shana.

Masu karar dai sun yi da’awar cewar, wadanda aka yi kara sun yi ruf da ciki akan wani katon filin makaranta mallakar mutanen unguwar Dorayi Babba Unguwar Jakada.

A zaman kotun na ranar Laraba, lauyan masu kara Barista Mustapha Zubair Kofar Na’isa ya bayyanawa kotun cewar, wannan shine karo na 3 da ake zaunawa akotun amma wadanda ake kara sun gaza bayyana a gaban kotun.

Kotun ta yi umarnin da a sake aike musu da sammace an kuma sanya ranar 24 gawatan Nuwanba domin ci gaba da shari’ar, kamar yadda wakulin mu Mu’az Musa Ibrahim ya rawaito.

Kasuwanci

Da sana’ar siyar da Awara a bakin Titi na sayi Fili, na gina Gida, kuma nake shirin yin Aure a Kano – Mai lalurar Kafa

Published

on

Wani matashi mai lalurar Kafa da ya rungumi sana’ar siyar da Awara a gefen titin Madobi mai suna Yusif Ibrahim mazaunin Damfami dake karamar hukumar Kumbotso ya shawarci Matasa da su tashi tsaye wajen riko da kananan sana’o’i domin su dogara da kansu.

Matashin mai lalurar kafar ya bayyana hakan ne yayin zantawarsa da wakikinmu na ‘yan Zazu Hassan Mamuda Ya’u, yana mai cewa riko da sana’ar na taimakawa mutum ya dogara da kansa, tare da magance wasu matsaloli da suke damunsu na yau da kullum.

“Sana’ar siyar da Awarar da nake yi da ita na sayi Fili, na gina Gida, yanzu haka kuma ina shirin yin Aure; Ina ganin budi dan haka akwai bukatar sauran matasa su nemi abin yi ko da sana’ar siyar da Awara ne, “in ji shi”.

Matashin ya kara da cewa akwai kalubale a sana’ar amma dai nasarorin sun fi yawa.

Continue Reading

Kasuwanci

Rashin tallafa mana na kawo nakasu a sana’ar mu – Masu yafin kayan lambu

Published

on

Sakatariyar kungiyar mata masu sana’ar yafin Iraruwan kayan lambu na yankin garin Ali dake karamar hukumar Garko Kubra Hassan, ta ce tallafawa masu yafin irin da abubuwan da suka sawwaka, zai taimaka musu wajen wadata kasar nan da kayan lambu ba sai an shigo da su daga kasashen ketare ba.

Kubra Hassan ta bayyana hakan ne yayin zantawarta da wakilinmu na ‘yan Zazu Hassan Mamuda Ya’u, tana mai cewa yanzu haka mata sun rungumi aikin yafin iraruwan kayan lambun, amma rashin tallafa musu daga bangaren gwamnati shine babban kalubalensu wanda hakan kan kawo musu koma baya a sana’ar tasu.

“Mata ku tashi tsaye wajen rungumar kananan sana’o i domin ku dogara da kan su, tare da taimakawa kanku da ma mazajenku a gidan aure, “in ji Kubra,”

Kubra Hassan ta kuma kara da cewa, babban burinsu shine wadata kasar nan da kayan lambu mai-makon ace an dogara da na kasashen ketare.

Continue Reading

Kasuwanci

Rashin taimaka mana yana kawo mana koma baya a Kano – Manoman Tafarnuwa

Published

on

Wani manomin Tafarnuwa dake garin Kofa a karamar hukumar Bebeji mai suna Bala Abdullahi Kofa, ya ce rashin samun tallafi a sana’arsu ta noman Tafarnuwa daga gwamnati kan kawo musu koma baya.

Mallam Bala Abdullahi ya bayyana hakan ne yayin zanatawarsa da wakilinmu Usaini Abdullahi Kofa a ranar Litinin, yana mai cewa matukar gwamnati ta shigo wajen tallafa musu da Taki, da samar musu da Famfon Burtsatse, babu makawa hakan zai kara bunkasa sana’ar tasu ta Noman Tafarnuwar.

Da yake nasa jawabin shima wani Manomin Tafarnuwar mai suna mallam Dalha Labaran Kofa, ya ce karin kalubalen da suke fuskanta a harkar noman Tafarnuwar shine yadda take konewa idan sun dasa ta, biyo bayan rashin wadataccen Taki da sauran matsaloli, inda suke neman daukin mahukunta.

Wannan dai na zuwa ne a dai-dai lokacin da manoma da dama ke kara neman tallafin mahukunta, domin kara bunkasa sana’arsu ta Noma a gurare daban-daban.

Continue Reading

Trending