Connect with us

Siyasa

Atiku ya na yi min katsalandan a lamura na – Gwamnan Benue

Published

on

Gwamna Samuel Ortom na jihar Benuwe, ya zargi jam’iyyar PDP, dan takarar shugaban kasa, Atiku Abubakar da yin katsalandan a kansa.

Ortom ya bayyana cewa, Atiku ya dauki matakin ne saboda ya bukaci a ba shi hakuri bisa kuskuren zarginsa da yi masa na bata sunan Fulani a jihar Binuwai.

Ortom, wanda ya kara da zargin Atiku da guje masa a nadin kungiyar yakin neman zabensa, ya bayyana hakan ne a fadar gwamnatin jihar da ke Makurdi.

Ya kara da cewa ya kira Atiku da ya karyata maganar a kafafen yada labarai, amma bai taba yi ba.

Gwamnan ya sha alwashin ba zai daina yin shiru ba kan kashe-kashe da korar mutanen jihar da makiyaya ke yi.

A cewar Ortom: “Lokacin da Atiku ya yi magana a Arewa House kwanakin baya, inda ya zarge ni da bayyana Fulani a matsayin masu laifi, na kira shi ne domin ya nuna rashin jin dadina a kan lamarin, na kuma kira shi da ya nemi afuwa.

“Atiku bai taba yi ba, kuma ya zagaya ya zage ni wajen daukar tsarin yakin neman zabensa. Duk da haka muna jiran ranar zabe.

“Ina da Fulani a cikin gwamnatita kuma za su iya rayuwa cikin walwala a jihar. Amma dole ne su mutunta dokar kasa.

“Hare-haren makiyaya da dama sun bar jihar mu ta zama tarihi, inda sama da ‘yan gudun hijira miliyan biyu ke sansanin kuma sun ce kada in yi magana.”

Hangen Dala

Take hakki:- Matakin Amnesty game da kama wasu ‘yan jarida a Kano

Published

on

Ƙungiyar kare haƙƙin ɗan adam ta Amnesty International, ta yi ala-wadai da cin zarafin ‘yan jarida biyu a Kano, wato mawallafin jaridar kano Times, Buhari Abba da kuma Isma’il Auwal.

Cikin sanarwar sa Ƙungiyar ta wallafa a shafin ta na facebook,
ta ce babu shakka abin da rundunar ‘Yansandan jihar Kano ta yi bisa umarnin Kwamishinan yaɗa labaran jihar, Ibrahim Waiya abin takaici ne.

Rundunar ‘Yansandan jihar Kano dai ta gayyaci Buhari Abba zuwa sashin binciken manyan laifuka (CID) ne, harma kuma ta tsare shi na tsawon awanni.

Kuma dai ana tuhumar mutanen biyun ne da zargin ɓata sunan kwamishinan, ta hanyar wani ra’ayi da jaridar ta wallafa wanda Isma’il Auwal ya rubuta.

Kungiyar ta Amnesty ta ce duk ba zata lamunci duk wani yunƙuri na takewa waɗannan ‘Yan jarida haƙƙinsu ba.

A ƙarshe ƙungiyar taja hankalin gwamantin kano da kuma rundunar ‘Yansandan jihar, da su guji yunƙurin daƙile ‘yancin faɗin albarkacin baki.

Continue Reading

Baba Suda

Gwamnatin Kano ta musanta labarin da ke cewa za ta saka kafar Wando daya da Sojojin Baka

Published

on

Gwamnatin jihar Kano ta musanta labarin da ke yawo na cewa za ta saka kafar wando daya da Sojojin Baka.

 

Kwamishinan yada labaran jihar Kwamred Ibrahim Waiya shi ne ya bayyana hakan lokacin wani taron karawa juna sani da hukumar kula da kafafen yada labarai NBC ta shirya a yau Alhamis.

 

Yace gwamnatin Kano za ta hada kai da Yan siyasa masu magana a Rediyo da aka fi Sani da Sojojin Baka, domin tsaftace harkokin siyasar Kano.

 

Haka kuma kwamishinan ya musanta labarin da ke cewa Gwamnatin Kano za ta saka kafar wando daya da Sojojin Baka.

 

Kwamishina Waiya ya kuma ce za su hada kai da kafafen yada labarai domin Kara kawo tsafta a harkokin siyasar Kano.

Continue Reading

Labarai

Tsohon shugaban majalisar Dattawa Ahmad Lawan ya ƙaryata ficewar sa daga APC zuwa SDP

Published

on

Tsohon shugaban majalisar Dattawa Ahmad Lawan, ya musanta wata jita-jita da ake yaɗawa kan cewar ya fice daga cikin jam’iyyar APC mai mulki a ƙasa, zuwa SDP, al’amarin da ya ce bashi da tushe ballantana makama.

A cikin wata sanarwar da mashawarci na musamman ga tsohon Sanatan a kafafen yaɗa labarai Ezrel Tabiowo, ya fitar a jiya Lahadi, ta ce jita-jitar da ake yaɗawa na cewar Ahmad Lawan ya fice daga jam’iyyar ta APC, ƙarya ce tsagwaronta.

Jaridar Daily trust ta ruwaito cewar, sanarwar ta kuma ce, har yanzu Ahmad Lawan ɗan Jam’iyyar APC ne, kuma yana biyayya ga jam’iyyar, wadda yake alfahari da ita.

Continue Reading

Trending