Siyasa
An rantsar da sababbin shugabannin kananan hukumomin Osun

Gwamna Gboyega Oyetola, ya rantsar da sabbin zababbun shugabanni da kansilolin kananan hukumomin jihar Osun.
An zabi sabbin shugabannin kananan hukumomin ne a zaben da hukumar zabe mai zaman kanta ta jihar Osun ta shirya.
Jam’iyyar siyasa daya ce ta APC ta shiga zaben da aka gudanar a ranar Asabar 15 ga watan Oktoba.
Da ya ke zantawa da zababbun shugabannin jim kadan bayan an rantsar da su, a gidan Bola Ige da ke sakatariyar jihar, Osogbo, Oyetola ya bukaci shugabannin kananan hukumomin da su ciyo wani ganye daga salon mulkinsa na gaskiya da rikon amana da aka shafe tsawon shekaru hudu ana yi. shekaru.
Gwamnan ya kara da cewa su kasance masu adalci da adalci da sanin ya kamata ga jama’a a duk wata mu’amalar da suke yi domin talakawan kasa su ci gaba da jin tasirin jam’iyyar APC a jihar.
A yayin da yake kara musu kwarin guiwar ganin mutanen da suka zabe su a matsayin wadanda suka mallaki ofishin, gwamnan jihar ya bukace su da su gudanar da kyakkyawan aikin da aka zabe su ta hanyar dimokradiyya.

Hangen Dala
Jami’ar Chikago ta baiwa Atiku bayanan Tinubu

Jami’ar Jihar Chicago da ke Amurka ta saki takardun karatun Shugaba Bola Tinubu, bayan da ɗan takarar shugaban ƙasar a a 2023 ƙarƙashin jam’iyyar PDP Atiku Abubukar ya buƙaci hakan.
A ƙarshen makon da ya gabata ne, wata kotun gunduma da ke arewacin Illinois a Amurka ta bayar da umarnin a sakarwa Atiku takardun karatun Tinubu.
A wani martani na buƙatar da Atiku ya miƙa a karo na uku, wanda ya nemi a saki kwafin sakamakon digiri 1977, Jami’ar ta ce takardun sun yi daidai da na Tinubu da ke ɗauke da kwanan watan 27 ga watan Yunin 1977.
“Bayan bincike mai zurfi, Jami’ar CSU ta gano ta kuma gabatar da takardun da aka nema kuma ta gabatar da su don amsa wannan bukatar. Lambobin takardun su CSUO008 zuwa CSU0010.
“An shafe sunayen ɗaliban da ke kan takardun saboda a sakaya sunansu.
“CSU za ta kuma saki sakamakon daliban da suke kusa da shi, masu lamba CSU0011 da lamba 0017 na wasu ɗaliban bayan an doɗe sunayen (saboda a sakaye sunanyensu)”.
“Waɗannan takardun sun yi daidai da yadda na Tinubu, dalibin da aka yi wa sauyin makaranta yake,” kamar yadda jami’ar ta rubuta.
A baya Tinubu ya yi iƙirarin ɓatan ainihin takardunsa na jami’ar, abin da ya sa ya gabatarwa da hukumar zaɓe INEC wata takardar a matsayin madadin takardun na ainihi domin takarar shugabancin Najeriya a 2023.
Takardu da dama na waɗari a kafafen sada zumunta a matsayin shaidar kammala karatun na Tinubu a Jami’ar jihar Chicago.
Tambari da kuma bajon da jami’ar CSU ta saki na digirin a 1977 sun yi daidai da irin wanda Shugaba Tinubu ya gabatar wa INEC, sai dai an samu banbanci a kwanan wata.
Sai dai cikin bayanin da jami’ar ta yi, ta ɗauki alhakin kuskuren da aka samu a kwanan watan, tana cewa kuskure aka samu wajen rubutawa.
A ranar 19 ga watan Satumba ne, Jeffrey Gilbert na kotun majitare da ke Amurka ya amince da buƙatar da aka shigabar gaban kotun tare da ba da umarnin sakin takardun karatun Bola Tinubu cikin sa’a 24.
A wani ƙoƙari na ganin haka bai faru ba, Tinubu ya ɗaukaka ƙara kan wannan umarni.
Nancy Maldonado ta kotun tarayya ta sake tabbatar da wannan hukunci da Tinubu ya so ƙalubalanta, inda ita ma ta ce a saki takardun.
Domin bin umarnin kotun da cika buƙatar Atiku Abubakar CSU ta ce ba za ta iya nemo ainihin kwafin takardun da ta bai wa Tinubu ba 1979.
“A tsarin CSU ba ta ajiye kwafin takardun ɗaliban da suka yi digiri, kuma bayan dogon bincike ta gaza samo kwafin irin wanda ta bau wa Tinubu a 1979, don haka ba a samu takardun da aka buƙata ba,” in ji jami’ar.
Sai dai jami’ar ta saki takardun wasu ɗaliban da ta rufe sunayensu, waɗanda suka yi daidai da na Tinubu domin tabbatar da cewa ya kammala makarantar a baya.
Atiku Abubakar dai na son amfani da takardun ne a matsayin shaida a kotun ƙolin Najeriya kan ƙorafin da ya shigar game da sakamakon zaɓen shugaban ƙasar da aka yi a 2023.
BBC

Hangen Dala
Hukuncin Kaduna :- PDP za ta daukaka kara

Jam’iyyar PDP reshen jihar Kaduna ta yi watsi da hukuncin kotun sauraron kararrakin zaben gwamna da ta tabbatar da zaben Gwamna Uba Sani na jam’iyyar APC, inda ta ce za ta garzaya kotun daukaka kara.
Alberah Catoh, Sakataren Yada Labarai na Jam’iyyar PDP ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya raba wa manema labarai a ranar Juma’a a Kaduna.
Catoh ya ce, wani nazari da lauyan PDP ya yi ya nuna cewa hukuncin bai cika wasu ka’idoji na tabbatar adalci ba.
Martanin ya zo ne sa’o’i bayan kotun da ke zamanta a Kaduna ta amince da nasarar zaben Sani.
Ya kara da cewa hukuncin bai dace da wasu dokoki da ka’idojin zabe ba.
Sanarwar ta kara da cewa, “Saboda haka jam’iyyar ta umurci lauyoyinta da su daukaka kara kan hukuncin da aka yanke a kotun daukaka kara da ke Abuja a cikin wa’adin da doka ta kayyade.”
Catoh ya kuma bukaci magoya bayan jam’iyyar PDP a fadin jihar da su kwantar da hankalinsu tare da nuna kwarin gwiwarsu kan lamarin.

Hangen Dala
Hukuncin kotu:- Zamu daukaka Kara – Abba Gida Gida

Gwamnan jihar Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf yace zasu ɗauki matakin ɗaukaka ƙara zuwa gaba domin tabbatar da adalci kan hukuncin da kotun sauraron korafe-korafen zabe ta yanke inda ta ayyana Alhaji Nasiru Yusuf Gawuna a matsayin wanda ya lashe zaben Gwamnan da aka gabatar a watan Maris din 2023.
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bayyana hakan ne yayin wani taron manema labarai da ya gudana a fadar gwamnatin Kano a daren laraba.
Gwamnan ya ƙara da cewa sun umarci lauyoyin su da su hanzarta wajen ɗaukaka ƙara ba tare da ɓata lokaci ba.
Ka zalika ya kuma ce wannan hukuncin bazai sanyar musu da gwiwa ba wajen ci gaba da gudanar da ayyukan da suka fara.
A ranar Laraba ne dai 20 ga watan Satumba 2023 kotun sauraron korafe-korafen zabe ta tabbatar da Nasiru Gawuna a matsayin Wanda ya lashe zaben Gwamnan Kano da aka gabatar a watan Maris. (more…)

-
Nishadi4 years ago
Ina neman mijin aure – Rayya
-
Manyan Labarai4 years ago
KAROTA: An baiwa Baffa Babba wa’adin kwanaki bakwai
-
Labarai3 years ago
Hamisu Breaker ya kai kan sa wajen ‘yan sanda
-
Nishadi4 years ago
Mansura Isah ta yi kaca-kaca da Sadiya Haruna
-
Labarai4 years ago
Auren dan Panshekara da ba Amurkiya ya samu cikas
-
Lafiya1 year ago
Rahoto: An gano wani gida da ake gini da takardun Kur’ani da Alluna
-
Nishadi4 years ago
An gano daliban da Adam Zango ya dauki nauyin karatun su
-
Manyan Labarai4 years ago
Sabuwar damfarar da ta fito a Kano