Connect with us

Ƙasashen Ƙetare

Gada mai shekaru sama da 100 ta yi sanadiyar mutuwar mutane 130 a Indiya

Published

on

Yan sanda a kasar India, sun tabbatar da mutuwar mutane fiye da 130, lokacin da wata gada da ta kwashe shekaru sama da 100 ana amfani da ita ta karye, abinda ya sanya wasu da dama fadawa cikin ruwa.

Daya daga cikin manyan jami’an ‘yan sanda a kasar ta India, Ashok Kumar Yadav, ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na AFP cewar zuwa wayewar garin Litinin din nan, adadin mutane 132 aka tabbatar da mutuwarsu bayan rushewar gadar da ta kwashe kusan shekaru 150 ana amfani da ita.

Ministan dake kula da Yammacin jihar Gujerat, Brijesh Merja yace kuma anyi nasarar ceto mutane sama da 80 da ransu.
Mahukunta sun ce akalla mutane kusan 500 ke kan gadar lokacin da ta rufta sakamakon sakewar da igiyoyin dake rike da ita suka yi, cikin su harda mata da yara.

Ita dai wannan gadar ba’a dade da kammala gyaranta ba, tana garin Morbi ne dake da nisan kilomita 200 daga Ahmedabad a Jihar Yammacin Gujerat.

Kafofin yada labaran kasar sun ce mutanen da suka taru akan gadar suna gudanar da ibada ne akan kogin Machchhu, yayin da wasu kafofi suka nuna hotunan bidiyon da ake bayyana cewar na hadarin ne dauke da mutanen dake kokarin yin fito domin tsira da rayukansu.

Kamfanin talabijin na NDTV yace an bude gadar ne ba tare da samun takardar inganci daga hukumomin dake kula da aikin ba

Ƙasashen Ƙetare

Sojoji Sun yi juyin Mulki a Gabon

Published

on

Sojoji sun bayyana a gidan talabijin na kasar Gabon tare da sanar da karbi mulki.

Sun ce sun soke sakamakon zaben da ka gudanar ranar Asabar, inda aka ayyana shugaba Ali Bongo a matsayin wanda ya lashe zaben.

Hukumar zaben ta ce Mr Bongo ya samu nasara ne da kasa da kashi biyu bisa uku na kuri’un da aka kada a zaben da ‘yan adawa suka ce an tafka magudi.

Sun Kuma ce Hambarar da shi zai kawo karshen mulkin shekaru 53 da iyalan gidansu ke yi a Gabon.

Sojoji 12 ne suka bayyana a gidan talabijin dake sanar da soke sakamakon zaben tare da rusa dukkan hukumomin kasar.

Daya daga cikin sojojin ya fada a tashar talabijin ta Gabon 24 cewa, “Mun yanke shawarar kare zaman lafiya ta hanyar kawo karshen mulkin da ake yi a yanzu.”

Mr Bongo ya hau karagar mulki lokacin da mahaifinsa Omar ya rasu a shekara ta 2009.

Continue Reading

Ƙasashen Ƙetare

Sojoji sunyi juyin Mulki a jamhuriyar Nijar

Published

on

Rahotanni daga jamhuriyar Nijar na cewa Sojojin Kasar sun yi juyin Mulki, tare da sanar da kawo karshen mulkin shugaba Muhammad Bazum.

Cikin sanarwar da suka bayar a gidan telebijin din Kasar, jagoran tawagar sojojin Kanal Amadu Abdramane yace “mun kawo karshen mulkin shugaba Muhammad Bazum tare da karbe dukkanin Wani Iko”.

Sojojin dai sun bayar da dalilin halin rashin tabbas da Kuma Matsin tattalin arziki a kasar.

Tuni dai sojojin suka garkame dukkanin iyakokin Kasar tare da Sanya dokar takaita zirga zirga daga karfe 10 na dare zuwa 6 na safe.

Tun a safiyar laraba ne dai aka wayi gari da fara wancan yunkuri, Wanda yanzu haka ta tabbata, Kasar Nijar na hannun sojoji, Wanda shi ne Karo na hudu ana gudanar da juyin mulkin a jamhuriyar Nijar.

Continue Reading

Ƙasashen Ƙetare

An tsaurara tsaro a fadar shugaban Kasar Nijar

Published

on

Rahotanni daga Jamhuriyar Nijar, na nuni da cewa dakarun da ke gadin fadar shugaban ƙasa sun rufe duk wata hanyar shiga fadar a wani lamari da ba a kai ga ganowa ba.

Sai dai rahotanni na cewa yanzu haka wasu daga cikin tsofaffin shugabannin ƙasar ta Nijar na tattaunawa da sojojin domin sasanta lamarin.

Karin bayani nan tafe….

Continue Reading

Trending