Connect with us

Ƙasashen Ƙetare

Zaben Brazil: Tsohon shugaban kasa ya karbi kujerarsa a hannun shugaba mai ci

Published

on

Luiz Inácio Lula da Silva ya lashe zaben shugaban kasar Brazil, bayan samun kusan kashi 51 na yawan kuri’un da aka kada, a zagaye na biyu na zaben da ya gudana a ranar Lahadi.

Sakamakon da hukumar zaben Brazil ta fitar ya nuna cewar, Lula ya samu kashi 50.8 na kuri’un da aka kada yayin da shugaba mai ci Jair Bolsonaro ya samu kashi 49.2.

Bayanai sun ce da fari shugaba Bolsonaro ne ya kasance kan gaba a lokacin da aka fara kidayar kuri’un da aka kada, amma da kidaya ta yi nisa, sai lissafi ya sauya, inda Lula da Silva ya koma kan gaba, lamarin da ya janyo barkewar sowar mutane da kuma wasa da motoci a titunan birnin Sao Paulo.

Zaben shugabancin na Brazil dai shi ne wanda ya fi daukar hankali, tun bayan komawar kasar ga mulkin dimokradiyya a shekarar 1985. Haka Zalika wannan shi ne karo na farko a Brazil da shugaban kasar mai ci ya kasa yin tazarce.

Al’ada ce a Brazil dan takarar da ya sha kaye ya fara gabatar da jawabi, ya kuma amince da shan kaye, sai dai sa’o’i bayan da hukumar zabe ta bayyana Lula a matsayin wanda ya lashe zaben, Bolsonaro bai yi wata sanarwa a bainar jama’a ba kan sakamakon. Abinda ya sanya wasu tunanin kila shugaban mai ci ya kalubalanci kayen da aka ce ya sha.

Ƙasashen Ƙetare

Sojoji Sun yi juyin Mulki a Gabon

Published

on

Sojoji sun bayyana a gidan talabijin na kasar Gabon tare da sanar da karbi mulki.

Sun ce sun soke sakamakon zaben da ka gudanar ranar Asabar, inda aka ayyana shugaba Ali Bongo a matsayin wanda ya lashe zaben.

Hukumar zaben ta ce Mr Bongo ya samu nasara ne da kasa da kashi biyu bisa uku na kuri’un da aka kada a zaben da ‘yan adawa suka ce an tafka magudi.

Sun Kuma ce Hambarar da shi zai kawo karshen mulkin shekaru 53 da iyalan gidansu ke yi a Gabon.

Sojoji 12 ne suka bayyana a gidan talabijin dake sanar da soke sakamakon zaben tare da rusa dukkan hukumomin kasar.

Daya daga cikin sojojin ya fada a tashar talabijin ta Gabon 24 cewa, “Mun yanke shawarar kare zaman lafiya ta hanyar kawo karshen mulkin da ake yi a yanzu.”

Mr Bongo ya hau karagar mulki lokacin da mahaifinsa Omar ya rasu a shekara ta 2009.

Continue Reading

Ƙasashen Ƙetare

Sojoji sunyi juyin Mulki a jamhuriyar Nijar

Published

on

Rahotanni daga jamhuriyar Nijar na cewa Sojojin Kasar sun yi juyin Mulki, tare da sanar da kawo karshen mulkin shugaba Muhammad Bazum.

Cikin sanarwar da suka bayar a gidan telebijin din Kasar, jagoran tawagar sojojin Kanal Amadu Abdramane yace “mun kawo karshen mulkin shugaba Muhammad Bazum tare da karbe dukkanin Wani Iko”.

Sojojin dai sun bayar da dalilin halin rashin tabbas da Kuma Matsin tattalin arziki a kasar.

Tuni dai sojojin suka garkame dukkanin iyakokin Kasar tare da Sanya dokar takaita zirga zirga daga karfe 10 na dare zuwa 6 na safe.

Tun a safiyar laraba ne dai aka wayi gari da fara wancan yunkuri, Wanda yanzu haka ta tabbata, Kasar Nijar na hannun sojoji, Wanda shi ne Karo na hudu ana gudanar da juyin mulkin a jamhuriyar Nijar.

Continue Reading

Ƙasashen Ƙetare

An tsaurara tsaro a fadar shugaban Kasar Nijar

Published

on

Rahotanni daga Jamhuriyar Nijar, na nuni da cewa dakarun da ke gadin fadar shugaban ƙasa sun rufe duk wata hanyar shiga fadar a wani lamari da ba a kai ga ganowa ba.

Sai dai rahotanni na cewa yanzu haka wasu daga cikin tsofaffin shugabannin ƙasar ta Nijar na tattaunawa da sojojin domin sasanta lamarin.

Karin bayani nan tafe….

Continue Reading

Trending