Labarai
Ganduje ya gabatar da kasafin karshe a gwamnatinsa na Naira biliyan 245.3

Gwamnan jihar Kano, Dr. Abdullahi Ganduje, ya gabatar da kasafin kudi na Naira biliyan 245.3 a majalisar dokokin jihar na shekarar 2023.
Wanda aka yiwa lakabi da Budget for Consolidation and Prosperity II, kididdigar sun haura Naira biliyan 49, sama da kasafin kudin 2022, a safiyar Juma’a
A shekarar da ta gabata Ganduje ya gabatar da sama da Naira Biliyan dari da casa’in da shida (N196b) ga majalisar dokokin jihar Kano, na shekarar 2022.
Kudirin kasafin kudi na shekarar 2023 da aka gabatar yana da Naira biliyan 144.6 a matsayin babban kashe kudi wanda ke wakiltar kashi 59 cikin 100 na jimillar kasafin kudin, yayin da kudaden da ake kashewa akai-akai a cikin kudirin da aka gabatar ya kai sama da Naira biliyan 100, wanda ke wakiltar kashi 41 cikin 100 na girman kasafin.
Kunshin kasafin dai shi ne na karshe na irin wannan gabatarwar da Ganduje ya yi a gaban majalisar dokokin jihar, domin a watan Mayun shekara mai zuwa ne ake sa ran zai mika mulki.

Hangen Dala
Rashin wuta: Muna cikin mawuyacin hali – al’ummar Kano, Katsina da Jigawa

Al’ummar jihohin Kano, katsina da Jigawa na fuskantar yanayi mara dadi, Sakamakon karancin samun wutar lantarki daga hukumar KEDCO.
Al’ummar jihohin sun ce iya sa’o’i uku kacal suke samun wutar, wanda hakan ke haifar musu da nakasu a harkokin kasuwancin su.
Wani bincike da jaridar Daily Trust tayi ta ambato yadda masu kananan masana’antu irin su Walda, Cajin Waya, Kankara da masu sana’ar dinki da dai sauran kananan sana’o’i dake amfani da wutar lantarki sun shiga mawuyacin hali.
Kazalika rashin wutar ya shafi hatta bangaren ruwan sha, dama masu sana’ar sayar da Ruwa a irin yankunan Hotoro da sauran irin wuraren dake sayen ruwa, Inda yanzu haka ruwan yayi tashin gwauron zabi a kowace jarka.
Koda dai ana ta bangaren hukumar rarraba hasken wutar lantarkin me kula da shiyyar Kano, Katsina da Jigawa KEDCO sun nemi afuwar al’umma.
Idan za’a tuna dai a makon jiya ne Ministan Wutar lantarki yace ‘yan Nigeria Miliyan 150 na samun wadatacciyar wutar lantarki.
Sai dai kuma a jihohi irin su Kano, Katsina da Jigawa na bayyana damuwa kan karancin Wutar, Inda suka ce bata wuce ta sa’o’i uku suke samu a kowa ce rana.

Hangen Dala
Rashin wuta:- Muna cikin mawuyacin hali – al’ummar Kano, Katsina da Jigawa

Ci gaba ba ya zuwa sai an samu haɗin kan al’umma – Dagacin Ja’en

Dagacin garin Ja’en da ke ƙaramar hukumar Gwale a jihar Kano, Alhaji Isma’il Sa’ad Usman, ya ce hadin kai ne kaɗai zai kawo ci gaba ga kowa ce irin al’umma.
Dagacin ya bayyana hakan ne Jim kaɗan bayan wani taron masu Ruwa da tsaki na Garin Ja’en, wanda Hakimin Gundumar Ɗorayi Barde Kerarriya Alhaji Shehu Kabir Bayero ya shirya, aka gudanar a yankin Ja’en a ƙarshen makon da ya gabata.
“Dukkanin wani ci gaba ba ya zuwa har sai an samu haɗin kan kowa ne bangare na al’umma, “in ji Dagacin”.
Wakilin Dala FM Kano, Ahmad Rabi’u Ja’en ya ruwaito cewa, taron ya samu halartar dukkanin bangarori, na unguwannin Ja’en, da suka haɗar da kungiyar mafarauta da maharba dabma kungiyar malaman makaranta.

-
Nishadi5 years ago
Ina neman mijin aure – Rayya
-
Labarai5 years ago
Hamisu Breaker ya kai kan sa wajen ‘yan sanda
-
Nishadi6 years ago
Mansura Isah ta yi kaca-kaca da Sadiya Haruna
-
Manyan Labarai5 years ago
KAROTA: An baiwa Baffa Babba wa’adin kwanaki bakwai
-
Labarai5 years ago
Auren dan Panshekara da ba Amurkiya ya samu cikas
-
Lafiya3 years ago
Rahoto: An gano wani gida da ake gini da takardun Kur’ani da Alluna
-
Manyan Labarai5 years ago
Sabuwar damfarar da ta fito a Kano
-
Nishadi5 years ago
An gano daliban da Adam Zango ya dauki nauyin karatun su