Manta Sabo
Raini: Kotu ta yi watsi da hukuncin da aka yi wa Shugaban EFCC

Babbar kotun tarayya da ke Abuja ta yi watsi da hukuncin da ya shafi shugaban hukumar EFCC, Abdulrasheed Bawa da laifin raina kotu.
Mai shari’a Chizoba Oji ce ta ya yi watsi da hukuncin a ranar Alhamis, bayan sauraron ƙorafin da shugaban hukumar yaƙi da rashawa da yi wa tattalin arziƙin ƙasa ta’annati ya shigar.
Kotun ta ce ta gano cewar ba za a iya cewa shugaban na EFCC ya raina kotu a lokacin da aka yanke hukuncin ba, kasancewar ya riga ya bayar da umurnin a mayar wa wanda ya shigar da ƙarar motarsa ƙirar Range Rover.
Kotun ta ce takardu sun nuna cewa an fara shirin mayar wa mai ƙorafin motarsa da kuma kuɗi naira miliyan 40.
A ranar Talata ne mai shari’a Chizoba Oji ta yanke hukuncin cewar EFCC ta raina kotu ta hanyar ƙin bin umurnin hukuncin da ya ce a mayar wa wani mutum motarsa da kuma kuɗi naira miliyan 40.

Manta Sabo
Kotu ta yanke wa wasu mutane 5 hukuncin Kisa ta hanyar Rataya a Kano

Babbar kotun jihar Kano, mai lamba huɗu karkashin jagorancin mai Shari’a Usman Na Abba, ta yanke hukuncin kisa ta hanyar rataya akan wasu mutane 5, waɗanda kotun ta samu da laifin haɗa baki da kisan kai.
Tunda fari gwamnatin jihar Kano ce ta gurfanar da mutanen a gaban kotun, da ake zargin su da haɗa baki da kisan kai.
Ƙunshin zargin da ake musu tun da fari ya bayyana cewar, a ranar 3 ga watan 9 na shekarar 2023 wata mata Mai suna Nadiya Ibrahim ta bayyana wa mai gidanta Faisal Yahaya cewar, ta yi mafarkin cewar wata makociyarsu mai suna Tsahare Abubakar ta biyo ta da wuka, bayan da ta farka kuma sai ta kama rashin lafiya.
Har ila yau, ƙunshin tuhumar ya bayyana cewar, Faisal ya yi zargin Tsahare mayyace, don haka ya gayyato wasu matasa 4 su ka bi Tsahare har gona suka daddatsa ta har sai da rai ya yi halinsa.
A yayin sauraron Shaidu lauyan gwamnati Barrister Lamido Abba Soron Ɗinki, ya gabatar da shaidu 4, kuma a yau kotun ta ayyana cewar, ta gamsu da shaidun masu gabatar da kara.
Kotun ta ayyana hukunci kisa ta hanyar rataya akan mutanen masu suna Daluta Ibrahim, da Abudil-Aziz Yahaya, da Faisal Yahaya, da kuma Ahmad Ibrahim, sai Abdurrahman Yakubu.
Sai dai kuma wata mata da ake tuhuma ta 6 mai suna Nadiya Ibrahim, kotun ta sallame ta sakamakon an gano cewar lokacin da aka yi kisan kan ita tana gida a kwance bata da lafiya.
Kazalika, kotun ta kuma gargadi yan uwan Tsahare akan cewar kada su cutar da Nadiya domin kotun ta gano bata da laifi.
Wakilimmu Yusuf Nadabo Isma’il ya ruwaito cewa, kotun ta kuma umarci Dagacin garin Ɗadin kowa da ke karamar hukumar Wudil, da su tabbatar an zauna lafiya akan wannan batu, har ma mai Shari’a Usman Na’Abba ya ce, ba a yin hukunci akan mafarki kuma idan wani ya faru da mutum sai ya tuntuɓi masana abin.

Manta Sabo
Kotu ta zartas da hukuncin rataye wani mutum har sai ya dai na numfashi a Kano

Babbar Kotun jahar Kano mai lamba 11 ƙarƙashin jagorancin mai Shari’a Nasir Saminu, ta zartas da hukuncin kisa akan wani mutum wanda kotun ta samu da laifin fashi da Makami.
Mutumin mai suna Abdurraham Yakubu mazaunin karamar hukumar Bele dake jihar Nassarawa, kotun ta same shi ne da laifin yi wa mutane da yawa fashi da makami ta hanyar amfani da muggan Makamai.
Cikin mutanen da mutumin ya yi wa fashin hadda wata mata mai suna Barrister Hajara Lawal Ahmad, wadda ya yi wa fashin mota da kuma Kuɗi.
Yayin da ya ke zartas da hukuncin mai Shari’a Saminu ya ayyana cewar, Kotun ta gamsu da shaidun da lauyan gwamnati Barrister Umar Yakubu ya gabatar, inda kotun ta yi watsi da shaidar da Abdurraham ya bayar domin kare kansa.
Kotun ta kuma bayyana cewar ta gamsu da muggan makaman da aka samu a hannun Abdurraham haramtattu ne, kuma ana tasarifi da su ta haramtacciyar hanya dan haka kotun ta yi umarnin a kashe shi ta hanyar rataya.
Wakilin Dala FM Kano, Yusif Nadabo Isma’il ya ruwaito cewa, bayan yanke hukuncin mai Shari’a Saminu ya yi masa addu’ar cikawa da kyau.

Manta Sabo
An yanke wa wani Matashi hukuncin kisan kai ta hanyar rataya bayan samun sa da laifi a Kano.

Babbar Kotun jaha mai lamba 7 karkashin jagorancin mai Shari’a Amina Adamu Aliyu, ta zartas da hukuncin kisa ta hanyar rataya akan wani matashi mai suna Abba Sulaiman, bisa samunsa da laifin kisan kai.
Tun da fari gwamnatin jahar Kano ce ta gurfanar da matashin a gaban kotun da kunshin tuhume-tuhume guda biyu.
An dai yi zargi matashin Abba da laifin hada baki da kisan kai.
Tashar Dala FM Kano, ta rawaito cewa, ƙunshin zargin ya bayyana cewar wani lokaci a cikin shekarar 2019, Abba Sulaiman ya haɗa baki da wasu matasa waɗanda a yanzu suka tsere, bayan da suka kashe wani matashi a unguwar Sauna Kawaji.
Yayin da take karanta hukuncin mai Shari’a Amina Adamu ta ayyana cewar, kotun ta karɓi shaidun masu gabatar da ƙara yayin da aka yi watsi da shaidar da Abban ya bayar dan kare kansa.
Wakilinmu Yusuf Nadabo Isma’il ya ruwaito cewar, kotun dai ta kuma ɗaure Matashi Abba Sulaiman shekaru biyar a laifin haɗa baki.

-
Nishadi5 years ago
Ina neman mijin aure – Rayya
-
Labarai4 years ago
Hamisu Breaker ya kai kan sa wajen ‘yan sanda
-
Nishadi5 years ago
Mansura Isah ta yi kaca-kaca da Sadiya Haruna
-
Manyan Labarai5 years ago
KAROTA: An baiwa Baffa Babba wa’adin kwanaki bakwai
-
Labarai5 years ago
Auren dan Panshekara da ba Amurkiya ya samu cikas
-
Lafiya3 years ago
Rahoto: An gano wani gida da ake gini da takardun Kur’ani da Alluna
-
Manyan Labarai5 years ago
Sabuwar damfarar da ta fito a Kano
-
Nishadi5 years ago
An gano daliban da Adam Zango ya dauki nauyin karatun su