Connect with us

Wasanni

Manchester United ta ci amana ta – Ronaldo

Published

on

Cristiano Ronaldo ya ce, Manchester United ta ci amanar sa yayin da ya ce, mai horas da kungiyar Erik ten Hag da wasu manyan jami’an gudanarwa na kokarin tilasta masa ficewa daga kungiyar a wata hira da aka yi da shi ranar Lahadi.

Dan wasan wanda ya lashe kyautar Ballon d’Or sau biyar, ya kasance dan wasa a fili a United tun lokacin da Ten Hag ya karbi ragamar horar da ‘yan wasan a watan Mayu.

An ladabtar da Ronaldo ne bayan da ya ki zuwa maye gurbinsa a wasan da suka doke Tottenham da ci 2-0 a watan da ya gabata, amma ya koma taka leda a ‘yan makonnin nan, har ma ya zama kyaftin dinkungiyar a wasan da Aston Villa ta doke su da ci 3-1 a karshen makon jiya.

Sai dai dan wasan mai shekaru 37 ba ya cikin tawagar a wasan da United ta doke Fulham da ci 2-1 a wasan karshe na ranar Lahadi kafin hutun mako shida na gasar cin kofin duniya.

“Ba ni da girmamawa gare shi saboda ba ya girmama ni,” in ji Ronaldo game da Ten Hag a wata hira da Piers Morgan ya yi da shi.

“Ba kocin kadai ba, amma wasu mutane biyu ko uku a kusa da shi su na cin amana.”

Da aka sake tambayarsa ko manyan shugabannin kulob din suna kokarin korar shi, Ronaldo ya amsa da cewa: “Eh, na ji an ci amana ni kuma na ji kamar wasu ba sa so na a nan ba kawai a bana ba har ma da bara.”

Ronaldo ya koma Old Trafford a watan Agustan 2021 daga Juventus.

Zamansa na farko a United ya kasance mai daukaka a karkashin jagorancin Alex Ferguson, inda ya lashe kofunan Premier uku, gasar zakarun Turai da kuma na farko na lashe kyautar Ballon d’Or a matsayin dan wasa mafi kyau a duniya.

Duk da kwallaye 24 da ya ci a duk wasannin da ya buga a kakar wasan da ta wuce, United ta sha fama da mummunan kamfen yayin da ta kare a matsayi na shida a gasar Premier kuma ta kasa tsallakewa zuwa gasar zakarun Turai.

Wasanni

Bayer Leverkusen ta zama zakarar gasar Bundesliga ta 2023/2024.

Published

on

Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Bayer Leverkusen ta zama zakarar gasar Bundesliga ta shekarar 2023/2024, bayan da suka samu nasara a kan Weder Bremen da ci 5-0.

Hakan ne kuma ya kawo ƙarshen shekaru 11 da Bayern Munich, da ta yi tana lashe gasar.

Wannan dai shi ne karo na farko da Bayer Leverkusen suka taɓa lashe gasar a tarihi, ida suka gaza ɗaukar kofin a shekarar 2002 a ranar ƙarshe ta gasar.

Har ila yau, a dai wannan shekarar ne su kayi rashin nasara hannun Shalke 04, a wasan ƙarshe na German Cup Da ci 4-2.

Haka kuma, Real Madrid suka doke su a wasan ƙarshe na zakarun nahiyar turai.

Rahotanni sun bayyana cewa ƙungiyar bata taɓa ɗaukar wata gasa ba a ƙarni na 21, sai bayan da Xavi Alonso ya karɓe su.

Continue Reading

Wasanni

Hukumar NPFL, ta amince da buƙatar Kano Pillars na ɗage wasan ta na mako na 28 da Enyimba

Published

on

Yanzu haka an samu dai-daito da hukumar NPFL, wanda ta amince da bukatar Kano Pillars na dage wasanta na mako na 28, da Enyimba zuwa ranar Alhamis, mai zuwa.

Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Kano Pillars, ce ta wallafa hakan a shafin ta na Facebook da yammacin Litinin ɗin nan, ta ce ƴan wasan ta za su tashi a gobe Talata, da safe zuwa Aba domin fafata wasannin su.

Idan dai ba’a manta ba ƙungiyar ta wallafa kaɗan daga irin ƙalubalen da take fuskanta a harkokin gudanarwar ta.

Pillars, ta wallafa ƙalubalen ne kamar haka, “A yanzu haka zancan da muke muku Kano Pillars ta rasa kudin da za taje garin Aba, domin buga wasan hamayya na Nigeria Premier league wato Zobia Classic”.

Wasan dai shine wasa mafi ɗaukar hankali a league din Nigeria baki ɗaya, ku taya mu yadawa dan Allah.

Continue Reading

Wasanni

Glesner ya zama sabon mai horas da Palace.

Published

on

Kungiyar kwallon kafa ta Crystal Palace ta sanar da nadin Oliver Glesner a matsayin sabon mai horaswar ta.

Glesner wanda tsohon mai horas da kungiyar kwallon kafa ta Eintracht Frankfurt ne mai shekaru 49 dan asalin kasar Austrian, ya maye gurbin tsohon mai horaswa Roy Hodson, wanda ake ganin ya gaza kai kungiyar ga tudun mun tsira.

A wasanni 16 da Crystal Palace ta buga a bayan nan ta yi rashin nasara a wasanni 10 duk karkashin jagorancin Roy Hodson wanda hakan yasa take mataki na 16 a teburin gasar firimiyar kasar Ingila.

Glesner dai ya rattaba kwantaragi da Palace har na tsawon shekaru biyu, zai kuma jagoranci kungiyar a wasan sa na farko da kungiyar kwallon kafa ta Burnley a ranar Asabar mai kamawa.

Continue Reading

Trending