Connect with us

Wasanni

Qatar 2020: FIFA ta kuma zabo mawakin Najeriya Kizz Daniel

Published

on

Tauraron mawakin Najeriya, Kizz Daniel, ya shiga cikin jerin fitattun mawaka da za su taka rawa a gasar cin kofin duniya na 2022 a Qatar.

Kizz Daniel shi ne dan Najeriya na biyu maiwaki da FIFA ta zabo domin faranta ran magoya bayan gasar kwallon kafa ta duniya.

Hukumar kula da kwallon kafa ta duniya a makon da ya gabata ta sanya Patoranking cikin fitattun taurarin mawakan da za su hau matakin a babban filin wasa na Qatar a ranar farkon bude wasan.

Mawakan biyu za su yi waka a Doha a ranar 23 ga Nuwamba.

Sunan Kizz Daniel na ainihi shine Oluwatobiloba Daniel Anidugbe.

Shi ne wanda ya lashe lambar yabo da yawa na Nigerian Afrobeats, Pop, R&B mawaƙin, kuma marubucin waƙa tare da fitattun waƙoƙi irin su Woju, Buja, Cough da sauran su.

Wasanni

Tsohon mai horas da Super Falcons Mabo ya rasu.

Published

on

Tsohon mai horas da tawagar ‘yan wasan kwallon kafa ta mata ta kasa, Super Falcons, Ismaila Mabo, ya rasu ya na da shekaru 80 a duniya.

Dan uwansa Salisu Nakande Mamuwa ne ya bayyana rasuwar ta sa a shafin sa na sada zumunta a safiyar yau Litinin.

Karanta wannan labarin: http://flying eagles

Kafin rasuwarsa dai Ismaila Mabo ya jagoranci Super Falcons a gasar cin kofin duniya na mata, inda ya jagorance su zuwa wasan dab da na kusa da na karshe a shekarar 1999, ya kuma jagorance su zuwa gasar wasannin Olympics a shekarar 2000 da kuma 2004.

Continue Reading

Wasanni

Silva ya tsawaita kwantaraginsa da Chelsea

Published

on

Thiago Silva wanda ke buga wasa a baya, ya sake tsawaita kwantaraginsa da kungiyar kwallon kafa ta Chelsea na tsawon shekara daya, inda kwantaragin zai kare a shekarar 2024.

Silva mai shekaru 38, ya koma kungiyar kwallon kafa ta Chelsea daga PSG ta kasar Faransa a shekarar 2020, kawo yanzu ya bugawa Chelsea wasanni 106.

Thiago Silva wanda dan asalin kasar Brazil ne, ya tallafawa Chelsea ta samu nasarori da dama wanda daga ciki harda nasarar lashe kofin zakarun nahiyar Turai.

Continue Reading

Wasanni

Za a iya Conte aikin gaggawa a mafutsara – Tottenham

Published

on

Kungiyar kwallon kafa ta Tottenham Hotspur, ta baiwa mai horas da kungiyar, Antonio Conte, hutu yayin da a yau ake shirin yi masa aikin tiyatar gaggawa a mafutsararsa.

Kungiyar ta Tottenham ta tabbatar da hakan a wata sanarwar da ta wallafa a shafin ta na internet.

Conte ya kamu da rashin lafiya a farkon wannan makon, kuma ya koka da matsanancin ciwon ciki.

An gano tsohon manajan na Chelsea ya na da cutar cholecystitis, yanayin da ke haifar da kumburi da ja na mafutsara.

Labarai mai alaka: Kungiyar kwallon kafa ta Tottenham ta dauki aron Danjuma daga Villarreal

Sanarwar ta Tottenham ta ce “A kwanan nan Antonio Conte ya yi rashin lafiya tare da matsanancin ciwon ciki.”

“Bayan an gano cutar cholecystitis, yau za a yi masa tiyata a mafitsara a yau, kuma zai dawo bayan wani lokaci idan ya samu murmurewa. Kowa a kungiyar ya na yi masa fatan alheri.” Inji Tottenham.

Continue Reading

Trending