Connect with us

Wasanni

Rauni: Dan wasan Faransa ya fice daga gasar cin kofin duniya

Published

on

Dan wasan baya na Faransa, Lucas Hernandez, ba zai buga sauran gasar cin kofin duniya ba, saboda raunin da ya ji a gwiwarsa a wasan da suka doke Australia.

Dan wasan baya na Bayern Munich mai shekaru 26 da haihuwa, ya ji ciwo ne gwiwarsa ta dama a wasan da kungiyar da ta kare da ci 4-1 a wasan farko.

Wasu manyan ‘yan wasan Faransa da suka hada da Karim Benzema na Real Madrid sun samu raunuka kafin a fara gasar.

“Na yi matukar nadama da Lucas,” in ji koci Didier Deschamps.

An tabbatar da girman raunin Hernandez ta hanyar duban MRI a safiyar Laraba.

Ya samu raunin a gwiwar sa ne a minti na 13 da fara wasa da Australia.

Wanda ya lashe kyautar Ballon d’Or, Benzema, mai shekaru 34, ba zai buga wasan kare kasarsa ba a gasar cin kofin duniya, sakamakon rauni a cinyarsa.

‘Yan wasan tsakiya Paul Pogba da N’Golo Kante suna fama da ciwo a kafarsu.

Dan wasan baya na Paris St-Germain Presnel Kimpembe ya janye daga wasan a ranar Litinin din da ta gabata bayan ya kasa murmurewa daga raunin da ya ji, inda aka maye gurbinsa da Axel Disasi na Monaco.

Bayan kwana biyu, dan wasan gaba na RB Leipzig, Christopher Nkunku, ba zai samu damar buga atisaye ba,, inda dan wasan Eintracht Frankfurt Randal Kolo Muani ya maye gurbinsa.

Wasanni

Kungiyar Al-Ittihad ta sallami mai horaswar ta Nuno.

Published

on

Kungiyar kwallon kafa ta Al-Ittihad da ke kasar Saudiyyah ta sallami mai horaswar ta Nuno Espirito Santo, bayan kwashe watanni 16 ya na horas da ita.

Santo dan asalin kasan Portugal mai shekaru 49, kuma tsohon mai horas da Kungiyar kwallon kafa ta Tottenham Hotspur ta kasar Ingila, ya fara horas da kungiyar Al-Ittihad ne a watan Yuli na shekarar 2022 bayan korar sa da kungiyar kwallon kafa ta Tottenham Hotspur ta yi.

Kungiyar kwallon kafa ta Al-Ittihad dai ta bayyana cewar ta sallami Nuno Espirito Santo ne sakamakon rashin kokari da kungiyar ta ke yi karkashin jagorancin sa, Al-Ittihad dai tayi nasara ne a wasanni 6 cikin wasanni 12 da ta buga a kakar bana.

A ranar Litinin din da ta gabata ne, Kungiyar kwallon kafa ta Air Force ta kasar Iraq, ta doke Al-Ittihad da ci 2 – 0 a wasan zakarun Asian Champions league.

Continue Reading

Wasanni

Kano Pillars ta koma mataki na hudu a gasar NPFL.

Published

on

Kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars ta koma mataki na hudu a gasar cin kofin kwararru na Nigerian

Pillar dai ta doke Kungiyar kwallon kafa ta Bayelsa United ne, da ci uku babu ko daya a wasan mako na shida na gasar ta shekarar 2023 zuwa 2024.

A ranar lahadi 5/11/2023 ne kungiyar ta Kano Pillars za ta ziyarci Kungiyar kwallon kafa ta Sporting Lagos a Jihar Lagos a wasan mako na bakwai na gasar.

Continue Reading

Wasanni

Sakamakon wasan mako na hudu na gasar NPFL

Published

on

Sakamakon wasan mako na hudu na gasar cin kofin kwararru na Najeriya na kakar 2023/2024 wato NPFL.

Tun a ranar Asabar din da ta gaba ta ne 21 Oktoba 2023, aka buga wasa daya tilo kamar haka÷

Niger Tornadoes 1 – 0 Bayelsa United

Sai dai an dage wasa tsakanin kungiyar kwallon kafa ta Doma United da Enyimba

Wasanni da aka buga a ranar Lahadi 22 Oktoba 2023 kuwa÷

Gombe United 1 – 0 Bendel Insurance

Akwa United 0 – 0 Shooting Stars

Heartland Owerri 1 – 1 Katsina United

Kano Pillars 1 – 0 Rivers United

Kwara United 1 – 1 Enugu Rangers

Lobi Stars 2 – 0 Abia Warriors

Plateau United 1 – 0 Sunshine Stars

Remo Stars 2 – 1 Sporting Lagos.

Continue Reading

Trending