Connect with us

Ƙasashen Ƙetare

‘Yan Sanda sun ce Beraye ne suka shanye hodar Ibilis a ofishin su

Published

on

‘Yan sandan kasar Indiya, sun ce ɓeraye sun lalata kusan kilogram 200 na hodar Ibilis da aka ƙwace a hannun wasu mutane da ke safararta aka kuma ajiye a ofishinsu.

“Ɓeraye kananan halittu ne da ba su san wani tsoron ‘yan sanda ba. Abu ne mai wahala iya kare su,” a cewar Kotu da ke zamanta a jihar Uttar Pradesh.

Kotun ta bukaci ‘yan sanda su gabatar da shaida da ke tabbatar da cewa ɓeraye ne suka lalata hodar.

Alkalin ya bada misali da kararraki uku da aka gabatar kan ɓeraye sun lalata kwayar.

Mai shari’a Sanjay Chaudhary ya ce ko a baya an samu rahotanni da ke cewa ɓerayen sun lalata kilo 195 na hodar iblis, da kuma kilo 700 duk a ofisoshin ‘yan sanda.

Sanjay ya faɗawa ‘yan sanda cewa ba su da kwarewar yaƙi da irin waɗannan ɓeraye. Ya ce hanya ɗaya tilo na kare aukuwar irin wannan shi ne kai hodar ko kwayar dakunan adana magunguna ko aiwatar da gwaji. In ji BBC.

Ƙasashen Ƙetare

Zaben Amurka: Zan sake tsaya wa takara a shekarar 2024 – Trump

Published

on

Tsohon shugaban kasar Amurka, Donald Trump, ya bayyana cewa zai tsaya takarar shugabancin kasar a zaben 2024 na jam’iyyar Republican.

Trump na neman komawa fadar White House bayan da ya sha kaye a yunkurinsa na sake tsayawa takara a zaben 2020 ga Joe Biden.

Ya bayyana hakan ne a ranar Talata yayin da yake jawabi a gidansa da ke Mar-a-Lago, Florida.

“Domin sake mayar da Amurka girma da daukaka. A daren yau ne nake sanar da cewa zan tsaya takarar shugabancin Amurka,” in ji Trump.

Ku tuna cewa Trump ya lashe zaben shugabancin Amurka a karon farko a shekarar 2016 lokacin da ya fafata da Hillary Clinton.

Trump zai zama shugaban kasa na biyu da zai sake karbar mulki a fadar White House idan ya yi nasara a shekarar 2024, inda ya zama shugaban kasa na 45 da na 47.

Continue Reading

Ƙasashen Ƙetare

Firaministan Rwanda ya sauka daga mukaminsa bayan ya sha Barasa

Published

on

Firaministan Rwandan ya sauka daga muƙaminsa tare da neman afuwar ‘yan ƙasar saboda shan barasa a lokacin da yake tuƙi.

Gamariel Mbonimana ya ajiye muƙaminsa kwana guda bayan da shugaban ƙasar Paul Kagame, ya soke shi kan yin tuki a lokacin da ya sha barasa.

A wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na Twitter mista Mbonimana ya nemi afuwar ‘yan ƙasar da kuma shugaban ƙasar yana mai alƙawarta cewa ”Ba zai sake shan giya ba”.

Tuƙi yayin da aka sha barasa laifi ne a ƙasar, da tararsa ta kai dala 140, tare da ɗaurin kwana biyar idan an kama shi.

Yayin da yake wani jawabi a ƙarshen mako shugaban ƙasar Paul Kagame ya soki ‘yan sandan ƙasar kan rashin kama firaministan, saboda ”Kariyar” da yake da ita.

Mista Mbonimana shi ne firaministan ƙasar tun shekarar 2018, mamba ne a jam’iyyar Liberal Party wadda ke kawance da jam’iyyar RPF ta shugaba Kagame mai mulkin ƙasar. In ji BBC.

Continue Reading

Ƙasashen Ƙetare

Mutumin da ya yi karyar ya mutu an sake kama shi

Published

on

Kotu ta yanke hukuncin cewa wani mutum da aka kama a wani asibiti a Scotland a bara, dan kasar Amurka ne mai suna Nicholas Rossi, bayan an kammala bincike. Mutumin ya yi iƙirarin cewa shi ne wanda aka yi masa kuskure, kuma ya dage cewa sunansa, Arthur Knight mai makon Nicholas Rossi. Amma Kotun Edinburgh Sheriff shaidar yatsansa sun yi daidai da na Rossi.

Hukumomi a Amurka na neman a tasa keyar Rossi, bisa zargin fyade da cin zarafi. Ana zargin cewa ya yi karyar mutuwar na sa ne kuma daga baya ya gudu zuwa kasar Scotland, domin gujewa fuskantar tuhuma. Ya shafe shekara guda a matsayin sunan shi Arthur Knight, kuma shi maraya ne daga Ireland wanda bai taba zuwa Amurka ba.

A dai watan Maris mai zuwa ne kotun za ta yanke hukuncin cewa za ta mika mutumin zuwa Amurka ya fuskanci hukunci ko akasin haka. A shekarar da ta gabata ne dai ‘yan sandan Scotland suka kama Rossi a wani asibiti bayan da aka gano zanen da yake a jikin hannun sa na Tatto ya yi kama da nasa a lokacin da ake bashi kulawa a asibitin bayan ya sha fama da cutar Covid 19.
Sai dai a gwajin shaidar zanen ya tsayar sa ta yi daidai da wanda ake tuhuma, kamar yadda kwararriyar mai bincike Lisa Davidson ta shaidawa kotu.

Continue Reading

Trending