Wasanni
Arsenal ta gaggauta daukar Ronaldo – Seaman

Tsohon mai tsaron ragar Arsenal, David Seaman, ya bukaci kungiyar da ta sayi tsohon dan wasan Manchester United Cristiano Ronaldo.
Seaman ya yi imanin cewa, zai zama cikakkiyar sa hannu idan Arsenal ta kawo Ronaldo filin wasa na Emirates.
Ronaldo a halin yanzu ya na da ‘yanci, bayan da aka soke kwantiraginsa da Manchester United a wannan makon.
An kawo karshen kwantiragin kyaftin din na Portugal kwanaki baya,n wata fitacciyar hirar da ya yi da mai yada labarai Piers Morgan, inda ya caccaki Manchester United, dangin Glazer, Erik ten Hag, da sauransu.
“Ronaldo bai yi nisa ba kuma zai dace da Arsenal,” Seaman ya shaida wa TalkTV.
“Zan yaba masa [ga hirar da ya yi, domin a fili ya na fadin gaskiya. Yawancin kayan da ya fito da su ba kayan da ba mu ji ba.
“Mun ji wasu gogaggun ‘yan wasa da yawa suna nishi da sukar Man United kan yadda kasa take da kuma horo.
“Hakan ya girgiza ni kuma bai kamata hakan ya faru ba. Ya kasance a duk faɗin duniya kuma ya ga yadda ko’ina ya ci gaba kuma ya dawo wurin ƙaunataccen Man United kuma babu abin da ya canza. “

Wasanni
Kungiyar Al-Ittihad ta sallami mai horaswar ta Nuno.

Kungiyar kwallon kafa ta Al-Ittihad da ke kasar Saudiyyah ta sallami mai horaswar ta Nuno Espirito Santo, bayan kwashe watanni 16 ya na horas da ita.
Santo dan asalin kasan Portugal mai shekaru 49, kuma tsohon mai horas da Kungiyar kwallon kafa ta Tottenham Hotspur ta kasar Ingila, ya fara horas da kungiyar Al-Ittihad ne a watan Yuli na shekarar 2022 bayan korar sa da kungiyar kwallon kafa ta Tottenham Hotspur ta yi.
Kungiyar kwallon kafa ta Al-Ittihad dai ta bayyana cewar ta sallami Nuno Espirito Santo ne sakamakon rashin kokari da kungiyar ta ke yi karkashin jagorancin sa, Al-Ittihad dai tayi nasara ne a wasanni 6 cikin wasanni 12 da ta buga a kakar bana.
A ranar Litinin din da ta gabata ne, Kungiyar kwallon kafa ta Air Force ta kasar Iraq, ta doke Al-Ittihad da ci 2 – 0 a wasan zakarun Asian Champions league.

Wasanni
Kano Pillars ta koma mataki na hudu a gasar NPFL.

Kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars ta koma mataki na hudu a gasar cin kofin kwararru na Nigerian
Pillar dai ta doke Kungiyar kwallon kafa ta Bayelsa United ne, da ci uku babu ko daya a wasan mako na shida na gasar ta shekarar 2023 zuwa 2024.
A ranar lahadi 5/11/2023 ne kungiyar ta Kano Pillars za ta ziyarci Kungiyar kwallon kafa ta Sporting Lagos a Jihar Lagos a wasan mako na bakwai na gasar.

Wasanni
Sakamakon wasan mako na hudu na gasar NPFL

Sakamakon wasan mako na hudu na gasar cin kofin kwararru na Najeriya na kakar 2023/2024 wato NPFL.
Tun a ranar Asabar din da ta gaba ta ne 21 Oktoba 2023, aka buga wasa daya tilo kamar haka÷
Niger Tornadoes 1 – 0 Bayelsa United
Sai dai an dage wasa tsakanin kungiyar kwallon kafa ta Doma United da Enyimba
Wasanni da aka buga a ranar Lahadi 22 Oktoba 2023 kuwa÷
Gombe United 1 – 0 Bendel Insurance
Akwa United 0 – 0 Shooting Stars
Heartland Owerri 1 – 1 Katsina United
Kano Pillars 1 – 0 Rivers United
Kwara United 1 – 1 Enugu Rangers
Lobi Stars 2 – 0 Abia Warriors
Plateau United 1 – 0 Sunshine Stars
Remo Stars 2 – 1 Sporting Lagos.

-
Nishadi4 years ago
Ina neman mijin aure – Rayya
-
Manyan Labarai4 years ago
KAROTA: An baiwa Baffa Babba wa’adin kwanaki bakwai
-
Labarai3 years ago
Hamisu Breaker ya kai kan sa wajen ‘yan sanda
-
Nishadi4 years ago
Mansura Isah ta yi kaca-kaca da Sadiya Haruna
-
Labarai4 years ago
Auren dan Panshekara da ba Amurkiya ya samu cikas
-
Lafiya1 year ago
Rahoto: An gano wani gida da ake gini da takardun Kur’ani da Alluna
-
Nishadi4 years ago
An gano daliban da Adam Zango ya dauki nauyin karatun su
-
Manyan Labarai4 years ago
Sabuwar damfarar da ta fito a Kano