Wasanni
Ban taba zama masoyin Ronaldo ba saboda girman kan sa – Mikel Obi

Tsohon kyaftin din Najeriya, John Mikel Obi, ya bayyana dalilan da suka sa bai taba zama masoyin Cristiano Ronaldo ba.
Mikel Obi ya dage cewa, ya fi son abokin hamayyar dan wasan mai shekaru 37, Lionel Messi.
A halin yanzu Ronaldo yana da ‘yanci bayan Manchester United ta soke kwantiraginsa a wannan makon.
“Ban taba zama masoyin Ronaldo ba da gaske.
“A gare ni, lokacin da dan wasa ya na da girman kai, ba na samun shi sosai. Bai taba zama daya daga cikin ‘yan wasan da na fi so ba, kuma shi ya sa na ke son Messi da gaske,” Obi Mikel ya shaida wa Dubai Eye.
Ronaldo ya zama dan wasa na farko a tarihin gasar cin kofin duniya da ya ci kwallo a wasanni biyar a jere.
Kyaftin din Portugal ne ya fara zura kwallo a raga a ranar Alhamis, yayin da suka doke Ghana da ci 3-2 a wasan da suka fafata a rukunin.

Wasanni
Kano Pillars ta sayi Salisu Abdullahi

Kungiyar Kwallon Kafa ta Kano Pillars ta sayi dan wasan tsakiya na kungiyar kwallon kafa ta Capital City da take a babban birnin tarayya Abuja wato Salisu Abdullahi
Salisu ya rattaba kwantaragin shekara daya da kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars, ya kuma sha alwashin yin aiki tukuru tare da yan wasan kungiyar, dan ganin kungiyar ta samu nasarori a gasar da zata buga ta cin kofin kwararru na Nigeria ta shekarar 2023 zuwa 2024.

Wasanni
Chelsea ta sayi Lavia daga Southampton

Kungiyar Kwallon Kafa ta Chelsea ta sayi dan wasan tsakiya na kungiyar kwallon kafa ta Southampton wato Romeo Lavia a kan kudi €58m.
Romeo Lavia, dan asalin kasar Belgium mai shekaru 19, ya rattaba kwantaragin shekaru bakwai da kungiyar kwallon kafa ta Chelsea.
Kafin komawar dan wasa Lavia kungiyar kwallon kafa ta Chelsea, ya bugawa kungiyar kwallon kafa ta Southampton wasanni 34.
“Ina farin cikin komawa ta kungiyar kwallon kafa ta Chelsea, kuma komawar ta zo min kamar a mafarki, domin Chelsea kungiya ce da take da tarihi kuma kowanne dan wasa zai so ace yana buga wasa a Chelsea, kuma zan hada kai da abokan wasana dan ganin mun kai kungiyar mu ga babban mataki” a cewar Lavia.

Wasanni
Kungiyar Kwallon Kafa ta Kano Pillars ta dauki sabbin yan wasa

A yunkurinta na tunkarar sabuwar kakar wasan gasar Firimiyar Nigeria wato NPFL ta shekarar 2023 zuwa 2024, Kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars ta sayi sabbin yan wasa guda uku domin yin garan bawul ga kungiyar.
‘Yan wasan dai sun hadar da Ibrahim Mustafah Yuga da Abubakar Ibrahim Babawo wayanda suka tawo daga Kungiyar Kwallon Kafa ta Plateau United dake jihar Jos, sai kuma Abubakar Aliyu daga Kungiyar Kwallon Kafa ta Wikki Tourists dake jihar Bauchi, sanarwar dai ta fito ta hannun mai magana da yawun kungiyar ta Kano Pillars Lurwanu Idris Malikawa.

-
Nishadi4 years ago
Ina neman mijin aure – Rayya
-
Manyan Labarai4 years ago
KAROTA: An baiwa Baffa Babba wa’adin kwanaki bakwai
-
Labarai3 years ago
Hamisu Breaker ya kai kan sa wajen ‘yan sanda
-
Nishadi4 years ago
Mansura Isah ta yi kaca-kaca da Sadiya Haruna
-
Labarai4 years ago
Auren dan Panshekara da ba Amurkiya ya samu cikas
-
Lafiya1 year ago
Rahoto: An gano wani gida da ake gini da takardun Kur’ani da Alluna
-
Nishadi4 years ago
An gano daliban da Adam Zango ya dauki nauyin karatun su
-
Manyan Labarai4 years ago
Sabuwar damfarar da ta fito a Kano